TUN RAN GINI! 3

3 0 0
                                    

🎑🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*TUN RAN GINI*
*(RAN ZANE!)
🎑🎑🎑🎑🎑🎑🎑
*EPISODE 3️⃣*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

_____________ Nidai zanga ranar da zaka girma a gidan nan ASLAM! haba don Allah, yanzu da gaske gabad'aya madaran nan ka juye acikin wannan y'ar kofin sai kace wani d'an gidan shugaban k'asa, ta k'arashe tana nuna wata plastic cup dake hannunsa, wanda girmanta bai wuci cikin ludayi biyu ba

ASLAM da maganar ta ko kad'an bai dame shi ba, yaci gaba da motsa tea sa da cokali, kafin ya fara sha kad'an kad'an da cokali tamkar wanda akeyiwa dole.

ASMY ta saki baki tana kallon sa cikeda mamaki, duk da cewa ba yau ya fara yi mata hakan ba, tasan halin ASLAM tun ba yau ba, yaro ne shi mai wuyar sha'ani.

Yanzu mumcy saboda na shanye madara kike kallo na haka, wannan ay sai kisa na k'ware. ASMY tayi ajiyar zuciya ta mik'e tsaye tareda ta kowa har inda yake zaune ta tsuguna tana gyara masa kwalar rigan uniform d'in dake jikinsa.

Cikin wani irin sanyin murya ta fara magana, " ASLAM d'ina! kai kafi kowa sanin irin rayuwar da muke ciki, bawai ina hana ka bane, but inason ka koyi tattali saboda yanayin rayuwa, bamu san yazai zo mana ba anan gaba, kaga idan muka cigaba ahaka wataran fa ko madaran bazaka samu ba.

ASLAM yayi shiru na y'an sakwanni yana kallonta kafin ya kuma b'ata rai, ya ajiye kofin tea, ya mik'e tsaye zuwa ga jakar makarantarsa dake rataye ba tareda yace mata komai ba, ya d'auka ya rataya a bayansa.

Bak'aken cover shoe d'insa yasa ya nufi k'ofa, still ASMY na zaune tamkar sokuwa tana kallon sa bata iya tsayar dashi ba, kamar yanda bata iya tsayar da hawayen dake tsiyaya ba daga idanunta ba.

Har ya isa jikin k'ofa sai kuma ya tsaya cak kamar wanda ya tuna wani abu, sai ya dawo da gudu ya fad'a jikinta tareda fashewa da kuka mai ratsa zuciya, bata hana shi ba, kamar yanda ta hana kanta kukan ba itama.

Cikin kuka yake magana "mumcy don Allah ki kira babana yazo mana, kinga shi kad'ai ne zai dinga taimakon mu, zai dinga biya min kud'in makaranta, ya kaini makaranta kamar yanda baban IMRAN yake yi masa kullum, mumcy bakiga yanda yara ke yi min dariya ba idan ance kowa ya kira iyayensa suzo PTA meeting, sai suyi ta ce min wai ay kowa yasan bani da baba ni cikin shege akayi aka haifeni?

Mumcy da gaske ne banida baba? kuma meye cikin shege? ASLAM stop! ta fad'i tana mai dad'a rumgumarsa da k'arfi yayinda take dad'a k'ara sautin kukan ta.

K'arya suke yi maka ASLAM d'ina, kai ma kanada baba kamar kowa, kuma kai ba d'an shege bane, duk k'arya suke wallahi k'arya suke ta k'arashe da wani irin murya daya fara dishewa saboda kuka.

To meyasa ban tab'a ganinshi ba? meyasa su IMRAN suke zama tareda baban su amma ni nawa baban baya zuwa wajen mu? kullum naje school sai yara suyi ta tsokana na wai ni d'an shege ne banida baba? Mumcy tell me the truth? da gaske ne hakan ni banida baba?

Ta kuma k'ara sautin kukan ta, taci gaba da cewa k'arya suke maka ASLAM kanada baba kamar kowa, kuma kai ba shege bane da ubanka.

To Mumcy ina yake yanzu? kice masa yazo ya d'auke mu don Allah?

ASLAM kayi hak'uri ka bar maganar nan don Allah, na rok'e ka, babanka baya kusa damu kuma kona kirasa bazai zo ba.

Saboda meye? ASLAM yayi mata tambayar kai tsaye, saboda! saboda! sai ta kuma k'ara sautin kukan ta har tana shid'ewa.

ASLAM ya janye jikinsa da nata yayinda ya bar nasa kukan yana kallon yanda take kuka har tana had'iyar zuciya tana wani numfar fashi.

Ya sanya hannayensa biyu yana share mata hawayen, ki bar kuka mumcy na, daga yau na daina saka ki kuka, na daina maganar babana ma, ko zasu zageni bazan damu ba, tunda inada ke, kuma ay ko ba madara zan sha tea laifina ne mumcy don Allah ki daina kuka.

TUN RAN GINI! Where stories live. Discover now