18

56 0 0
                                    

NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)

Episode 18

Whispering abu yayi min cikin kunne nayi saurin mikewa , nabi bayan sa zamu bar dakin kawai sai muka ji voice din Hajjahkaka tace

Sannun ku jarababu, yanzu ke Falmata ko kunya baki ji ba zaki saka kafa ki bi mijin ki?

Cike da jin haushi na yinkuri komawa amma be bani daman yin hakan ba, sai shi ya bata amsa da cewa Hajjahkaka saka mana albarka sai mun dawo,yana fadin haka ya ja hannun na zamu wuce

Cike da matsifa Hajjahkaka tace kije idonki ai zai raina pata,walh kuma ki kuskura ki zo min da warin gawasa daki, kai kuma idan kunyi abin ku kar ka sake ka kawo min ita jinya, dan nasan baras zaka zubar da cikin da warin gawasa.

Murmushi Baana yayi kafin yace mungode da shawarar Hajjahkaka duk zamu kiyaye .

Ni duk na kosa na je na saka kanina a ido, muna barin dakin,muka shige part insa.
Duk na zaku ya bani wayar naga my little one...

Sai murmushi ya keyi yana kallona,nikam haushi kamar ya kashe ni, sai da yagama jamin rai kafin ya fito da wayar direct facetime yayi sai ga Faruq ya bayana, cike da murna ganin kanina na fara kwalla farin ciki, hey little one wheres Abba ?

Ya amsa da yana asibiti, Bigsis dagaske kin kusa dawowa UK? Uncle B yace min zaki dawo soon, don Allah ki dawo daddy is devastated coz you aren't here with us.

In shaa Allah zan dawo little one, nayi maganar ina kuka.

Is Uncle B trying to get you out from the abductors?

Shiru nayi ina kallon Baana kafin na kalla screen waya nayi nodding head irin eh.

I really like him Sis, he's nice and sweet. Please Uncle B Ka dawomin da sister...
Baana yace remember our promise ok ? Faruq yace ok Uncle B .
Bigsis zan koma class bye.

Kukan farinciki kawai na dinga yi ganin little one ya kara girma.

Are you happy now ? Baana yayi maganar yana kallon fuskata..

Share hawaye na nayi kafin nace don Allah ka mayar dani gun family na, ka tausayamin..

Nima ki tausaya min ki fara so na , sannan ki fara min kallon mijin ki...

Shiru nayi ina kallon sa kamar ina kokarin gano wani abu, tunawa nayi da maganar Hajjahkaka, can nace ka cire tsoran ka a raina and then teach me how to love you .. Cikin raina fadi nake ina barin wannan wuje sai I'll file a divorce case,infact zan tona asirin sa yadda za akashe shi a banza.

Shafa cikina yayi yaji shi flat, kin ci abinci ?ya jikin ki ?har yanzu kina throw up ?

Cike da jin haushin tambayar sa nace eh. Ni natsana ya dinga min magana kamar wata yarsa bacin yana matsayin Almajirina.

Mikewa yayi ya tube kaki jacket dake jinsa,kafin ya cire turtle neck tie hug dake jikin sa,wanda yayi revealing duk wani mascular line dake jikin sa , ga six packs din ya fito barau barau..

Cike da tsoro nace rakani dakin Hajjahkaka.

Be ce dani kome ba,sai ma kokarin unbelting trousers da yake ,
Zubur na mike nace ka dakata da cire kayan nan,ni ka mayar dani gun Hajjahkaka nayi maganar ina hawaye ni duk tsoro ya gama cika ni , dan ko da wasa bazan so abin da ya faru wata daya da suka wuce ya sake faruwa ba, ina ma zan yarda ?

To ki taimaka kiyi min wanka don nagaji, Baana yayi maganar cikin shagwaba .

Bansa lokacin da nace walh baka da kunya Baana ni kake cewa nayi maka wanka ?

Murmushi yayi sosai wanda ya bayanar da fararan hakoran sa da bakin dasashin sa, kafin yace kunya kuma ? Daman akwai kunya tsakanin mata da miji ne ?ina sha kusan sati na kwasa ina miki wanka.

NI DA ALMAJIRINA(Our Incomplete Story)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora