PAGE 7-8

3 0 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
             (UWAR MIJI CE SILA)

TRUE LIFE STORY

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞
                &
UMMUSULTAN

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚

               *FREE PAGE*
                *PAID BOOK*

DAGA WANNAN PAGE DIN SAURA NA KARSHE,KU BIYA KAMIN A GAMA FREE PAGES,DAZARANVAN GAMA ZAI KOMA NORMAL PRICE DIN SHI WHICH IS 500.

*Gimbiya Ayshu's  Data service*

*Ku siya data a garabasa*

*MTN*                   

500MB-180
1GB -280
2GB - 550
3GB - 750
5GB - 1250
10GB -2500

*AIRTEL*
300MB - 170
500MB - 200
1GB - 300
2GB - 550
5GB - 1350
10GB - 2600

*GLO*

200MB - 120
500MB - 180
1GB - 300
2GB - 550
3GB - 850
5GB - 1350
10GB - 2600

*9MOBILE*

500 - 180
1GB -280
2GB - 550
5GB - 1300
10GB - 2500

Account number:8036434941

Account name: Maryam Maaruf Muhammad

Bank name:Opay

*Contact me on this number:08076119294*

BOOK 2:CHAPTER 7-8

_____________________Da sauri Aisha ta fita parlor,ta yi Sa'a ko har yanzu yana zaune bai tashi ba,ga Ummu a gefen shi tana haɗa masa abinci ko kallon inda ta ke bata yi ba,tsugunawa ta yi a gaban sa ta ce"Hajiya ta ce tana kiran layin ka ba ya shiga wai ka kira ta yanzu".

Dago idanuwan sa ya yi ya zabga mata wata uwar harara,ba ta san lokacin da ta yi ƙasa da nata idan ba.

Murya a kausashe ya ce"na ji tashi ki bani wuri kafin na yi ƙwallo da ke",ya fada ran shi a bace.

Ba shiri ta miƙe jikin ta na rawa kamar mazari,sosai ta ji haushin abin da ya mata a gaban Ummu,amman ba komi,a j uri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe,girgiza kai ta yi ta ce"da ni ka ke zancen yaro za kasan ka yi da yar halak".

Dakin ta ta nufa rai bace,ba bata lokaci ta dau waya ta yi ta kira Hajiya,Hajiya dake ta jiran kiran ta ne ta yi saurin dagawa,dama a ƙage ta ke,ji take kamar ta yi tsutsuwa ta ganta a gidan.

Cikin sauri ta ce"kin fada masa dai koh?".

Lankwasa murya ta yi ta langwabe kai ta wani karkace baki ta ce"na faɗa masa Hajiya amma sai ya ce"na tashi na bashi guri kar ya yi ƙwallon da ni",ta fada tana shasshekar munafirci.

Zaro ido waje Hajiya ta yi ta ce"shiMahmood ɗin ne ya ce miki zai yi ƙwallon da ke dan na aike ki gurin saaaa!",lallai asiri ya fara taɓa min shi,ai banga ta zama bah,dole na san abun yi,ta fada tare da kashe wayar tana huci.

kiran ta Abban Yasir ya yi amman har ya katse bata daga ba,yana katsewa ya kuma kira,kiran na gabda katsewa ta daga cikin tsananin bacin rai ta ce"sai yanzu kaga daman kiran nawa?" ,...... zai yi magana ta yi saurin katse shi ta ce"ba na son jin komi,duk abinda kake yanzu ka bar shi kazo gida ina son magana da kai,kuma wlh ka kuskura ka wuce minti ashirin baka iso ba ranka zai yi masifar baci,ka dai ji na gaya maka",ta fada tare da katse wayar ba tare da ta saurare shi ba.

Bin wayar ya yi da kallo yana mamakin abinda ya bata mata rai,toh mai kuma ya faru ya ji muryar Hajiyarsa haka,mikewa ya yi tare da ɗaukar car key din shi,yana shirin fita daga parlor kiran ta ya kuma shigowa,dakatawa ya yi ya daga kiran cikin ladabi,kafin ya kai ga magana ta ce"kar ka yi gaggawar zuwa yanzu,na fita wani uzurin amman bazan jima ba zan dawo,sabida haka ka zauna cikin shiri ina dawowa zan kira ka,dan ina da muhimmiyar magana da kai kuma ban san ya wuce yau,ina fatan ka fahimta".

"Na ji Hajiya Allah ya dawo da ke lafiya".

"Amin",ta fada tare da kashe wayar tana jan wata doguwar tsaki ta ce"jani talo kawai,ka zauna mace na juya ka,wawa kawai,wlh baze sabu ba,bazan zauna ana wannan shashancin da ni ba",gaba daya ƴariyar nan UmmuAymana ta rusa rayuwar ɗan ta tunda ya aure ta,kwata-kwata baya zama baya jin maganar ta sosai,sai ta haɗa da asiri sannan ta ke samun kansa,wlh na gaji sam,gaskiya shawarar ki ta yi Lauratu,yanzu kin ga zamu iya zuwa gidan Malamin nan mu dawo kohh?".

