page 4

12 0 0
                                    

©️®️Amjad....

    💋JANAN 💋
(The Captain Family)

This book isn’t free it’s just 500 contacts me via 08100312134 ‘Yar uwa ki daure ki biya dari biyar dinki ki karanta cikin salama,inada tabbacin baza kiyi nadama ba domin jigo ne na abunda ke damun mata a wannan k’arnin ,koda ke bakya cikin irin wnn matsalar to tabbas ‘Yar uwarki ko wata a dangi ku tana fuskantar makamanciyar ta .

Ya tambayeta yana zuba Mata idanun shi Da suke dauke Da wani bacin rai .

“Ba haka nake nufi ba Dadyn su “

Katseta yai yace “Tashi kije “. Zuciyan shi yana tafasa,a wurinta ne kawai yake samun peace of mind amman itace zata budi baki ta mishi wannan magana ta fishi sanin ya kamata ne. ?

“Ki tashi kije nace ,ki tarkata kayan abincin ki ki tafi “.

Ya fada yana kauda kai .
Kamar yanda yai zato kuwa ko kusa batayi yunkurin tashi ba sema sadar da kanta da tayi kasa tana jin babu dadi na bata mishi rai ina laifin me kaunar ka ? Kuma ta tabbata tunda ya nemi abinci awurinta be samu awurin Momy ba , amma ita abunda zeje ya dawo take gudarwa Kanta ,tunda fita yake yabarta da su kuma banda wannan Ma bazataso ta shiga lokacin wata ba kamar yanda itama Bata jin dadi In an Mata Hakan. 

Runtse idanun shi yai yana sauraron sautin kukan ta dake fita Ahankali,ji yake kamar ana zuba mishi barkono a cikin zuciyar shi ,bayason kukan ta ko kadan Wannan shine rauninshi ,baze iya cigaba da sauraron kukanta ba amman so yake ya hukunta ta,tayanda ko nan gaba bazata sake ba .

Mikewa yayi rike da wayarshi ya fara takawa Dan shigewa bedroom dinshi .

Tsayawa yai cakk zuciyan sa na bugu da sauri jin yanda ta d’afe jikin shi ta rungume shi ta baya tare da daura kanta abayanshi tana cigaba da kukanta .
“Kayi hakuri bazan kara ba “
Ya jiyo Amon muryanta yana kai kawo cikin kunnenshi.

Be tsaya bin Umarnin zuciyar sa ba ya juyo da sauri tare da rungumeta sosai yana pating bayanta slowly .

Yasan bashida tamkar ta aduk duniya ita kadai ce bata mararin ganin bacin ransa,ita kadai ce take gudun abunda ze masa kutse cikin farin cikin sa, shiysa ta samu matsayi me girman gaske a zuciyar shi ,shifa yasan baze iya rayuwa babu itaba,baze ma iya dogon fushi da itaba duk girman laifin da zata mishi .

“Am Sorry for hurting you fatee na “.
Da sauri ta girgiza kanta tace “Ni na maka laifi Ina neman gafarar ka “.

“Na yafe miki “.

Murmushi ne ya subce mata tace “Nagode mijina “

Jan hannunta yai yace “Muje abani abinci karna zauce da yawa “.

Ita ta bashi abincin abaki kamr yanda ta saba Seda ta tababtar ya koshi , sannann ta barshi .

Tare suka wuni adaki tana ta debe mishi kewa , ko nan da can yaki barinta taje sallah ne kawai ke tada su . Bayan sallah azahar ya kwanta bacci yana kwance a cinyarta, ko kwakwaran numfashi batayi saboda karya farka .

Be tashi ba se gab da laasar, shi ya fara bude idanun shi yana kallonta ganin yanda ta jingina da jikin gado ,still itama baccin take , mamaki yake karde ace all this while ahaka take zaune at least awa biyu kenan . ?

Hannun shi yakai ahankali yana shafa lallausan kumatun ta ,idanunta ta fara budewa a hankali harta gama budesu akan shi .

Da sauri ta karasa budewa tace “Ka tashi “.?
“Allah ya miki albarka ina alfahari dake Fatima “.

Murmushi tayi tace “Amin “
Saukkowa yai daga kan gadon yace “Zomuyi alwala muyi sallahn zan fita ne Nima Yanzu “

Tare sukayi alwalan yajasu jamii sukayi sallahn ,Da kanta ta taimaka mishi yai wanka , duk da rabin wankan lamura ne suka wakana 😉 cikin shadda getzner ya shirya ruwan Toka se fitar da kamshi yake ya daura hula Tangaran akanshi ruwan toka da ratsin blue black da kuma milk ajiki .

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 19, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

JANANWhere stories live. Discover now