💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahimWannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 21
Duk da ba wani son mlm yahuza take ba amman tunanin rabuwa dashi Kullum yana bibiyar zuciyarta dan duk yadda take qoqarin ta yakicesa daga tunaninta abun ya cutura ba dan komai ba sai dan tsananin kirkinsa da tausayinsa gareta komai na duniya ya fitar mata a rai hatta zaman gidansu ya fita ranta saboda Harare hararen da take sha daga kowace fuskar ta mutan gidan wanda hakan yasa ta kasa samun sukunu ta rasa da me zataji da kwace mata saurayi da suka yi ko kuwa da nemanta da fitina da suke yi ?."
Tana kwance shiru akan katifa kamar mai barci alhalin ba baccin take ba. aunty ta leko d'akin tana kiran sunanta "princes baki ta shi bane ? tasan dole ta kasan tashi saboda abinda ya faru dole zai hana zuciyarta sukuni ."ahankali maryama ta yunkura ta mike daga kwanciyar da tayi ta ari murmushi da sukuni ta dasa a ranta tana cewa "aunty na tashi , tayi haka ne dan kada aunty ta gano har yanzu abinda ya faru yana ranta har yasa ta qara mata zancen addu'ar ma data kwana yi cikin dare ya d'an sanyayyar mata da zuciya, kuma har ranta taji ta samun sauki dan har yanzu data mike tana maimaita adduar Allahuma ajirni fi musibatihi wa aklifini khairan minha yafi sau babu adadi dan bata san iyaka adadin data yi ba , aunty ta riko hannunta cikin nata suka fito zuwa parlour ta zaunar da maryama ta lumshe idanunta cikin sanyayyar muryarta tace "aunty ina after dad ?""Tun safe ya fita zuwa filin kwallo amman nasan yana kan hanya dawowa yanzu numfashi ta sauke da karfi sakamakon tunawa datai yau asabar ce daman kuma ranar asabar da lahadi sune ranakun daya ware domin zuwa filin kwallo , ta mike tsaye a natse ta nufi hanyar kitchen domin had'a kan kayan wanke wanke ta jiyo sautin muryar aunty tana cewa "ina zaki ?" .
"zan shiga kitchen na had'a kayan wanke wanke na wanke ne ." tayi maganar cike da raunin zuciya Kmr zatayi kuka , shiru aunty tayi tana kallonta cike da tausayawa kallo d'aya zaka mata ka fahimci bata cikin natsuwarta da kwanciyar hankali tayi wata muguwar rama " ga abinci akan table ki d'auko kizo ki karya kafin ki fara aiki ."
ta sauke numfashi sannan ta rausayar da kwayar idanunta bata jin cin komai amman kuma bazata iya cewa aunty bazata ci ba dan tasan bazata ji dadi ba dan damuwarta damuwar aunty ce , idan ta runtsa aunty ta runtsa ,idan ta kwana Jin motsinta to haka itama bazata runtsa ba ,ta dinga kai kawo kenan a tsakanin d'akinta da nata ."
Jikinta a matukar sanyaye ta qarasa inda kular abincin yake ta bud'e ,shiru tayi tana kallon abincin , sai data d'auki second goma tana kallon abincin sannan ta kalli aunty fuskarta d'auke da tambaya "ummah ce ta aiko mana dashi , sanyayyen ajiyar zuciya maryama ta sauke sannan ta d'auko Kula tazo ta zauna kusa da aunty ta fara ci a natse , ba wani abincin kirki taci ba ta rufe kular tana qoqarin mikewa tsaye aunty tace "har kin yi me kenan princess ? " ki koma ki qara cin abinci duk fa kwanakin nan ina lura dake ba wani abinci kirki kike ci ba ,ki taimakeni ki manta da abinda ya faru ga gobe can tana d'aga muna hannu kullum cikin miki addua nake , nayi imani allah bazai barki haka ba zai kawo miki wani mafi alkhairi."

YOU ARE READING
MAR'ADAMS
Romancelabari ne Mai dauke da soyayya , ilimantarwa, fadakarwa, nishantarwa jajicewar rayuwa .