Page 1

25 0 0
                                    

     💋JANAN 💋
(The Captain Family)

©️®️Hafsatouamjad.

The Writer Of .
BANI DA ZABI .
TAREEQ.

NOTE !
This novel is a work of fiction ,any resemblance of story or lifestyles should be considered as a coincidence.

Page 01.

K’arfe biyu daidai black Siena yayi parking a babban parking space din dake cikin wani qayattacen gida ,babu bata lokaci yaran suka fara fitowa ko wanne Da uniform ajikin sa se kuma lunch box dinsu dake rike ahannun su, Manyan ne da shekarun su basu gaza 18 ba suka Mara musu baya , Islam ce rike da hannun Janan tana ce Mata “Zan shigo anjima Dan Maths dinan fah ba ganeshi nayi ba “
Murmushi janan tayi tace “Toh Isssy “...

Da sauri Janan tayi kasa har lunch box dinta ya fadi sakamakon Bangaxarta da Ya Khadija tayi , Dagowa issy tayi tace “Haba ya Khadija sekace bakya gani , zaki wani bangaje mutane “?
Juyowa tayi a fusace tana nuna Issy tace “Na bangaza din ko zaki rama Mata ne rasai “?
Murguda baki Issy tayi tana dage kanta sama tace “Eh din zan rama matan “

Gudu ta saka ganin yanda Ya khadija Tayo kanta tana huci,tasan tabbas ta kamata zata ji ajikinta, ahaka suka fara zagaye faffadan compound din gidan har Issy ta samu ta shige ciki .

Daukar lunch box dinta ta zugunna tayi tana karkade jikinta , batare da ta kalli ragowan da suka bita da harara ba tayi shigewarta ciki tana tafiya ahankali kamar yanda ta saba , Toh me ze dameta? Halin yayunta duka ba bak’o bane a wuri ta idan Da sabo tariga Da ta saba da hantarar su da musguna Mata Da suke daga su har iyayen su , ko a makarnta bata tsira ba haka zasu hado kan kawayen su suzo suyi Mata cin mutunci kamar basu santa ba , amman duk da Haka ita bata tabajin wani abu me kama da haushin su ba ,kasancewar Maamah na iya kokarinta wurin bata ingantacciyar tarbiya Da nuna Mata muhimmancin su awurinta .

Da salllama ta shiga cikin babban parlour nasu daya kaure Da kamshi tun daga kofa ta cire baby hijjab dinta ta wulla shi kujera da sauri ta karasa kusada stand Ac dake parlour ,takai fuskanta jiki tana lumshe ido lokaci daya sanyin Ac yana ratsata, ta dauki atleast 5mins kafin ta matsa awurin ta nufi dining ta ajiye lunch box dinta ,kitchen ta nufa Da Murmushi a fuskanta ta shiga ciki , juyowa Mamah tayi tana amsa sallama manta tace “Kun dawo kenan “?
Gyada Mata kai tayi tana cewa “Mamah yau me kike dafawa kamshi tun daga  Gate “

Murmushi Mamah tayi tace “Your favorite “
Ihu Janan tayi tana rungume Mamah tace “Allah kamar kinsan shi nake so naci “.
Juyowa mamah tayi itama Murmushi kwance afuskanta tace “Shiyasa na miki ai ,go and dress up first “

Sakin Mamah tayi ta fito da sauri ta nufa hanyar dakin ta , uniform din ta fara cirewa ta sakasu cikin laundry basket dake corridor toilet dinta sannan ta shiga toilet din , bata wani jimaba ta fito daure Da karamin towel Doguwa rigar atamfa ta saka ta feshe jikin ta Da turare sannan ta daukko Chantily cap ta saka ,kwata kwata batason dankwali acewarta takura Mata yake ko unguwa zasuje se Mamah tayi da gaske take daurawa .

Parlour ta fito time din Mamah ta gama girkin ta jera akan dinning ,Seda ta cika cikin ta sannan ta koma cikin parlour ta zauna tana ma Mamah Santin yanda abincin yayi dadi .

Suna shigowa Dakin Ya Khadija tace “Momy kiyiwa Issy magana ta raina ni Wallahi zan karyata kwanan nan “
Issy da ta buya abayan Momy ta Leko tace “Bismillah Dan halak ya fasa ,wanda be fasa ba ya raina..”
Momy ta katseta Da cewa “Wallahi kika karasa sena fasa miki baki mara kunya ,Dan ban Mika Mata Ke ba taci miki uba“?

Zunbura baki Issy tayi tace “Momy itace fah babu abunda janan ta mata ta bangajeta Seda ta fadi “

“Toh Ina ruwanki Dan ubanki Ke ta bangaje banson shiga sharri ba Shanu fah Issy “

JANANWhere stories live. Discover now