24

991 27 6
                                        

EPISODE 2️⃣4️⃣

Kawai tausayi taji tabama kanta saisa takasa rike hawayen dan tana cikin jarabawan rayuwa, she's 30 batai aure ba babu miji, kowa is pressuring her, her biggest support, her biggest fan is her best friend Ni'ima da tun suna yara suke tare, kawancen amana da iyayensu sun zama daya ma, she's not a small girl when she sees love she knows love, wani irin kaddarane wannan? Baban Yaseer can never be her amsa nooo please Ya Allah not my best friend's husband, ganin hawaye yakasa tsayawa daga idanunta asanyaye Aliyu yace "I'm here for you, I will forever be right here! Ina taredake Hawwa in good times and bad times, dare da rana, I'm right here" ahankali yadaura hanky kan fuskanta wani sanyi taji dayasa ta lumshe idanunta da sauri takai hannunta i ta karbi handky tana goge fuskanta, tadanja majina dadan ragowan karfin zuciya tace "maisa kabiyoni Baban Yaseer? Nace kabiyoni ne must u follow me everywhere? Must you get involved in my issues? An gayamaka I can't take care of myself ne ko I need your protection"? Ataushashe yana kallonta ganin ranta abace, cikida zazzafan kauna yace "sabida bazan taba iya bacci ba bayan nasan kina irin wannan hanyan, I care for you" ahankali Hawwa tace "wat if something happens to you"? Asanyaye yace "I don't care koma menene yasameni I just wanna keep u safe" abu tahadiye a wuyanta sai kawai ta juyo ta yunkuro tace "I need to change my tire, spare tire na booth" matsamata yayi tafito tai booth yabi bayanta tana bude booth din takai hannunta zata dauki tayan yarigata dauka yace "let's go muje motana ki zauna" tsayawa tayi tana kallonshi, "muje dan Allah Hawwa dare ne mu kadai a titi" batai musu ba yayi wajen motanshi da ita yabude mata gaba ta shiga ta zauna ya maida yarufe sannan yadawo booth nata yaciro supanu yaje gaban motan yana kwance tayan dayay less, sosai  Hawwa take kallonshi kaman yauta fara ganinshi abubuwa da dama suna yawo aranta, tana zaune awajen saiga yan sanda sunzo wajen fitowa tayi ta nuna musu ID card dinta tayasu gyara tayan sukayi, suna gamawa Baban Yaseer yabar musu motanshi yabasu kudi su tsaremai sannan  yashiga na Hawwa, hakan yasa ta zagayo ta zauna ya kunna motan yaja waje tajuyar da kanta tana kallo ahankali yace "do you think is right kije kidan Anty ki middle of the night? Kodai idan mukaje zaria namiki booking hotel, idan gari yawaye saikije"? Tana kallon waje batare data juyoba tace "zan iya zuwa wajen Ammi na anytime anyday" gyadamata kai yayi bai sake magana kusan 30min sai chan yace "Hawwa it's okay not to be okay" lumshe idanu tayi tabude anatse yace "you got this! Karki bari kalaman Baba natabaki, karki karaya, I hate seeing you like this" yadan kalleta yanda take kallon waje yace "kinji" gyadamai kai tayi daganan basu sake magana ba harsukakai zaria, nunamai hanya tadingayi har zuwa wani gida a wani anguwa mai dan kyau da mutunci, saukowa tayi ta zagayo tadan kalli Baban Yaseer dake kallonta tace "dan bani car key" zare key motan yayi yabata yana kallonta, a gate tasaka wani key dake jikin motan tabude kofan tashiga ciki tana sallama tsakar gida ne mai fadin gaske, tourchlight taga an haskewa taji muryan yan dattijuwa na "waye awajen