"Eh! Sosai ma kuwa",ta bata amsa hankalin ta gabaki daya na kan wayar da take danawa,haushi ne ya kama Hajiya Zara,karɓe wayar ta yi sannan ta ce"wallahi Lauratu ki kiyayyeni ina magana kina danna waya,sai na ci ubanki shegiya kawai,za ki tashi mu tafi ko kuma sai na sassaba miki",duk wannan faɗi tashin dana ke dan su wa na ke idan ba ku ba?,amman dan tsabar wulakanci shine ina miki magana kina danna waya kohhh!,toh wlh ki kiyaye ni ko na hau kanki wallahi.

Turo baki ta yi tana kunkuni ta ce"ni fa ba wani abu na ke yi ba,Aunty na ke bawa labarin abunda ya faru shine ta ce" dama ita yanzu zata gun wannan Bokan nata dake hayin rigasa,insha Allahu idan ta je za ta yi maganar Yaya a gunsa,shine kafin na bata amsa kika karɓe wayar a hannuna",ta karasa maganar ta tana turo baki.

To ai kece da shashanci,da sai ki faɗa min,yanzu dai tashi mu tafi kafin ya ƙaraso,ta fada tare da miƙewa ta rataye ɗan karamin mayafi wanda ko wuyan ta bai sauka ba.

Komawa kan sofar da ya tashi ya yi ya cigaba da dana wayar sa yana tunanin dalilin daya sa Hajiya take neman shi,daga jin muryar ta ya san ba lafiya ba,bayan kaman minti ashirin ya mike ya shiga parlor Ummu,a zaune ya same ta tana bawa Yasir nono amma gabaki daya hankalin ta baya duniyar mutane,ta yi nisa cikin tunanin da take,zama ya yi a kan kujerar dake kusa da nata yana kallon ta,bai san dalilin da yasa yake jin haushin ta ba,kuma ya san bata mishi komi ba,ya rasa dalilin da yasa yake jin haushin ta,gyaran murya ya yi yana kallon ta,hakan ya sa ta yi saurin daga kai tana kallon shi fuskar ta dauke da mamakin yaushe ya shigo,kuma ga dukkan alamu ya jima a zaune,"har ka dawo ne?,ban ji shigowar ka ba,sannun da zuwa",ta fada tana kokarin kwantar da Yasir da ya riga da ya yi barci.

Kamar ba zai yi magana ba da farko,sai kuma daga baya ya ce"ina zaki ji shigowa ta,gabaki daya kin sa damuwa a ranki,tashi ki kawo min kayan abinci nan na ci,sai anjima zan je gidan Hajiya,wai yanzu za ta fita".

Mikewa ta yi tana kokarin fita ta ce" Allah ya nuna mana anjiman lafiya",sai da ta sake warming abincin sannan ta kawo ta ajiye.

Kamar daga sama ta ji ya ce"mai kike son faɗa min dazu,ina sauraran ki",ya fada tare da kai loman abinci bakin shi.

Tattaro sauran jarumtar daya rage mata ta yi ta ce"ba komi,dama ina son sanar da kai cewa Aunty Salma tazo ɗazu,ta karashe maganar ta a hankali tana kallon shi dan taga reaction din shi".

Ganin yanayin shi bai chanza ba yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah,ganin bai sake magana ba yasa itama ta ja bakinta ta yi shiru,sai da ya gama cin abinci kamar daga sama ta ji ya ce"mai ta zo yi?".

Baba ne ya ce tazo sabida aikin ya min yawa ga kuma karamin yaro,ga kuma theater da aka min,shi yasa ya turo ta dan ta dan taimaka min kafin Aisha ta yi arba'in",ta karasa maganar ta gaban ta na dukan tara-tara.

Wayar shi kawai ya dauka ba tare da ya furta mata komi ba,ganin haka yasa taja bakinta ta yi shiru,ta san ikon Allah ne kawai ya ƙwace ta ba iyawar ta ba,In ba haka ba ai da yanzu an rasa zaman lafiya a gidan nan,amma duk da haka hankalin ta bai kwanta ba sabida ta san muddin ya je gidan Hajiya dole ya sanar mata,kuma bata san da wani fuska zai dawo ba,ita kam ga ta ga Allah,Allah ya shige mata gaba......................................


SHARE FISABILILLAH

BY UMMUSULTAN & GIMBIYA AYSHU💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(UWAR MIJI CE SILA) BOOK 2Where stories live. Discover now