Page 2

5 0 0
                                    

©️®️Amjad.

     💋JANAN 💋
(The Captain Family)

This book Isn’t for Free it’s just 500 ,contacts me Via 08100312134 charts only no call .

Page 02.

Seda ta gama gyara duk inda ya dace kama daga bedrooms dinsa dake part din duka da parlours din suma sannan ta wanke toilet ,Seda ta gama tayi mooping sannan ta hada undies dinsa ta wanke su ya tarasu da yawa kuma su ragowan matan nashi basu damu da wanke mishi ba , acikin toilet din ta shanya su sannan ta fito zuwa lokacin ko Ina ya dauki haske , rage Ac main parlour tayi ta kashe globes sannan ta janyo kofar part din .

Da yamma tare suka shiga kitchen da Janan bayan ta dawo daga islamiyya girki kala uku sukayi for dinner tunda yau girkinta ne kuma gaba daya ake haduwa ayi dinner ,ko wacce acikin su ranar Girkinta harya kare dinner na duka gidan zatayi .

Se Magrib suka gama komai suka zuba a Manyan warmers Janan ta jerasu a katon basket din da suke zubawa .

Suna parlour Dady yayi sallama suka amsa duka suna welcoming nashi kamar yanda suka saba ,Da kulawa yake amsa musu idanun shi akan Anty da tayi kyau sosai cikin laces maroon dinki half bubu da straight sicket ba wani kwalliya tayi ba na azo agani ba powder ne kawai da lipstick amman ba karamin kyau tayi ba .

Dauke idanun shi yai akanta lokacin da take amsar jakar Hannun shi ta wuce gaba ya biyota abaya .

Ita ta taimaka mishi yai wanka kamar yanda ta Saba ya shirya cikin jallabiya .

Tare suka fito daga dakin ,Anty ta wuce wurin babban dinning dinsu da yake cin sama da mutum 30 .
  Da sauri Janan ta taso ta fara tayata jera abincin ,daya bayan daya suka zazzauna akan dinning din ,kowa ya fadi abunda yake so Janan tayi serving nasu ,
  Janyo plate din gaban Dady Anty tayi ya kalleta yace “Ki bari mamana ta zubamin mana”
Murmushi Janan tayi ta dago tayiwa Anty gwalo,ta nufa wurin Dady kwafa Anty tayi ta zauna a kusa da kujeran shi .
   “Dady daman kafison Janan “
Da sauri suka dago gaba Dayan su suna kallon Ihsan Jin furucin da ya fito daga bakinta ,sosai Dady yai mamakin jin wanann maganar yanada tabbacin Manga bazatayi wannan tunanin ba sede idan fada mata akayi .

Tsaya mishi lomar da ya ke bakin shi yai acikin makogaron shi ,lokaci daya wani takaici ya rufe shi ,ko kadan baya son abunda ze taba hadin kan yaranshi yana iya kokarin shi na ganin ya kwatanta adalci “Waye ya fada miki haka ,me nake mata da ke bana miki Hauwa,“?
Dady ya jefa Mata tambayar ranshi na suya yana Allah wadai da halin iyayensu ,yana tufka suna warware mishi .

Ahankali manga da harta fara tsiyayayr da hawaye tace “Am Sorry Dady I didn’t mean to hurt you “

Sauke ajiyar zuciya yai yace “Daga yau banson sake jin irin wannan maganar gaba Dayan ku ina sonku kuma babu wadda nafiso “
Gyada kanta tayi tace “Insha Allah”.

Ummah da ranta ya baci ta Kalle shi wani kululun bakin ciki yana tsaya Mata a makoshi tace “Gaskiya ce dai baaso amman komai a bayyane yake “

Har suka gama cin abincin babu wanda ya sake magana acikin su ,se Ummah da taketa kwafa gaba daya ranta ya baci kuma taso Alhajin ya kulata ta fadi maganganun dake ranta .

Seda suka gama Janan ta kwashe kayan gaba daya ,yau babu wanda ya tsaya hira saboda Malam yazo duka suka wuce parts dinsu Dan dakko qurani da sauran dirasat din da Malam ke musu .

Anty da kanta ta kara gyara parlour sannan ta shiga ciki ,gyaran drawer sa take so ta masa Dan kayan sunyi yawa aciki kuma basa samun gyara.

Kayan ciki ta fara fito dasu masu bukatar ninki tana ninkesu.
   Ganin ya fito ne yasa ta ajiye kayan hannunta ta nufo shi kallonta yai yace “Kici gaba da aikin ki kawai zan shirya da kaina “

JANANWhere stories live. Discover now