NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)Episode 1
_NOTED# WANNAN SHINE LITAFINA, NA FARKO WATAKILA SHINE NA KARSHE 🥹 IDAN KUN GA KUSKURE KUYI MIN AFUWAN 👏🏼_
*ALHAMDULILLAH*
*Dukkan yabo da Godiya sun tabbata ga ALLAH mai kowa mai komai, da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi mai suna "NI DA ALMAJIRINA" ina roƙon Allah ya bani ikon rubuta abin da al'umma zasu amfana da shi Amin. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Annabi Muhammad SAW*._I dedicated the whole book to MissDmk my one and only Sister🫡Thank you for your endless love,support and for also believing in me ❤️❤🔥
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
"HajjahKaka in shaa Allah nine zan zama mijin Falmata.
Wacce aka kira da HajjahKaka akala zata haura shekaru sittin a duniya,ta saki baki da hanci tana kallon sa, kafin can tace, amma Baana dai kai Dodi minal Dodi ne ko? Ato in ba Dodi minal Dodi ba kana ALMAJIRINTA ina kai ina zama mijin ta?
Murmushi Baana yayi wanda shi kadai yasan fassarar Murmushi sa, can yace HajjahKaka to shi ALMAJIRI ba mutum bane?
Mutum ne man, amma ko wacce kwarya da uwar gurbin ta, kai tsaya kaji Falmata tafi karfin ka ta ko ina, bacin makirci da mugunta na shuwari(Gidan Sarauta)da kai baka issa ka bude wannan bakin ka mai wari kace kaine mijin ta ba,tana gama fadin haka taja wheelchair inta ta shige daki.
1pm
Karfe daya rana, wata fara, doguwa kyakkyawar yarinya wacce akala baza ta wuce shekaru sha biyar a duniya ba, ta shigo gidan da salama, Baana dake wanki ya dago da fara'arsa ya amsa salamar, kafin yace barka da dawowa Hajjahna.Tamke fuska Falmata tayi kafin tace haven't I warned you to stop using that awful word? Oops na manta baka jin yaren da nake yi, well in na sake jin kace Hajjahna sai na ci mutunci ka, rubbish. Tana fadin haka ta shige cikin gida..
Murmushi Baana yayi wanda ya bayyanar da fararan hakoransa masu kyau da ban sha'awa," Baana dai baki ne, hakoransa ne kadai fari a jikin sa, harta dasashin sa baki ne wanda hakan yake kara masa kyau duk lokacin da yayi murmushi, Baana dai Saurayine matashi mai jini a jika da kuma kiran jarumi, ga tsawo ga kwari, wanda akala zai wuce shekaru ashirin a duniya.
Falmata na shiga ciki, direct dakin HajjahKaka, ta nufa da salamar ta, HajjahKaka dake tasbh ta dago tana kallon ta kafin ta dauke kai ta cigaba da tasbh.
Cikin shagwaba Falmata tace HajjahKaka nifa inaso naje Bama idan ayi wannan hutun.
Cikin tsiwa HajjahKaka tace to maza tashi kije, ki ga yadda za ayi miki koran kare a wannan bakar masaurata, yanzu duk labarin da na baki akan irin cin kashi da akayi miki baki yarda ba? amma shine kika budemin wannan burmame bakin ki kike ce min zaki? Ah ban ga laifin ki ba? Laifi nane da nabar masaurata ta gado na zauna dake..
Turo baki Falmata tayi kafin tace to HajjahKaka shikenan haka zan ta zama ba tare da sannin dangi mahaifiya ta ba?
HajjahKaka tace to dan ubanki ni dangi ubanki ne? Inasha nice dai na haifa Shafaatu?
Falmata tace amma kinsa dalilin da yasa Abba yace nazo garin mahaifiya ta kenan dan na saba dasu.
Kallon hadarin kaza HajjahKaka ta tsaya tana mata kafin can tace karya kike yi, ya turo ki nan ne sabida matsiyaciyar Matar sa dake daura ki a hanyar banza, ke tsaya kiji tunda har uwarki Shafaatu ta rasu Shuwari basu so ta ba akan auren bare da tayi to banga dalilin da yasa zasu karbe ki ba. Idan ma zaki cire wannan tunanin ki cire shi, nan ma sai da nayi da gaske kafin aka yarda na zauna dake.ato duk dangi mu ba fari sai ke, to ina ma aka taba ganin Kanuri mutum fari in banda kaddara da yasa uwarki ta bijire wa kakanta wato Sarki na uku mahaifi na kenan, ta auri wannan bahago uban naki Doctor yake ko waye ma?
