PAGE 3-4

5 1 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
             (UWAR MIJI CE SILA)

TRUE LIFE STORY

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞
                &
UMMUSULTAN

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
       

           
                  *FREE PAGE*

PAID BOOK
BONUS 300
NRLM 500
COMPLETE 1000

*Gimbiya Ayshu's  Data service*

*Ku siya data a garabasa*

*MTN*                   

750 -230
1GB -280
1.5GB - 380
3GB - 720
6GB - 2200
10GB - 3700

*AIRTEL*

750 -230
1GB -280
1.5GB - 380
3GB - 720
6GB - 2200
10GB - 3700.

*GLO*

750 -230
1GB -280
1.5GB - 380
3GB - 720
6GB - 2200
10GB - 3700.

*9MOBILE*

750 -230
1GB -280
1.5GB - 380
3GB - 720
6GB - 2200
10GB - 3700.

Account number:8036434941

Account name: Maryam Maaruf Muhammad

Bank name:Opay

*Contact me on this number:08076119294*


BOOK 2:CHAPTER 3-4

__________________________A haka ta gama aikin ta cikin damuwar da ya zame mata abokin rayuwa,ita kam a rayuwa babu abinda za ta ce sai godiya ga Allah,tun tashinta gidan mahaifin ta bata san dadin rayuwa ba sabida azabtarwan kishiyoyin Maman ta,gashi har gidan miji abin ya biyo ta,wallahi ba za ta ce tasan wani abu wai shi faɗa da kishiya ba,amma uwar miji ita ce ta fitine ta ta hanata zaman lafiya a gidan ta,duk da itama kishiyar tana nata aikin asiri daga gefe,ga shi ta girmeta nesa ba kusa ba.

Babban damuwar ta a yanzu shi ne zaman Anty Salma a tare da ita,ta so ta tafi tare da Anty Lubna amman Anty Lubna taki ta dage sai ta zauna tare da ita har a gama azumi wanda ba karamin tashin hankali za'a yi da Abban Yasir ba,gashi basa shiri sosai da Aunty Salma kamar yanda suke da  Aunty lubna,Anty Lubna na iya ganin abu ta ɗauke ido amman ban da Aunty Salma,komai ta gani sai ta yi magana kuma ta tanka,a ƙarshe kuma laifin ya dawo kaina,kuma ni ba iya kwatan kaina zan yi ba idan Abban yasir ya fara bala'i.

Ta yi zurfi cikin tunanin da take har Anty Salma ta fito ta zauna kusa da ita bata sani ba,kallonta kawai Aunty Salma take,tana mamakin yanda Ummu ta koma,yarinya ga kyau ga diri ga haske Masha Allah,ita ba siririya ba sannan ba mai kiba ba,amma ji yanda ta koma duk ta bushe ta lalace sai kashin wiya kamar an haka rami,wai yau Ummu ce babu kamshi bale suturar arziki,ba wai dan ba ta da kaya ba,kudin dinkin ne babu,kuma wanda take da su babu kwanciyar hankalin da za ta sasu duk a dalilin Uwar miji da shi kan shi mijin.

Juyowa Ummu ta yi da sauri jin an dafa ta,ganin Aunty Salma ce ya sa ta yin murmushin yake tana goge hawayen kan fuskarta ta ce"Aunty ke ce?kin fito kenan?,yanzu na ke shirin zuwa na duba ki",kallon ta Aunty Salma ta yi sannan ta ce"Ummu".

Amsawa ta yi muryar ta a sanyaye da
"na'am Aunty".

"Ummu!,Ummu!,sau nawa na kira ki".

Muryar ta na rawa tace"sau uku Anty",ta fada tana goge hawayen dake gangaro mata".

"Meh ke faruwa da ke a gidan nan?,akwai wata matsalar ne bayan wanda na sani?,kuma kar ki kuskura ki min karya dan naji duk yanda kuka yi da Lubna,wato ni kin ɗauke ni ba nida sirri shiyasa baki faɗamin matsalarki kohhh!?".

Da sauri Ummu ta riƙe hannuta hawaye na anbaliya a kan kuncin ta tace"a'a wallahi Aunty ba haka bane,aini a tunanina babu wanda yasan halin da nake ciki fiye da ke,tunda kusan rabin rayuwar aurena a tare muka yi shi,Aunty kar ki manta tun cikin Yasir na da wata uku(3month) muke tare,toh menene baki sani ba?,babu wani saban abunda ya karu,kuma maganar da kika ji muna yi da Aunty Lubna ba komai bane face kan zaman da za kiyi da ni,shine nace ba karamin matsala da rashin kwanciyar hankali zaman ki a tare da ni zai janyo ba,hakan yasa nace ta roki iyami ko Allah zai sa ta chanja maganar ta,sai ta ce ba zai yiwu ba,taya za'a bar ni ni kadai ga azumi ga karamin yaro ga rashin isasshen lafiya sannan ga aikin gida kuma ba mataimaki,haba sai kace mara gata,ba zai maida hankali wurin kula da ke ba dan matar shi ma ta haihu,kuma kin san halin da kike ciki yanzu dole sai da mataimaki,sabida haka kiyi hakuri kamar yanda kika saba,Allah na tare da mai hakuri",ta karasa maganar ta tana kuka.

