TUN RAN GINI! 1

2 0 0
                                    

🎑🎑🎑🎑🎑🎑🎑
   *TUN RAN GINI!
   (RANAR ZANE)
🎑🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

PAGE 1️⃣

_________  Yau take monday ko muce litinin na bawa inji hausawa, ranar da duk wani d'an boko ke son zuwansa, yayinda awani b'arin kuma suke tsoronsa. litinin kenan makamar aiki, ranar da ma'aikata, y'an makaranta, y'an kasuwa, da duk wani mai mu'amala ta yau da kullum ke d'aukansa a matsayin mafarin mu'amalar rayuwar yau da kullum.

Ba anan ta tsaya ba, hatta y'an siyasa kama daga shuwagabanni k'asa, gwamnoni, sanatoci da y'an house of assembly wannan rana ta zama jigo babba dake da babban muhimmanci awajensu.

Talking about y'an siyasa, kamar daga sama na jiyo tashin jiniyar motoci ta ko ina na dumfaro inda nake, duk kuwa da cewa akwai rata sosai daga inda wannan k'aran ke tashi da inda nake, wanda a k'iyasce zai iya kamar nisan kilometer ashirin hakan bai hana ni da duk wanda yake taredani a wannan wajen jin wannan k'aran na tashi tamkar dai yanda aka saba ji ne a wannan area yau da kullum.

Wanda banyi mamakin jin hakan ba a yau, tunda ba b'oyayyayen abu bane, abu ne wanda kowa yasan cewa a yau litinin sha uku ga watan bakwai ne babban kotu ta k'asa, wato (supreme court) zai kawo k'arshen zaman dayakeyi akan k'aran da wasu jam'iyun siyasa keyi kan sanata mai wakiltar mazab'ar  gwaram ta tsakiya wato "Alhaji Isa gwaram" babban sanata daya dad'e yana jan kambunsa na siyasa ya jima yana samun kujeran sanata batareda ya sha kayi ba awajen y'an adawa, duk kuwa da cewa da yawa kan yi ta soki burutsun bai cancanci kujeran ba, wanda yasa izuwa yanzu bazar dayake takawa ta fara gushewa har ake ganin kujeran nasa ma ba guminsa bane ke basa illa murd'iya, zamiya, cin gumin al'umma shine k'ashin bayan kujeran nasa a yanzu.

Dalilin dayasa wannan karon kujeran nasa ke neman kubce masa, saboda wasu hujjoji da y'an adawan keta fafutukar ganin sun gabatar wa kotun, don ganin ta aiwatar da adalcin datake ikirarin zatayiwa wad'anda aka zalunta.

Hakan kuwa bai tab'a d'ad'a sanata gwaram ba, saboda yana ganin yayi k'arfin da babu mai iya tunb'ukesa a wannan kujeran.

To saidai! ba nan gixo ke sak'a ba, kamar dai Alhaji gwaram yayi nisan bacci, wanda kafin ya farka har an samu wasu sunyi wa al'amuransa shigan burtu, yayinda suka fara bud'e closets d'insa wanda hakan ke barazana wa kujeran daya dad'e yana tattalawa.

Shigowarsa harabar kotun wacce ta cika mak'il da jama'a, kama daga lauyoyi, masu k'ara, y'an kallo, y'an kasuwa da kuma uwa uba sarakan d'aukan rahoto, tsuliyan labari, wad'anda basu ganin labari su barta ta tafi scot free wato (journalist) a hausance muce y'an jarida!

Da d'an gudu kowannensu rik'e da mic  a hannunsu suka nufe shi yayinda yake k'ok'arin fitowa daga motarsa wanda wasu mutane masu bak'ak'en Court suka fito da sauri suka bud'e masa, sunata ta k'ok'arin k'are shi daga mutane, yayinda shi kuma yake ta d'aga hannu ga wani murmushin dayakeyi tamkar gonan auduga.

Saidai kash! duk yanda suka so gujewa tambayoyin y'an jaridun nan basu tsira ba, don kamar yanda ake cewa akwai y'an jarida masu tambayar k'ak'a uwaka ta haifeka wanda idan sunyi maka irin wannan tambayar ko kai dutse ne sai ka motsa.

Ga mai tsantsar lura zai ga yanda yanayinsa ya canza atake, don ko taku d'aya ya kasa k'arawa, saidai dayake he's so good at hiding his true colour, sai ya juyo yana cigaba da murmushi yayinda idanunsa ke sauk'a akan wannan kyakkyawan y'ar jaridan dake bayansa.

Security sa sun so su fara bud'e mata idanu, amma sai ya d'aga musu hannu  yana mai k'ara kureta da idanu, kallon da ba lallai ka fahimci dalilinsa na yin hakan ba.

Itama murmushin tayi wanda kana gani kasan she's just forcing herself to do it, don batayi zaton tambayar da tayi masa har walau zata ga murmushi a fuskarsa. he's so good at acting ta fad'i acikin zuciyarta.

TUN RAN GINI! Where stories live. Discover now