Luβπα Sufyαπ*Rayuwa ba abakin komai take ba. Shekara biyu cikakkiya zai wuce in wuce. Magana bata taba hadamu ba. Naji wani iri, naso ko da sau daya mun taba gaisawa. Allah ya gafarta maka Dan ladi. Allah ya ya saukaka maka kwanan farko nayau a kabarinka. R.I.J DAN LADI*
Ta jima a zaune tana addu.o.i. bayan ta idar da sallar magrib.
Dan tana mikewa ana kira. Isha.i dan haka ta sauke nauyi.
Jingina kanta tai da gado. Tana sauke ajiyar zuciya. Batasan ta yanda zasu soma magana da natacce ba.
Basa magana da ganin juna kullum ma ya ta kare da bugun zuciyarta duk idan sun hadu.
Ita da take neman makasar auren nan.
Kwankwasawa taji anyi a hankali ta furta.
"Shigo"
Kaman ko da yaushe kamshin shi ya cika mata hanci. Wannan karin sai taji gajiya ta saukar mata.
Batai kokarin fada da yanayin da take ji ba. Kyale kamshin tai ya ratsa ko ina na jikinta.
Da sallamar sa ya karasa inda take. A kasalance husna ta amsa.
"Nas yace in fada maki saida safe. Ya gaji sosai ya kwanta"
Ya fadi idanuwansa na yawo a fuskarta.
Cikin sanyin murya tace.
"Allah ya kaimu lafiya"
Ya amsa da.
"Amin"
Yana dorawa da
"Thank you"
Jin tayi shiru ya sashi mikewa.
"Good night"
Ya fadi bai jira amsarta ba ya fice abin shi.
Wani numfashi husna ta sauke da batasan tana rike dashi ba.
Wani iri take ji. Wannan kirkin nashi yasata jin daban.
Wayar ammar ta katse mata tunanin da take.
Dagawa tai tace.
"Nawan barin zo. Wanka zan sai mu sha hira"
Ya amsa da.
"Karki dade"
Wanka tai ta rigar bacci marar nauyi. Ta dauki wayarta ta kira ammar.
Bai dauka ba ya kashe ya kirata.
Sunata hira yace.
"Tawan ina jin tsoro fa. Jikina yana bani zan iya rasaki har abada"
"Hmm nawan. Dan Allah ka daina karyamun zuciya haka. Believe in us mana"
Shiru yai na wani lokaci sannan yace.
"Bakomai"
Hira sukai tayi har bacci ya soma daukar husna. Hakan yasa suka hakura.
Tai addu.a.
Bacci ya dauke ta.
*
Prince ishaq harya kwanta yana mamakin karamcin da natacciya taima kanin shi.
Shi mutum ne da baya manta alkhairi ko ya yake. Sannan indai kai masa mutunci komin kankantarsa yakan ji dadi.
Yana son Nas sosai. Duk wanda ya nuna ma Nas kauna dole ne ya samu karammawa a wajen shi.
YOU ARE READING
WATA BAKWAI 7
SpiritualKaman yanda kaddara ta hada aurensu bayan ta rabata da wanda take so. Haka yake tunanin kaddara zata sa dole ya cika alkawarin daya dauka bayan cikar WATA BAKWAI. #Love triangle #HausaNovel