BABBAN GIDA
11
"Kin gama gudun ne?".zuciyan ta wani irin buga wa yayi a rikice tace
"Ya--ya Nasir san-nu da zuwa".
Murmushi yayi wanda ya kara nuna kyawun fuskar shi.
Da sauri ta juya zata fita ya tashi kafin ta fita yaja hannun ta ya tura kofar sannan ya tsaya dab da ita.
Saukar da kanta tayi tana jin yanda zuciyan ta ke buga wa dan tsoro.
Sa hannu yayi ya ɗago fuskar ta suka haɗa ido se yace"ya kike?".
"Lafiya na kalau".ta faɗa tana kara mannuwa da bangon Bayan ta.
Murmushi yayi ya fara shafa fuskar ta da hannun shi ita kuwa har hawaye sun cika a idonta ahankali tace
"Ya--ya Nas---ir umma tana kira na".
Matsa wa yayi daga kusa da ita sannan yace"je ki zanzo da kaina".
Da sauri ta fita daga ɗakin zuciyan ta se buga wa yake yi.Direct side nasu taje inda ana shirin tafiya da amare side nasu.se kuka sukayi tun Bama Jamila ba da har Muryar ta ya toshe dan kuka.
Aka kai su parlour na Alhaji ya musu nasiha me shiga jiki sannan sukayi sallama da iyaye aka kaisu mota.Gate na gidan yana cikin babban gida,estate ɗin babba ne da side daya wa wanda aka gina dan yaran.
Haka aka shiga dasu gidan suka kai su side nasu wanda yake kallon juna.gida Masha Allah ya ginu ko wanne beni ne daban daban guda 20.
Side na Farida komai fari ne na Jamila kuma komai ash ne.ko wani side akwai wurin parking na mota wanda ze ɗau akalla mota huɗu.akwai fili a gidan se da garden babba ta gefe.sauran side ɗin empty ne.Haka suka shigar da Jamila se kuka take yi sunyi rarrashi har sun gaji.anam bata tsaya ba kawai ta koma babban gida.tana shiga ta haɗu da ayban dake hira da Yasir.
Zuwa tayi wurin shi tace"yaya ayban ɗazu ka kirani amma dana je baka ɗakin".
Ayban yayi murmushi yace"daman Nasir ne yace in kira Mishi ke dan bai ganki ba,baki Ganshi bane?".
"Na Ganshi".tana faɗan haka ta bar wurin,side nasu taje ta zauna a parlour dan sauran duk suna gidan amare.
Majid ne ya shigo yana cewa
"Adda Anam mami tana kiran ki".
Anam tashi tayi ta wuce side da aka ba wa mami.
Tana shiga ta wuce ɗakin da sallama.mami ta amsa mata sannan tace"yawwa Anam daman tunɗazu ina neman ki,gashi kije ki bawa Jamila".ta gama maganan tana miƙa wa Anam wani gift box me kyau.
Anam murmushi tayi sannan ta karɓa ta fita.
Ahankali take tafiya har ta iso sannan ta shiga side na Jamila.
Haryanzu dai Jamila kuka take yi.anam ta zauna kusa da ita ahankali tace"haba Jamila kukan nan ya isa mana kinsan yaya harun in yazo yaga kina kuka ƙara Miki zeyi".
Jamila share hawayen ta tayi ta ɗaga ido ta kalle Anam sannan tace
"Anam kinsan bana son yaya harun ko auren nan".
Anam hugging nata tayi tace"kiyi hakuri kiyi wa mijin ki biyayya,kiyi duk abinda yace kiyi karki saɓa Mishi"Jamila gwaɗa kai tayi sannan Anam ta miƙa mata gift box ɗin tace
"Inji mami in kawo Miki".
Murmushi tayi sannan Anam ta tashi zata tafi khairat dake zaune akan kujera tace
"Baza ki tsaya se anjima mu tafi ba?".
Anam karkaɗa kai tayi ta fita ahankali take tafi har ta isa side nasu.
Tayi wanka tasa rigan bacci da bai wuce cinyarta ta ba ta kwanta.Bayan minti kaɗan taji an buɗe kofar ita taɗau su khairat ne so bata motsa ba sanda taji ƙanshin turaren shi a razane ta tashi taga Nasir na tsaye a kofa da murmushin shi me ɗaukan hankali amma banda nata.
Ahankali ya fara takowa har ya iso wurin gadon ta ya zauna.matsa wa tayi se yayi murmushi yace
"Nace zanzo shine harkin kwanta".
Ƙara matsa wa tayi dan ba halin tashi kayan ta bayi da tsayi.
Ahankali ya fara matso wa kusa da fuskar ta har suna jin nunfashin juna da sauri Anam ta tashi a razane tace
"Ya--ya Nas---ir da--nallah ka bar-ni bacci nake ji". murmushi yayi ya kalle ta sama da ƙasa sannan ya tashi taka wa har inda take yayi se yace
"Ai yanzu tunda nazo bake ba bacci".
Ze riƙe hannun ta da sauri ta fita a ɗakin ta shiga ɗakin su alisha da haryanzu basu dawo ba.
Zuciyan ta se buga wa yake yi tana Allah Allah wani yazo.
Kawai taji an buɗe kofar wani razana tayi da sauri ta ɗauka wani hijabi dake kan gadon fiddat tasa,shi kuwa kallon ta yake yi.
Sanda tasa hijabi sannan yace"yunwa nake ji kizo ki bani abinci".
Gwaɗa kai tayi tana jira ya fita amma yana tsaye.
Murmushi yayi yace"baza kije bane?".
Da sauri tazo ta wuce ya bita a baya,sanda suka je kusa da main kitchen sannan yace"ki kawo min ɗakin ayban". yana faɗa ya wuce.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.