BABBAN GIDA
18
"Na farko zan haɗa auren Mansur da ilham se salis da Amina se Abdul da kauthar inshallah nan da wata biyu".
Wasu sunyi mamaki wasu kuma basu yiba.salis tashi yayi ya fita se Anam ma ta bishi.a garden ta same shi yana zaune ya riƙe kanshi.da sauri ta zauna kusa dashi da damuwa a fuskar ta tace"yaya baka da lafiya ne?".
Salis ɗaga kai yayi ya kalle ta cikin ido yace"Anam ne bana so na aure Amina Ni ke nake so".
Anam dan tsaban mamaki ko motsi ta kasa yi kawai kallon shi take dan bata ma san me zata ce ba.
Shiru ne ya biyo baya.
Chan se Anam tace"yaya hakuri zakayi ai daman ba ko wani abinda kake so zaka samu ba".
Murmushi baƙin ciki yayi yace"Anam tun da kike karama nake son ki amma na kasa faɗa Miki dan nasan Ni a matsayin yayan ki kika ɗauke Ni".
Anam tace"ya--ya--".kasa magana tayi ta tashi zata tafi ya riƙe hannun ta se shima ya tashi yace"Anam na sani bakya so na amma dai yau nayi farin ciki dana faɗa Miki abinda nake ji akan ki".
Anam tace"yaya salis ai ko yaushe kai yaya nane kuma a haka zaka zauna".
Tana gama faɗan haka taja hannun ta ta wuce side nasu inda ta same Amina da kauthar se farin ciki suke dan sunji daɗin zaɓen da Alhaji yayi musu.
Shiga ɗaki tayi ta kwanta.A parlour kuwa hira suke kamar haka.
"Nikam gaskiya Alhaji bai kyauta min ba".ilham ta faɗa tana ɓata fuska.
Baby tsaki taja tace"me laifin yaya Mansur".
Ilham tace"Ni kawai bana son shi ne".
Amina dake ta fara'a tace"ohon Miki nidai daman tun da ina crushing akan yaya salis gashi yanzu Allah ya bani shi".
Kauthar ma da farin ciki tace"nikam daman mun taɓa soyayya da yaya Abdul".
Mamaki duk sukayi dan ko da wasa kauthar bata taɓa faɗa musu ba.
Fatma da mamaki tace"daman kin taɓa soyayya da yaya Abdul ne bamu sani ba?".
Kauthar dariya tayi tace"ehh lokacin da nake ss2 ne mukayi soyayyar shekara biyu se muka rabu".
Khairat tace"to yanzu kina tunanin yana son ki ne?".
Gwaɗa kai kauthar tayi se suka cigaba da hiran su.Canada.
"Bakusan me ya faru ba".iman ya faɗa yana fitowa daga ɗakin shi.
Ayban dake danna laptop nashi yace"me kuwa ya faru?".
Iman zama yayi yace"ai kun san auren su Yasir saura sati ɗaya kuma za'ayi meeting".
Gwaɗa kai sukayi se Farid yace"an kara wani auren ne?".
Iman da zumuɗi yace"an haɗa auren Mansur da ilham se salis da Amina se Abdul da kauthar".
Ba wanda yayi mamaki dan inda sabo sun saba.
Haidar yace"toh Allah ya nuna mana".sukace Ameen se Jamil ya tambaya"yaushe ne auren?".
Iman yace"nan da wata biyu".
Farid yace"mesa Alhaji yake sawa kaɗan kaɗan".
Malik yace"nima abinda na gani".
Muffik dake fito wa daga ɗakin shi yace"maybe yana so ya aurar da kowa da wuri ne".
Haidar yace"kuma haka ne dan ai wanda ya wuce wata uku yasa,nasu Jamila ma ai kusan wata shida yasa".
Kalil shima fitowa yayi daga ɗakin shi yace"maganan auren nan ya isa ku tashi mu tafi".tashi sukayi suka fita.Harun da Jamila.
Kwance take a ɗakin ta tana danna waya.muryar harun taji yana kiran ta.tashi tayi ta wuce parlour ta same shi a zaune yana kallon tv.
Kallon ta yayi sannan yace"je ki kira min Anam"
Fita tayi ta wuce side nasu Anam.
Tana shiga ta same su suna hira amma bata ga Anam ba.
Se ta tambaya"enmata ina Anam?".
Sumayya ce ta nuna ɗakin su Anam.
Ahankali Jamila taje ta buɗe kofar ta same Anam a kwance tana kallon wuri ɗaya.
Jamila tace"Anam baki da lafiya ne?".
Anam tashi tayi ta zauna sannan tace"lafiya na kalau".
Jamila gwaɗa kai tayi sannan tace"yaya harun yana kiran ki".
Anam tashi tayi suka wuce side nasu Jamila.Tana shiga ta tsaya a kusa da harun tace"yaya gani nan".
Kallon ta yayi Sannan yace"kalil yace in haɗa ki dashi a waya".
Taɓe baki tayi amma batayi magana ba.
Harun kiran kalil yayi sannan ya miƙa mata wayar.
Kalil ta cikin wayar yace"kije ɗaki na a drawer zaki ga wani envelope kije ki bawa Laminu wani ze zo ya karɓa".
Ahankali tace"toh yaya".
Katse wayar yayi se ta miƙa wa harun,se harun yace"kije ke da masir gidan Alhaji Ismail wata zata baku saƙo na".ɓata fuska tayi ta fita tana ta mita har ta iso side nasu Majid.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.