Babi na biyar

0 0 0
                                    

🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*YADDA KA DAUKE TA*🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
Alkalamin *Matar Sadi*🖌️🖌️🖌️🖌️🖌️🖌️🖌️🖌️

Allah ya Kara lafiya kawata Rahma ,Allah ya jikan baby ya saka masu ceton mune Amin ya rabbi

Happy children's day to all our kids Allah yai maku albarka amin ya rabbi

Suwai ta labartawa iyayen ta karya da gaskiya tace abunda ya faru kenan .Baba da kansa ya taka kafa da kafa yaje ya sami waliyyin Aminu, Kuma take aka kira Aminun domin gidan su na nan unguwar ya dawo tunda babu kowa ya rufe nasa ,Aminu ya sun kuyar da Kai har sai da malam bashari ya fusata yana ba magana ake Maka ba.

Yana dago fuska suka ga hawaye na zuba yace baba gaskiya bazan iya cigaaba da zama da suwai ba saboda ta aibata ta mun iyaye ,Kuma ba wannan ne na farko ba bata duba kasancewar su sun rasu ba Amma tayi hakan. Haka dai aka tashi ba tare da ya mayar da suwai ba.

Ana gayawa inna buruji tace to Allah ya sa haka shi yafi alkairi ,nan suwai aka fara idda ta dauka zata sami damar fita yawon ta tuni , baba ya taka Mata burki yace ko tana fita sai ta gama idda ,Shima ba sakaka ba sannan aka raba ayyukan gida da ita ,Mai jidda nayin wanke _wanke da shara Kan ta tafi makaranta ita Kuma suwai girki ya hau kanta .Ta dinga Jin haushi domin ita ko agidan ta ba Wani girki ta cika yi ba musamman na rana.

Lokaci yazo da canji da cikin watannin da tai tana idda ,mahaifan ta sunyi matukar bakin cikin mutuwar auren ta,ko wane iyaye zasu so in sunkai yar su ya zama mutu Karaba to haka ce ta kasance ga iyayen suwai .

Tana dab da gama iddar ta aka dawo da sojan Samy Zaria da aiki anan Basawa camp,Samira tayi matukar farin cikin wannan sauyin aiki,bayan sun Yi reporting Kai tsaye suka wuto Kano tare da goyan yarta humaira wacce taci sunan sojanta ,Kuma sai asannan tasan mutuwar auren suwai ,tayi bakin ciki har sai da taiwa Baban su maganar tunda saki biyune a duba ko za'a gyara Baban ya shaida Mata yayi kokarin hakan Amma waliyyin Aminu yace shi Aminun yace ai hakuri kawai baya Jin zai cigaba da zama da suwai ba.

Wallahi jeey agidan nan maganar yaya samy ake ji kawai ,Abu kadan kiji inna tace maman humaira Shima babban haka ke har su Mai jidda fa ai Ina ganin rayuwa ,"

"mijin ta Mai kudi ba dole su kauna ce ta ba "ke rayuwar nan in baka dashi dole kaga babban ci .

"Ai ki bari kawai Kiri Kiri sau Daya naje gidan ta wai inna ba za'a barni in dinga zuwa ba kar na kashe Mata aure "

Ai na dauka kince suna zariya"cewar jeey

"Ai Kan su tafi ya dankara masu gida a Rafin Dan nana anan suka sauka "

"Ke ni zan manta ma Ina abokin Faisal dina da nace Miki amatar sace ta mutu da sukai accident"

Eh nagane shi Musa ko ? Wanda kika ce Dan canjine

Eh shi ,to shine yace a samo masa Mata ni Kuma naga tunda gaki a kasa Kuma akwai hatimin nasara kawai sai ku dai-dai ta

Kai dama nasan ke Mai kauna tace jeey kina Sona da arziki suka tafa yanzu zasu dawo lunch tare Kinga sai ku gaisa ai .

Mafarin haduwar suwai da Musa kenan abokin mijin jamila wacce suka Fi kira da jeey.

Lefe yai wa suwai kamar budurwa ya saki bakin aljihu aka Wala musamman da yake gidan Samy takai walimar tarewar ta ,

Aka raka amarya gidan ta dake unguwar koki da fatan Allah ya Basu zaman lafiya .Inna kwa ta Kara da cewa Allah ya Saba halayye .Amin inna

Kuci_kuci Dan kankani ,milili Dan karrarami ,ayye yo ayye ayye yo

suwai ke wannan wakar Kuma ciki daga murya take yin ta,tana da kwance akan kujerar three seater a falonta Wanda ya tsaru iya tsaruwa don har da VCD kasan cewa lokacin yayin C.D plate ake ga carpet irin Mai wall to wall din nan red color, ga T.V ta kirar Sharp .

Musa yana Jin ta yai shiru Bai magana domin ance Mai habaici maso fada Wanda ya tanka Kuma ya fishi .

Da ta ga Bai kula ta ba sai ta sake salon wakar zuwa

30 second am done ,2 minutes maximum rate hahhh ta saka dariyar rainin hankali .Ni suwai naga life.


Mai kuka fahimta da wannan wakar ta suwai ?🤣😂😂
Kun fahimci Wani Abu ko tukunna ?
Ku cigaba da bina sannu labarin suwai yanzu muka fara da sauran aiki a gaba.

#Team suwai#
#Team Aminu#
#team Musa#.           
                Watpad@oum Hafsa
         

                       Oum Hafsa Amanee

YADDA KA DAUKE TAWhere stories live. Discover now