14

68 1 0
                                    

NI DA ALMAJIRINA
   (Our Incomplete Story)

Episode 14

Cike da mamaki Baana yace Wacce yarinya?

Cikin tsanar da kyamar ganin sa nace ni ka fice min daga gani, nayi maganar cikin tsawa.

HajjahKaka tayi saurin cewa Baana idan baso kake cikin nan ya fita yanzu to kabar nan, danye ciki ne fa ajikin ta kake sata wannan ihun?

Hankali tashe Baana ya fito daga toilet ya nufa idan HajjahKaka take, ya zauna. Cikin taushin mirya yace HajjahKaka Don Allah ki kulamin da ita da cikin, idan kuna bukatar wani abu ku gayamin.

Yamutse fuska HajjahKaka tayi kafin can tace dazun de tace tana bukatar danderu hakarkarin rago da kunun madara.

Kallon time Baana yaga to 11, can yace to HajjahKaka zan sa akawo maku yayi maganar yana mikewa daga zaune da yake,

HajjahKaka tace ba fa danderun gashin inji ba,na gashin tukunyar kasa take so, sannan ka canza mana yar aikin nan, Walhi warin da gafin gawasa kawai ke tashi a jikin wannan figigiyar mata, kai maza ma sam ba ta ido, habawa ace ina Namiji ai me zanyi da me duwawai kamar kobiyu?

Ganin surutun HajjahKaka bame karewa ba ne yace to, tana bukatar ya'yan itattuwa?

Ba dole ba, wannan aika aika da kayi ga kuma danye ciki zuke jini ya keyi.

Cikin hanzari ya fice daga dakin yana fita, HajjahKaka ta kirani da na fito.

Fitowa nayi na zauna kusa da ita, tace to kinga yadda ake wa Namiji, idan kika tabbatar da yana sonki to sai ki hada da kissa da kisisina bawai kema ki koma Dodi minal Dodi kamar shi ba,
Ina fatan kinyi spiriyens yanzu ko?

HajjahKaka yanzu shikenan baze sake zuwa inda nake ba? Nayi maganar ina murmushi.

HajjahKaka tace to bana ce ba idan kin fi sauran matan gardi da dadi to ki dinga ganin wannan tokareren katon kenan amma kissan ki ze kora shi.
Kai Falmata ashe Baana kyakkyawar mutumin ne haka?sai yanzu nake ganin kyawun sa,ashe rashin tsabta ne da kula yasa ya tirke,bakinkirin amma yanzu dube shi duk ya koma bakin balarabe

Rai bace nace to ina ruwana da wani kyaunsa HajjahKaka?

To wa ya san miki ko kyaun sa ne ya rijanye ki, kika daga masa patarin naki ya miki abin manya?

Fashewa nayi da kuka...

Sakin baki tayi tana kallona kafin can tace Walhy karki zama me spiriyens ki zama Dodi minal Dodi, Allah dura miki ciki zeyi kin ga zama ya kamaki annan.

Share hawaye na nayi kafin nace me abin so a wannan kazamin dan ta'adar ?ko bata rayuwar yammata da su keyi yaci ace tsine masu akeyi amma shine zaki wani ce wai kyaun sa ne ya rudeni?

To ya isa haka kafin ki batamin rai nakasa cin danderu, HajjahKaka tayi maganar tana kokarin kwanciya, taimaka mata nayi ta kwanta.

Sai wajan 2 dare aka aiko da wannan danderu, HajjahKaka kamar wata mayya ta mike ta soma cin kayan ta

Washe Gari

Journalist Bintu da wuri tabar gida sai parara gudu take akan titi har fita kan titi bata dena gudu ba, saida ta shiga wani jeji kafin ta ja birki ta tsaya, sai raraba ido take, can sai ga wani bakar BMW ta taho ta tsaya daide inda tayi parking.

Wayar ta ne ya fara kukan Kira, ta amsa a tsorace, ko seconds ba tayi da amsa wayar ba ta fito ta shiga BMW, tana shiga driver ya jata, saida sukai tafiyar kusan hour daya, kafin yayi parking, sake kiran ta akayi a waya, ta dauka cikin hanzari, amsawa tayi da to, kafin ta fito daga motar, tafiya ta dinga yi har ta issa wani camp, ta tsaya daide wurin.

NI DA ALMAJIRINA(Our Incomplete Story)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora