PAGE 1-2

22 3 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
           (UWAR MIJI CE SILA)

TRUE LIFE STORY

STORY AND WRITTEN BY
UMMUSULTAN
            &
GIMBIYA AYSHU 💞💞💞

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
            

PAID BOOK
BONUS PAYMENT 300
LATE PAYMENT 500
COMPLETE NOVEL 1000

ACCOUNT NUMBER 2245462427
ACCOUNT NAME AISHA MA'ARUF
BANK NAME UBA
EVIDENCE OF PAYMENT 08076119294

WHATAPP ONLY BANDA CALL!!!!!!!

KARKU BARI A BAKU LABARI,TAKEN NA DABAN NE,NA TABBATA WANDA YA SIYA BAZAI YI DANA SANI BA INSHA ALLAH.

BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI,YA ALLAH KAMAR YANDA KA BAMU DAMAR FARA LITTAFIN NAN CIKIN SA'A KA NUNA MANA KARSHEN SHI LAFIYA,KASA ALUMMA SU ANFANA DA SAKON DAKE CIKI AMEEEN.

                   *FREE PAGE*

BOOK 2:CHAPTER 1&2

________________________Sam banga anfanin kukan nan naki ba Ummu Aymana,babu maganin  da Kukar nan zai miki  illah ya haddasa miki wani ciwon,na sha faɗa miki wannan Mijin naki ba irin wanda za'a rufawa asiri bane,meyasa baza ki faɗawa iyayen ki ba su ɗauki mataki,yanzu idan wani cuta ya kama ki fah?,shi ba shida asara tunda yana da wata matar,kuma yana da kudin da zai iya ƙaro biyu ma a lokaci ɗaya.

Murmushi Ummu Aymana tayi tace"Aunty Lubna kenan,duk yanda kike tunanin aure toh ya wuce nan,ba kowane lokaci zaki faɗawa iyaye matsalar magidan ki ba,yanzun idan na fara kai ƙarar sa cewa za'a yi y'aushe ma aka yi auran da har zan fara kawo ƙara,kuma kinsan yanayin gidan mu ba sai na faɗa miki ba,dama ce kawai ake jira a samu abin faɗawa Mahaifiya ta,daman akwai wadan da ba su son auren nan,ni kuma duk abin da zai taɓa kimar iyaye na ba san shi na ke ba,dan haka ki tayani da addu'a kawai Allah ya kawo min sauyi cikin rayuwar aure na".

"Hmmm toh shikenan tun da haka kika ce kuma kika zaɓa,ni dai ban ga dalilin da zai sa na zauna a na cin zarafina kuma na yi shiru ba,wlh bazai yu ba,sai dai wata lubna ba ni ba,amma babu komai zamu jira mu ga ikon Allah inda rai".

Nagode sossai Aunty Lubna,"dan Allah ki rike min SIRRI NA,duk duniya babu wanda yasan matsala ta face ke,ko iyaye na ban gayawa ba,ki taimake ni kamar yanda Allah ya taimake ki ki rufa min asiri a ko wani irin yanayi".

Murmushin takaici Anty Lubna tayi tace"shikenan zan yi kamar yanda kika ce amman ba dan ina so ba,Allah ya shige mana gaba Ameeen,muje na raka ki kafin Abban Yasir ya dawo ya iske baki gida ya zama wani abin".

Bata jima da dawowa ba Abban Yasir ya shigo dauke da Yasir,cikin sauri Ummu Aymana ta ajiye aikin da take ta fito dan ta tarbe shi,sam ba tasan abinda zaisa aci zarafin ta dana iyayen ta da Magaribar nan.

"Sannu da zuwa Abban Yasir".

Dagowa ya yi ya kalle ta sannan ya watsar kamar bai ji mai ta ce ba.

Hanka da yayi ne yasa ta cigaba da zama a wurin tunda bai bata izinin tafiya ba,sai da ya gama shan kamshi da hura hanci sannan yace"ke baki san ki kawowa mutum ruwa daya shigo gida ba kohh!,sai dai ki sa shi gaba kina kallon kaman kin sami majigi".

Dago kyawawan i'danuwan ta tayi tana kallon shi tace"Allah ya baka hakuri ya huci zuciyar ka,na ga baka amsa sannu da zuwar da na maka ba ne shi yasa na zauna".

"Ohhh! toh sai na amsa kenan za ki tashi ki bani ruwa kohhhh?,shin wai dole ne amsa gaisuwar taki?,kehh!ni fa ban san naci,idan zaki ba ni ruwa ki bani,idan kuma baza ki bani ba na tashi na je gurin da za'a ban cikin soyayya da kauna".

Kala bata sake ce mishi ba ta mike ta kawo masa ruwan,har lokacin yana nan inda ta bar shi yanawa yaran shi wasa shi kuma yana wangale masa baki.

Tanan ne kawai ta ke jin saukin abubuwan da ke faruwa da ita a gidan aurenta,akwai shakuwa sosai tsakanin sa da Yasir,duk da dai yana da wasu yaran a gun Uwar gidansa, amma yana ji da Yasir sossai.

Mikewa yayi zai fita da yasir a kafadar shi,ko mai kuma ya tuna sai ya dawo ya nufi  hanyar dakin shi,tasan alwala zai yi dan an yi kiran sallah,mikewa ta yi dan gabatar da na ta sallar.

Duk abin nan dake faruwa Aunty Salma na ji,bakin ciki kamar ya kashe ta,haba dan Allah wannan wacce irin rayuwa ce Ummu Aymana ke ciki,kamar ba matar auren sa ba,wallahi baza ta sabu ba wai bindiga a ruwa,i dole ne ma ta faɗawa Iyami halin da a ke ciki wlh...........................................


Comment
Vote
Share fisabilillah


By Ummu sultan & Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(UWAR MIJI CE SILA) BOOK 2Where stories live. Discover now