Babi na daya

4K 154 2
                                    

Ke!!! Kina ina ne ana ta kwala miki kira kina jin mutane? Ta dago kanta a tsorace ta dubi matar jikinta na kyarma tace mata "hajiya wankin da kika sani nake yi". Budar bakin hajiya tace mata; ke wace irin yarinya ce me tsinannen nauyi ne? Awar ki nawa kina wankin? Toh wallahi ki kara minti goma a wajen nan baki gama ba, ba ke ba abincin rana yau har sai kin gama min ayyukana. Cikin rawar jiki ta ansa ta da "to hajiya dan Allah kiyi hakuri". Hajiyan ta sa kai ta wuce ciki tana mita.

Wani irin silent kuka intisar ta saki me cin rai da ban tausayi. Wata irin kewar mahaifanta da familynta ne ke damunta. Kusan kullum a mafarkin su take..tana wanki kwakwalwar ta na tariyo mata rayuwarta tiryan tiryan.
                     ************

Intisar haifaffiyar garin kano ce. Gidansu na unguwar railway.yarinyace da ta taso cikin gata, iyayenta na kaunarsu ita da yan uwanta Mus'ab, da rayhaan, sai kuma ita wato auta intisar. Kasancewarta auta ya sa mahaifanta suke ji da ita sosai haka ma yayyenta, ba kamar Mus'ab da suke shiri sosai da ita. Ita kuwa rayhaan akan taba fadan sako-da-sako.
Makaranta mafi kyau da tsada mahaifinsu Alhaji Abdurrahman ya saka su. Mahaifiyarsu hajja fatima tana iyakar kokarinta akan tarbiyyar yaranta. Kuma Alhamdulillahi kwalliya ta biya kudin sabulu. Wannan gida akwai wanzuwar farin ciki a cikin sa.komai nasu abin sha'awa saboda yanda ake aiwatar da abubuwa cike da ilimi da wayewa.
Duk da kyau da kwarjini, aji da cikar kamala irinta hajja fatima, bata sakarwa masu aiki ragamar gidanta ba, ita ce take kulawa da cimar maigidanta da yaransu,har ya zamanto duk da kankantar shekarun su rayhaan ssi da ta basu tarbiyyar shiga kitchen da gyara muhallinsu, suturarsu, da su kansu.
Wannan shi ya sa kullum take kara cikawa maigidanta zuciyar shi,bugu da kari ga iya kwalliya da kissa, yayinda shi kuma ya zage yake musu abinda ya dace.

                     **********

Saukar rankwashin da ta ji ne yasa tayin firgigit ta dawo hayyacinta. Tayi maza ta dago daga sunkuyan da tayi. Hajiya ce a gabanta tana huci kamar bakin kumurci. A cikin zuciyarta kuwa, intisar addua take Allah ya fidda ita kawai, dan yau hajiya ba sauki a lamarin nata. Wani lokacin in tana yi mata mugun hali kamar basu taba hada dangantaka da ita ba.
Dan Ubanki har yanxu wankin kike yi ko? Toh wllh ki shiga hankalinki intisar, anai miki magana kin gwalalo idanuwa sai kace na mayu kina karewa mutane kallo, to kuruwa ta kur ki ci kanki ki sha bakin ruwa, ki yi ki gama yanxun nan ga Anas can ya dawo ko daki baki gyara mai ba, baki wanke mishi bandaki ba, ki wuce ki kai mishi abinci ki dawo ki karasa. Kuma wllh kar kiyi da sauri ki ga tanda zamuyi dake. Mutuniyar wofi.
Tsautsayi ne yasa intisaar cewa;  hajiya wallahi yunwa nak.... kauuu!!!ta hada kan intisaar da garu. Nan da nan tayi tsit, goshi ya tashi, abinka da farar fata har fuskar tayi ja. Bata kara 3 seconds ba da wurwuri ta nufi kitchen dan zubawa Anas abinci. Ta je kai mishi ya tusa ta da kalatattun idanuwan shi. Ta tsane shi kamar ranar mutuwar ta. Ta lura da yanda ya wani fiddo idanuwansa waje tare da ce mata wa yai miki haka muradina? Ba dai hajiya bace,? Wllh tsiyata da tsohuwan nan ta iya kwapsi, zo ki zauna a nan! Yai mata nuni da cinyar shi, zan lailaya miki goshin kar ya ki komawa ya bata min fuskata. Ita karin abinda yake bata haushi shi ne choice of words din shi, shi a lallai irin shegen nan a fagen soyayya, aikin banza! Wai muradina, ko me hakan yake nufi oho. Tsaki tayi kasa kasa amma ya jiyo ta.ya dube ta yace mata ah ah masoyiyata kar mu fara irin haka dake fa, sabida bana som rashin kunya da fitsara. Kafin ya mike tayi wuf ta gudu. Ta karasa bakin famfon farfajiyar gidan ta kalli himilin kayan kamar ta kurma ihu take ji. Ga yunwa na addabar cikinta, jikinta har rawa yake. Nan ta dukufa ta cigaba da aikin da ke gabanta hadi da tunanin butulci irin na mutum..Allah ya sa mu dace, ta furta a fili!

DUNIYA MAKARANTAWhere stories live. Discover now