TUN RAN GINI 2

0 0 0
                                    

🎑🎑🎑🎑🎑🎑
     TUN RAN GINI
   (RAN ZANE!)
🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*EPISODE 2️⃣*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

*Da farko nayi niyyar maida shi free book, but due to rashin had'in kan da kuka k'i bani wajen comments the book would still be paid book 300 naira as said before*

_____________  Batasan lokaci ya tafi sosai haka ba, saida taji jabir mai gabatar da labarun k'arfe shida na yamma ya iso ya fara gabatarwa, ta kuma yin hamma ta rufe baki tana korin shed'an da a'uziyya.

Nusaiba da zuwan ta kenan saboda aikin dare zatayi tace ya dai ASMY naganki har yanzu anan ko dai tayamu kwana zakiyi yau?

ASMY ta tashi tana gyara wuyan hijabinta tana dad'a kallon d'akin datake kafin ta kuma kallon Nusaiba tace, kar dai har kinzo aiki?

Nusaiba ta ajiye jakar hannunta a gefe tace bangane har ba, shida fa ta kusa bugawa yanxu haka. ASMY tayi zumbur ta mik'e tsaye tana zazzare manyan idanunta tamkar tayiwa sarki k'arya, sai kuma tace ina NI'IMA take?   NI'IMA? NUSAIBA ta maimaita in a confused way, kafin tace kar dai kice mun ita kike jira? ASMY tace yes ita kai.

NUSAIBA tayi murmushi tana mai neman wajen zama, kafin tace lallai kece mai zaman jiran gawan shanu, NI'IMAN da tuntuni na had'u da ita zan shiga kasuwa d'azu take ce min zata koma gida saboda bata jin dad'i.

ASMY ta kuma zaro idanu tace what? yanzu NI'IMA ta koma gida shine ta barni nake jiranta anan yini guda.

NUSAIBA ta kuma yin dariya ta juyo tace k'ila wani abin kikayi mata tayi fushi yasa tayi deciding ta punishing d'inki ta wannan hanyar.

ASMY ta d'an yi shiru na dad'i k'u kafin tace nooo! ta nufi table d'inta da d'an gudu ta zaki jakarta tayi waje, tanaji NUSAIBA nayi mata saida safe amma ko juyowa bata iya yi ba ta fita daga harabar wajen ta nufi titi tana addu'ar samun nasarar abin hawa da sauri.

Cikin ikon Allah kuwa ta samu wani taxi wanda zai shiga dei_dei wanda anan take zama, tayi hamdala tana jin k'aramin relief a tareda ita. har aka iso da ita gida tunanin ta ya tafi can wata duniyar ne. wanda ta tattare shi tas akan NI'IMA datake tsoro da fargaban ko wani abu ne yasameta.

Don haka addu'a bai bar bakin ta ba, har ta iso gida a yayinda waje yayi duhu sosai tamkar an raba dare, ta nufi k'ofar y'ar k'aramar gidansu tana kallon agogon fatar hannunta daya nuna k'arfe takwas da minti goma daidai.

Taja gwaron numfashi tana mamakin yanda lokacin ke gudu sosai tamkar ana jansa ne.

Gidan gidane k'arama ta daidai masu k'aramin k'arfi, wanda kana shiga zaka fahimci hakan, saboda d'aid'aikun d'akin dake gidan wanda bai wuci guda uku zuwa hud'u ba.

Babu kowa a compound d'in gidan, tasan za'ayi hakan tunda tasan Umma ba hiran dare take yi ba saboda saurin baccinta, NI'IMA dai take sa ran samunta a farke.

A hankali tayi sallama a k'ofar d'akin kamar mara gaskiya, nayi mamakin ganin d'akin yanada fad'i, don har gado biyu yaci ga kuma y'ar three sitter a ta bakin k'ofa, wanda naga wani yaro a kwance akai.

ASMY ta kalli gefen datake sa ran ganin Umma anan ilai kuwa harta fara bacci, ta maida idonta kan NI'IMA dake zaune a d'ayan gadon kan cinyarta wani y'ar k'aramar system ne data maida full attention d'inta akansa.

Suna had'a ido da NI'IMA tayi kicin kicin da fuska, tareda cigaba da abinda take yi. hakan datayi bai dami ASMY ba, jakar hannunta ta ajiye a kusa da wannan yaron ta nufi wajen NI'IMA tareda zama kusa da ita tana murmushi.

Haba my NI'IMA wai waya tab'a min ke ne sweety? ta k'arashe tana mai tab'o kumatunta datake ta k'ok'arin kumburawa.

NI'IMA dake k'ok'arin basarwa amma ta kasa, ASMY is one of the people da bazata iya yin dogon fushi dasu ba.

TUN RAN GINI! Where stories live. Discover now