TUN RAN GINI TRAILER

0 0 3
                                    

🎑🎑🎑🎑🎑🎑
     TUN RAN GINI
   (RAN ZANE!)
🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

*TRAILER*
*RELEASE DATE 30th /April /2024

*paid book 300*

*Wannan littafin k'irk'irarren labari *ne, duk wani kama, suna da gari akasi ne*

*TALLA*

Kina ina uwargida ran gida, amarya shalelen mai gida, me kukeyi har yanzu baku mallaki sha yabo sha nema, kayan gyaran jiki mai da tsohuwa yarinya na Maman Meenat wacce tayi fice a fad'in k'asar nan. Shin kinsan da kud'i k'alilan zaki mallaki duk abinda kikeso awajen Maman Maman, kama daga kayan gyara skin irinsu whitening set, lightening set, glow set, milky set, amarya set. wannan saitin idan kika mallake su Hajiya kin wuci sara saidai kiji ana abaki wajen zama awajen taro.
Kayan Maman Meenat ba anan ya tsaya ba, tanada kayan gyaran da zai maida miki martabarki fiyeda yanda kike tunani, akwai zumar k'iba, hips set, breast set, slimming honey, flat tummy powder hair set, men booster honey, Strechmark oil and cream, hand and foot cleanser kai bari na barku haka, a tak'aice dai duk abinda kike buk'ata zaki samu insha Allahu guarantee ga kyau ga sauk'in kud'i

Wani abinda dad'in ba sai kin dami kanki da maganar kud'in mota ba, Maman Meenat tanada manyan distributors a different state na k'asar duk garin da kike zaki fad'a sai a had'a ki da distributor garin.

Me yafi wannan dad'i 😍😍 nace me yafi shi dad'i y'ar uwa me kike jira har yanzu
Duk mai buk'atar sanin inda zai sami Maman Meenat akwai social accounts d'inta kamar Facebook @mum meenat organic products
Ko number ta na whatsapp kamar haka +234 915 545 5326
Maza y'ar uwa nemi naki kafin lokaci ya k'ure miki 💃💃

_____________  Batasan lokaci ya tafi sosai haka ba, saida taji jabir mai gabatar da labarun k'arfe shida na yamma ya iso ya fara gabatarwa, ta kuma yin hamma ta rufe baki tana korin shed'an da a'uziyya.

Nusaiba da zuwan ta kenan saboda aikin dare zatayi tace ya dai ASMY naganki har yanzu anan ko dai tayamu kwana zakiyi yau?

ASMY ta tashi tana gyara wuyan hijabinta tana dad'a kallon d'akin datake kafin ta kuma kallon Nusaiba tace, kar dai har kinzo aiki?

Nusaiba ta ajiye jakar hannunta a gefe tace bangane har ba, shida fa ta kusa bugawa yanxu haka. ASMY tayi zumbur ta mik'e tsaye tana zazzare manyan idanunta tamkar tayiwa sarki k'arya, sai kuma tace ina NI'IMA take?   NI'IMA? NUSAIBA ta maimaita in a confused way, kafin tace kar dai kice mun ita kike jira? ASMY tace yes ita kai.

NUSAIBA tayi murmushi tana mai neman wajen zama, kafin tace lallai kece mai zaman jiran gawan shanu, NI'IMAN da tuntuni na had'u da ita zan shiga kasuwa d'azu take ce min zata koma gida saboda bata jin dad'i.

ASMY ta kuma zaro idanu tace what? yanzu NI'IMA ta koma gida shine ta barni nake jiranta anan yini guda.

NUSAIBA ta kuma yin dariya ta juyo tace k'ila wani abin kikayi mata tayi fushi yasa tayi deciding ta punishing d'inki ta wannan hanyar.

ASMY ta d'an yi shiru na dad'i k'u kafin tace nooo! ta nufi table d'inta da d'an gudu ta zaki jakarta tayi waje, tanaji NUSAIBA nayi mata saida safe amma ko juyowa bata iya yi ba ta fita daga harabar wajen ta nufi titi tana addu'ar samun nasarar abin hawa da sauri.

Cikin ikon Allah kuwa ta samu wani taxi wanda zai shiga dei_dei wanda anan take zama, tayi hamdala tana jin k'aramin relief a tareda ita. har aka iso da ita gida tunanin ta ya tafi can wata duniyar ne. wanda ta tattare shi tas akan NI'IMA datake tsoro da fargaban ko wani abu ne yasameta.

Don haka addu'a bai bar bakin ta ba, har ta iso gida a yayinda waje yayi duhu sosai tamkar an raba dare, ta nufi k'ofar y'ar k'aramar gidansu tana kallon agogon fatar hannunta daya nuna k'arfe takwas da minti goma daidai.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 16 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TUN RAN GINI! Where stories live. Discover now