gate din nan" ana bude kofa da gudu Hawwa tai wajen kofa matan na bude kofa dadan charbi a hannu Hawwa ta rungumeta da karfi tace "Ammiiii na" ririketa matan tayi tace "Hasbunallahu wa ni'imal wakeelu Hawwa kece da daddaren nan, ke tashi kiga na ganki lafiya Hawwa" tadago Hawwa daga jikinta murmushi Hawwa tayi tace "Ammi baban Naseer na waje bani key gate na bude ya shigo da mota saiya dan zauna zuwa safiya yakoma Abuja" wani dan kallo Ammi tamata tace "Baban Yaseer kuma? Aliyun Ni'ima"? Gyadamata kai Hawwa tayi Ammi tabata key fita tayi Ammi itama tafito tana haskawa bude gate din Hawwa tayi yashigo da motan ta maida gate din tarufe Ammi tace "maraba da Baban Yaseer, sannunku sauko sauko" Saukowa yayi kanshi akasa cikeda kunya yace "Ammi mun sameku lpy" cikeda fara'a tace "Alhamdulillah ina jikokina? Da y'ata Ni'ima hope duk suna lpy"? Akunyace ya gyadamata kai yace "Alhamdulillah" murmushi tayi tace "muje nakaika side din su Baffa ka kwanta bazakabi hanya da tsakar daren nan ba sai idan Allah ya kaimu da safe akawo maka abinci ne"? Dasauri yace "a'a Ammi dare nayi bana iya kara cin abinci" satan kallon Hawwa yayi dake gefen Ammi tana wasa da hannunta yamika mata car key ta yace "take" dan dagokai tayi kafin tasa hannu ta karba Ammi tace "muje" suka wuce suna hira itakuma tawuce wajen motar ta booth taciro akwatinta ta gu huri ta shiga dashi ciki, bayin Ammi tafada tana cikin wanka Ammi tashigo tasami waje ta zauna yanda ta ganta haka tasan dawani abu.
Towel din Ammi ta dauro tafito Ammi ta kalleta tace "zonan Jidda" kayan shafanta tadauka tazo kusada Ammi ta zauna tana bata cream dinta a hannu Ammi ta karba tana sauke ijiyan zuciya tace "meya faru?" Dan shiru tayi sabida kawai taji komi yadawo mata sabo, hannunta Ammi takama tana shafa mata mai kafin takalleta strictly tace "ya akayi kike tare da mijin kawarki at this type of time and day Hauwa'u"? Baki tabude zatai magana saikuma tadan sauke ijiyan zuciya Ammi tace "speak" anatse tace "Ammi wlh I don't know cus ni ko kiran Ni'ima ma banyi da abun yafaru ba, probably Baba ne yakirasu to check ko ina gidansu, saita kirani daga gayamata ina hanya zanzo wajenki hala to shine ta turoshi" Ammi na kallonta ta sauke ijiyan zuciya tace "Hawwa babu wani naki dabaisan relationship dinki da Ni'ima ba, yarinyar nan kawar amana ce, yanda kika daukeni haka tadaukeni, don't ruin friendship naku under no circumstances, you know maganan danake" gyadamata kai Hawwa tayi tace "nasani Ammi" saikuma ya tashi daga gadon ahankali zuwa akwatin nata tadauki dogon riga na bacci tasaka ta zare zanin wankan ta shanya ta dawo gadon tahau ta daura kanta kan cinyan Ammi tareda sauke ijiyan zuciya tabude watsapp tama Ni'ima chat "Just got to Ammi's place, Ni'ima why did you send Baban Yaseer? Why" tura chat din tayi taga yayi layi biyu alamun datan ta a kunne amman ba'a budeba jira tayi ta amsata but shiru ijiye wayan tayi ahankali tana lumshe ido kafin kaceme bacci yayi awon gaba da ita dan tagaji yau.
Yanda bacci ya shigeta yasa Ammi bata tadataba ta shiga dakin yammatan ta su biyu Amina da Ramla ta tadasu don salla itama tayi sannan tasa suka shiga kitchen cus taji Baban Yaseer yafice salla.

GARGADAN SOWhere stories live. Discover now