30

980 26 2
                                        

EPISODE 3️⃣0️⃣

Washegari around 5 ta farka da ciwon kai har bata iya bude idanu da kyau, gashi tai staining kayanta da wajen abinda bata tabayiba, ta tashi tacire kaya da zanin gadon batada karfin wanki a basket na laundry tasa, tasake kwanciya ko daga kafa tayi saitaji akanta, tana ahaka Baba yayi knocking da sallama da katuwan muryan nan nasa yace "zan shigo" kofan yabude ya shigo dakin yaganta kan gado hankalinshi yakara tashi ganin sosai Hawwa fa batada lpy, batama iya bude idanu, cikeda damuwa yace "Hawwa na" yazo wajen gadon yana dagota jikinta kaman fire Baba yace "subhanallahi, Hawwa zoki lallaba kiyi wanka muje asibiti, kokuma bari kiga nakira Ni'ima" wayansa yaciro daga aljihu yashiga kokarin kiran Ni'ima Hawwa na kallonshi da kyar harya katse bata dagaba yace "bata dagaba bari kinsan asuba ne hala bata tashi ba, bari nasake kira" yasake dialing number saiya cema Baba busy kusan sau 4 yana trying yace "busy busy yake gayamin" dan murmushi kadan Hawwa tayi ganin shima Baba tai blocking nashi, cikeda karfin hali muryanta baya fita da kyau tace "Baba karka damu bari naci abinci zan lallaba naje asibitin nasu adubani" gyadamata kai Baba yayi yajuya yace "shirya wankan bari nahada miki ruwa" sosonta yaduka yadauka yafita yana dungura sanda yashiga kitchen Umma na kitchen din ta banka uban tsaki ko kallonta baiyiba, ruwan da aka ijiyemai nashi na wanka yajuye mata yadauka yafito yatara na sanyi ruwan yayi dalam dalam dan jikinta akwai zafi sosai yakaimata bayi sannan yadawo dakin yabuga mata yace "fito Hawwa" fitowa tayi da hula akanta ahankali take tafiya tana dafe kanta da hannu daya hannu daya tana dafe bango, Baba yakama hannunta gwanin ban tausayi ya jinginata a bangon wajen yaci bari nakawo miki kujera, kujera ya dauko yasamata abayin sannan ya shigar da ita yarufo mata kofa, bata taba sani ana irin ciwon kan nan aduniya ba, kowani motsi tayi sai kan ya amsa, tadan jima tabude kofan Baba na jiranta, brush yabata daya koma daki yadauko mata tayi yariketa yakai daki ya zaunar kan gado, Allah sarki da kanshi yabude sip yazaro mata yar doguwan rigan da yagani na atampa green, ya ijiye mata kusada ita, tabishi da kallo yanda yake dingisawa yadauko mata mayyukanta yakawo gadon ya ijiye duka kusada ita murya chan kasa yace "sa kaya ganinan zuwa" yawuce yafita, da kyar ta tashi tadauko su pad, pant bra tashiga shiryawa ahankali tasaka green atampan da Baba yadauko, dogon riga very simple yet stylish dinki dan har collar gareshi rigan, ta zauna ahankali kome zatayi kaman kanta zai fadi, dan karamin gyalenta green ta dauka ta yafa tasake kwanciya agadon Baba yashigo da shayi a hannu yazo gadon yazauna kusada ita yace "zoki sha muje" hannu tadagamai alamun bazata iyasha ba, tana lumshe idanu saikuma dan gajeren bacci yayi gaba da ita wuraren 7 ta farka, jikinta har kyarma yake sabida zazzabi kaman ana tsinka hanjin cikin jikinta, idanunta sunyi jajir, gyalen tasake dauka tayafa dan bazata iya daurin dankwali ba ta lallaba ta mike tana daukan wayanta da handbag da car key a hannu tasaka flat shoe black tafito, Baba na compound tafito yamike dasauri yataho da sauri yana kallonta yace "kin tashi" dan murmushin karfin hali tamai tace "bari naje asibitin su adubani" Baba yace "zaki iya tuki kuwa da ciwon kan nan"? Murya cha kasa tace "zan iya Baba karka damu" har mota yarakata ganin hankalinshi bai kwanta ba da fitan ita kadai yasa ahankali tace "Baba ko Ni'ima zata iya dawo dani kazauna kaji" gyadamata kai yayi ya maida mata kofan yarufe ta tada motan taja Baba yabi motan da kallo.

