babi na hudu

1.1K 57 4
                                    

Da ta fice da gudu ba inda ta nufa sai gidansu kawarta mai tausayinta, Aysha imam. A tsorace ta shige gidan har tana cin karo da wani abu. Tana dago kai sukai ido hudu da yayan Aysha, tai maza ta durkushe tana gaishe shi tana ba shi hakuri domin ta tsorata da irin kallon da yake jifanta da shi. Shi kuma a nashi bangaren tambayar kan shi yake wa ke bin yarinyar nan haka? Kamar ma ba a hankalinta take ba. Ganin irin yanda ta tsorata yasa shi dan murmusawa yace mata tashi ki shiga ciki. Tayi maza ta shige ciki da saurinta tana share guntun hawayenta.

A parlour suka ci karo da aysha tana shirin fitowa, da alama itama sauri take yi.mamakin ganin intee ne ya sata tsayawa turus. Daga bayan aysha intee taji ana cewa ba zakiyi sauri ki kira shi ba sai ya fice ko Aysha? Bana son shiririta fa. Da sauri aysha ta cewa intee shiga ciki kawata. Gani nan zuwa tayi waje tana gudu-gudu sauri-sauri. Intisar kuwa tayi tsuru kamar mage a ruwa. Kamar daga sama taji ana cewa wacece a nan ne? Cikin sassanyar muryarta tace ni ce umma. Intisar! Shigo ciki mana. Dama kina nan? Zo ki zauna kusa dani mana. A hankali na karasa kusa da kafafunta a kasa na zauna. Zauna a sama mana. Intee tace bakomai umma nan ma yayi. Ya mutan gidan naku? Da fatan dai komai lafiya.

Shiru nayi na kasa amsata. Jin nayi shiru ne yasa ta cewa intisaar! Me akai miki? Muna hada ido hawaye  dake makale a idanuna suka shiga bin fuskata. Dai dai lokacin Aysha ta shigo ta cewa umma. Kan na karasa ya ja mota. Ina ta daga mishi hannu bai ganni ba. Girgiza kai kawai umma tayi tace Allah ya shirya. Zama aysha tayi a gefen intee tace dama ana ganinki? Hawayen da ta gani a fuskar intee ne yasa jikinta yayi sanyi nan take.. intee me ya faru? Ke da hajiya ne? Ko baki da lafiya ne? Ki min magana intee zuciyata na min ba dadi ganinki a wannan halin. Umma ce tai karaf tace mata aysha ki dan saurara mata tambayoyin naki sunyi yawa. Ta maida duban ta ga intee tace mata diyata meke faruwa ne? Ki saki jikinki nima mamanki ce kin ji? Wadannan kalamai na umma ba karamun tasiri sukai a ranta ba. Nan da nan taji hankalinta ya kwanta da matar. Nan ta kwashe abinda ke faruwa ta gaya mata. Abinda yafi daure mata kai shi ne ina iyayen wannan yarinyar da take zaune da wannan azababbiyar matar? Ta kalli intee ta kara nazarinta sannan tace mata, ina iyayenki? Nan intee ta kuma barkewa da kuka.. ba wanda yace mata komai sai da tayi mai isarta. Sannan ta nisa tace umma mahaifiyata ta rasu, mahaifina kuma ban san inda yake ba. Yayyensa da kannensa suna kyashin irin son da mahaifansu ke masa, saboda duk cikinsu ba wanda yake da hankali, mutunci, da kuma sanin yakamata. Sanadiyyar batan shi muka shiga wani mummunan tashin hankali har yayi sanadin rashin mahaifiyarmu sakamakon ciwon zuciya d ta kamu da shi.da fari, sun nuna tausayawar su a garemu amma kuma daga baya sukai kunnen uwar shegu damu. Cin yau da kyar, na gobe ba tabbas. Alhali mun taso cikin arziki da gata da soyayyar iyaye.
Tana kaiwa nan ta sake saka wani kukan me ban tausayi. Umma da aysha ma abinkq da masu saurin kuka sai hawaye suke yi. Umma ce tai ta maza ta rarrashe su ganin ita ce babba. Tace ya isa haka! Aysha kuje ku co abinci kuyi sallah..in kun kammala sai ku dawo. Intee ki bar kukan haka kinji? Ta gyada kanta kawai alamar taji. Suka wuce dakin aysha domin gabatar da sallar isha. Umma ma ta mike ta shiga ciki...

💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢

Can kuwa a gidan hajiya, tana ta kwalawa intee kira amma shiru, nan tazo ta daga labulen dakin taga wayam. Ta duba bayi ma haka. Ta leka kofar gidan ma shiru. Tayi wata irin kakkaurar kwafa hadi da cewa zaki ci kaza kazanki. Wato kinyi kafafuwan fita kenan, ganin inai miki sanyi sanyi kwana 2. Tana cikin sambatu ne murjanatu ta shigo tace hajiyata lfy kuwa kike ta magana ke daya. Ta dago wani irin murmushi ya kwace mata alamar jun adin ganin murjanatu. Ah ah! Auta! Ina kika shiga ne tun jiya, inabkika kwana? Nayi kewarki(kuji fa! Uwa ce wai bata damu da inda 'yarta ta kwana ba, har fadi take wai tayi kewarta). Da muka dawo daga partyn dare yayi sai muka kwana a gidansu lubcy( lubabatu), cewar murja. Murmushi hajiya tayi tace da fatan partyn ya kayatar dai ko? Tace ba laifi manyan yara sunxo sosai anyi harkoki wllh hajiyata. Bani da kati a wayata bara na tura wannan sadaka yallan ta siyo min. Hajiya tayi caraf ta amshe tace ita fa na dawo daga nema fa. Ban ma san inda tayi ba, yau kuwa ni da ita ne. Zata dawo ne ta sameni. Murjanatu ta dubeta tace baza ta wuce gidansu kanjamammiyar yarinyar nan ba. Wace yarinya kenan? Hajiya ta tambaya. Wannan me shegen girman kan tsiyar mana Aisha. Sisto fa ta so yayanta yaki bada hadin kai.. Auta jeki ki kado min ita maza maza. Kai hajiya! Bar shi kawai. Ba zan iya zuwa ba wllh nemi yaro kawai a waje. Haba auta ti hakuri ki je min mana. Ta kike tana gunguni tana fizge fizge.

Ta kusa isa gidansu Aysha kenan wani mai mota kirar glk ya haskota. Kwailalliyar fuskar nan da karin gashi ya ja shi. Yana tai mata horn ita kuwa gogar an samu abinda ake so. Tsuntsu daga sama gasasshe.tana yauki ta juyo da kyar ta dube shi. Shi kuma alhajin sai washe baki yake anga farar mace.. Ranki ya dade ayi hakuri na dan dameki. Ta dube shi a yatsine tace masa ina jinka, yaya sunan malamar ne? Ta kalleshi wani iri tace mishi ni ba malama bace, sunana bby jaana.. nan dai ya tsare ta tas! Ko da yake dai dama abinda take so kenan, daga bisani kuma ta bashi number. Sukayi sallama ta karasa gidansu aysha. Gaban intee ne ya fadi suna hada idanu da ita. Umma ta dubeta tace baiwar Allah ko sallama sai kiyi ai, da kyar tayi musu sallamar.sannan ta dubi intee tace dallah malama hajiya na kiranki, ina zaman zamana ina hutawa kin sa a wani taso ni. Kuma ke da ita ne tunda ba ubanda kika tambaya izinin fita. Intee tayi tsuru dan ta rasa ta cewa. Take abincin da take ci ya fita a ranta.
Umma ce ta fara yiwa murja fada saboda dibar albarkan da take musu. Ke madam dakata nofa ba a min fada ba a nuna da yatsa saboda haka ki...taaasss!!! Wani arnen mari taji an sakar mata. Duk su ukun suka mike tsaye. Intee zawo me kadai bata saki a wando ba.. saboda yau ta dalilinta an mari 'yar gwal. Na shiga uku kawai take maimaitawa. Umma kuma ta dubi maabocin marin, yaya hameed ne. Yayan aysha ma dazu. Subhanallahi! Dan me yasa zaka mare ta, ya dubi jaana cikin ido yace mata ba a haifi wadda zata dagawa mahaifiyata murya ba, talkless of nuna ta hannu. Be very careful, you are very lucky i ddnt go further, kuma daga yau kada na kara ganinki xikin gidan nan. GET LOST!!! ta kalle shi tayi kwafa sannan tace mishi kayi da yar halak! Zaka sani ne. Fuuu ta fice. Umma tai mishi fada daidai gwargwado, sannan ta sa su raka intee gida. Ita dai intee ba baki, tunani take ko me zata tarar a gidan oho! Wannan kenan

DUNIYA MAKARANTAWhere stories live. Discover now