Ajiyar zuciya mai karfi Aunty Salma ta sauke tace"bar kukan haka dan Allah kar su jiyo ki,na dauka ai kin fara boye min damuwar ki ne,Ummu ni da kaina na faɗa musu a hakura a barki amman sun kasa ganewa,su gani suke kamar ke ce ba kisan mutane su zo gidan ki,duk yan uwan ki na kaduna haka suke tunani,kuma su ke kara zuga Iyami ta yi miki fada,musamman kawarta Bilkisu.

Ajiyar zuciya Anty Salma ta yi tace"ya za'a yi da mai gidan ki?,kin san wallahi ba zan raga masa ba idan ya ce zai kawo min rashin hankali,in ba rashin imani irin na wasu ba taya zai ce kar kowa ya zo wurin ki haba,sai kace mara dangi,saboda Allah fahhh!,ni dai gaskiya tunda na taso ban taba ganin rashin mutunci irin wannan ba,Allah dai ya sa mu da ce Ameen",ta faɗa tare da mikewa tsaye tana mita.

Murmushi Ummu ta yi tace"Aunty Salma kenan,ba dai rigima ba".

Miƙewa ta yi dan an iddar da sallar  Isha'i,ta san yanzu zai shigo,hakan yasa ta yin hanzarin shiga daki dan ta watsa ruwa ta shirya kafin ya shigo,so take yana shigowa ta sanar da shi zuwan Aunty Salma,baza ta ce masa Iyami ce ta turo ta ba sai dai ta ce Babanta ne ya turo ta,sai da ta tabbatar ta jera komai sannan ta juya za ta tafi taga kamar coolers din yayi kan hanya,dawowa ta yi ta matsar da su dan kar ya zo ya yi tun tuɓe da su ta shiga uku,Allah sarki rashin sani ya fi dare duhu.

Yana shiga ya ga coolers a gefe,nan take annurin fuskar shi ya dauke,hanyar dakin ta ya nufa ran shi a mugun bace,yana shiga dakin ya tarar tana bayi,juyawa ya yi a fusace,ba zarce ko ina ba sai parlor shi,ya kai kusan minti arba'in a zaune yana jiran ta zo ta naime shi amman har lokacin shiru,mikewa yayi yana ta faman safa da marwa a parlor hannun sa nade a bayan sa sai tsaki yake yana karawa,sai alokacin Ummu ta fito cikin kwanciyar hankali ta shirya ta dan yi light make-up dan ta ja hankalin shi,tana shiga parlor ta iske kayan abincin ta yanda ta bar su ko taba su ba'a yi ba,dakin ta ta koma,ganin yasir kwance a kan gadon sa yasa ta tabbatar da ya shigo dakin ta dan ba a nan ta bar shi ba,toh mai yasa bai ci abincin ba,wani bangare na zuciyar ta ta ce kila abincin yayi sanyi,girgiza kai ta yi da sauri tace"inaaaaa! abincin da na gama yanzu",wuri ta samu ta zauna tana jiran dawowar shi dan duk a tunanin ta ya shiga gun kishiyar ta Aisha.

Ta shafe minti talatin a zaune amman shiru babu shi babu alamun shi,wata zuciyar ce ta ce ko dai  yana parlor shi ne,dan duk ranar da yake jin tsiya haka yake,ilai kuwa tana zuwa parlor ta iske shi sai safa da marwa yake ya cika yayi fam sai huci yake kamar zai ci babu.

Wani irin muguwar faduwa gabanta yayi,a fili tace"na shiga uku"....................................….

Paid book ne,bonus 300,nrlm payment 500,complete book 1000.

Karku bari a baku labari,idan aka gama free pages kudin zai koma normal price din shi 500.

Kar ku baribayi ba ku,na tabbata za ku nishadantu,littafin na kunshe da kalubalen"MATSALAR GIDAN MIJI"sai kin karanta zaki tabbatar da hakan.

Payment is available,wasu sun fara biya.

Account details
Account number 2245462427
Account name Aisha Maaruf
Bank name UBA
Evidence of payment 08076119294
WhatsApp kawai banda call.

A turo receipt of payment ta wannan number na sama,nagode.

Comment
Vote
Share

BY UMMUSULTAN & GIMBIYA AYSHU💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(UWAR MIJI CE SILA) BOOK 2Where stories live. Discover now