BABBAN GIDA
35
"Haba ayban dan Allah ka rage abunda kake wa yarinyar nan,kaji dai abinda doctor ya faɗa". haidar ya faɗa da ɓacin rai.
Suna zaune a asibiti a ɗakin da aka riƙe hamra.
"Yaya gaskiya abinda kake yi yayi yawa". Anam ta faɗa tana kallon shi da haushi.
"Hamra kinsan abinda nake bukata,idan kikayi shikenan zan barki,ke ma kinsan ina son ki sosai shesa nake Miki Abinda nake yi".ayban ya faɗa yana kallon hamra dake kwance tana hawaye.
"Yaya so nawa zan baka hakuri,so nawa zan tsuguna na nema yafiyan ka,so nawa zanyi kuka a gaban ka akan ka yafe min?".hamra ta tambaya tana kallon shi hawaye na zuba a idonta.
"Bakiyi abinda nake so ba hamra ke ma kin sani". ayban ya faɗa.
"Yaya kasan ban kara kallon shi ba tunda abun ya faru".hamra ta faɗa tana zama.
Shekaru hudu da suka wuce.
"Hamra zo in faɗa Miki wani abu".ayban ya faɗa yana jan hannun ta wurin motan shi.
"Toh yaya ina jin ka".ta faɗa tana kallon shi.
"Akwai abinda nake so na faɗa Miki da daɗe wa amma ina jin shekarun ki bai kai ba shesa amma yanzu zan faɗa Miki".ayban ya faɗa yana kallon ta cikin ido.
"Toh yaya".ta faɗa tana sauke kanta.
"Hamra ya daɗe ina son ki but na kasa faɗa miki,i really love you hamra".
Shiru tayi tana kallon shi ta ma rasa me zata ce.
Chan se ta cire tsoro tace"yaya akwai wanda nake soyayya dashi,wanda yafi min kai so dubu kuma shi nake so na aura mu zauna har karshen rayuwa na.me zanyi dakai?,yaya kasan ko maza sun kara a duniya bazan taɓa son ka ba,bazan taɓa jin son ka a zuciya na ba".ta gama maganan tana jan tsaki sannan tabar wurin.
Ayban Binta da kallo yayi harta bar wurin sannan a fili yace"inshallah se nasa kinyi nadaman abun da kika faɗa hamra wannan alkawari ne,se kin tsaya a gaba na kina bani hakuri hamra,se na maida rayuwar ki abun tausayi har se ranan da kika ce abinda kikayi ba daidai bane Ni kaɗai kike so kuma zaki aure".
(Ranan auren su mira).
"Salamu alaikum".ayban yayi sallama yana shiga parlourn Alhaji dasu baba da sauran duk suna wurin.
Amsa sallamar shi sukayi sannan ya zauna.
"Alhaji ina so na faɗa maka wani abu".ayban ya faɗa yana kallon Alhaji.
"Toh ayban ina jin ka". Alhaji ya faɗa yana maida hankalin shi wurin ayban.
"Alhaji daman da daɗe wa Inason hamra shine nazo akan a bani auren ta in zaka Amin ce".ayban ya faɗa yana kallon Alhaji ba kunya.
Sosai duk iyayen suka nuna farin cikinsu.
"Masha Allah ai daman haka muke so ayban,kasa a ran ka hamra matar ka ce inshallah".
****
"Salam mu shigo ne?".alisha ta faɗa suna tsaye a kofar ɗakin ayban."Ku shigo mana".hamra ta faɗa ta cikin ɗakin.
Shiga sukayi sannan suka zauna kusa da ita.
"Ya jikin ki?".fatma ta tambaye ta.
"Ai na warware sosai". hamra ta faɗa tana murmushi.
"Kin bawa yaya hakuri ne?".Anam ta tambaya.
"Hmm ke dai ki bari ba irin hakurin da kike tunani bane".hamra ta faɗa tana kallon Anam da rashin damuwa.
YOU ARE READING
Babban gida
RandomKu biyoni cikin labarin babban gida masu ban mamaki da sirri karku bari a baki labari. Labari ne akan wani gida da suke da haɗin kai,suna zama a kwanciyar hankali,amma fa akwai sirriku daya wa a cikin gidan.