Ahankali take tukin, da kyar take iya bude idanu har jiri jiri take gani amman sabida karfin hali haka tashiga hanya jikinta kaman wuta, ko kadan bata gudu sosai cus jiri take gani, har layi take, hospital nasu na yan sanda takeso taje tunda Ni'ima tace tadaina zuwa hospital nasu wanda shine hospital datake using idan batada lpy, sunkai wajen traffic light na zone 3 ta tsaya tana jiran yakai turn nasu tawuce, dan tsayawan kawai yasa taga idanunta sun fara ganin duhu, kawai idanunta suka fara kukkullewa suna firfir, internally taji kaman an kunna wani engine na vibration a jikinta, kawai jikinta yafara rawan da bata iya controlling tana fisfisgewa tafara convulsing.

Bakin rigiman Noor yasa yau yatashi da wuri cus tace shizai kaita school, tunda suka shiga motan nan surutu takemai, ganin an kirashi yafara waya yasa ta barshi tawuce window tamike tsaye tana kallon hanya ganin sun tsaya chak, motan dake next to them a layi yar corolla data tsufa ba irin tasu ba ta kalla, ihu tayi tace "Dady loook someone is sick, Dady someone is shaking, I think is Fairy Angel Anty, Daddy!" Yarinyar tai ihu dayasa Khaleel yadan dakatar da wayan dayake yazo wajen yace "Princess menene"? Leko da kanshi yayi shima idununshi suka sauka kan Hawwa dake convulsing acikin mota ita kadai kanta na karkacewa yawu nabin gefen bakinta, daidai tawani mike ta sandare ta danna tootle motanta yayi gaba yana arnen gudu jikake karakakakakap!!!! Motanta yana dukan motocin dake gabanta with full speed...
Dawani irin sauri Khaleel yabude bayan motan yafito yanabin motanta da gudun bala'i kaman bashiba acikin traffic din nan some people ma nafitowa dan some people anga Hawwa na convulsing, every gudu da Khaleel yake he's telling her in his mind don't die! Don't die! Saida motanta yahada 5good cars suna gudu saida sukakai jikin wani trailer ne akai gwarap!!! Dole motocin suka tsaya hakama nata ya tsaya but still pushing nata keyi sabida kafanta, glass na gaban motanta ya tarwatse kwasha kwasha kanta na jini hannayenta na jini, lafiyayyen accident Hawwa ta hada,  Khaleel yafara reaching wajen motanta yana zuwa wajen motan nata dake hayaki sosai yashiga budewa jama'a nataruwa ana tayashi budewa ana zuwa wajen sauran motocin yana kallonta yana kokarin bude motan yanda har airbag na motan yafito yatareta tagaba, bude motan yayi nasaran yi yashigo jini nabin hannuwanta da goshinta ga some kwalabe ajikinta, ya zare sitbelt dinta, Hawwa tafado jikinshi tana convulsing kumfa nafitowa ta gefen bakinta da yawu, jini nabin gefen goshinta, dasauri Khaleel yasa hannunshi yariketa, yakai hannunshi ya zare kafafunta daga tootle flat slippers nata nafita daga kafafun, lips nata na jini sabida yanda take biting nasu zata cigaba dasauri Khaleel yakai hannunshi yasa abakinta ta shiga tattaunewa tana datse hakoran akansu, daidai Salman da bodyguards nashi da mopol dinshi rikeda bindigoginsu sunzo akahau kallonsu jama'a while ana ciro sauran mutanen da Alhamdulillah babu wanda ya mutu saidai ciwo, rike Hawwa yayi gam ajikinshi yace "Salman pay for all damages she caused, I'm taking her to the hospital!".

GARGADAN SOWhere stories live. Discover now