babi na shida

841 64 3
                                    

Alhaji buba shahararren maikudi ne na ajin karahe, irin su ake kira da money miss road, dan ko bangwayen aji guda hudu bai taba ahiga da sunan neman ilimi ba, na addini kuma akwai shi, amma kuma ba za a ce yana da zurfi ba. Yana da mata daya da yara goma, duk da dai yayi aure aure yafi sau nawa. Hajiya hajara, wadda ake kiranta fa hajo, tana matukar hakuri da hali na matsolanci irin na alhaji buba. Ba mai cin kudin shi sai kadangarun bariki, tun abin yana damunta tun aurensu na jariri har daga baya ta dangana. Mahaifinta ne ya bata jari kafin Allah yai masa rasuwa, da wannan kudin ne take ta juyawa Allah ya taimaketa ta tallafi 'ya'yanta tana musu hidimar makranta ta yau da kullum.
  Bai gama sheke ayar sa ba sai da sare ya tsala sosai sannan ya baro kyau a hotel din. Da kyar ta iya kyale shi ya tafi akan alkawarin washegari zai dawo. Haka alhaji buba ya dawo gida a makare, ya tarar da matar sa kan sallaya tana addua. Kallonta yayi yace hajo kenan. Ta dube shi a ladabce tace mishi sannu da zuwa. Kamar ba zai ansa ba sai daga baya yace yawwa. A miko maka tuwon ne malan? Kallonta yayi a wulakance yace wannan tuwon ai sai ku. Bata sake ce mishi komai ba ta samu guri ta kwanta, dama tana shirin kwanciya ne ya shigo.
  Yana fitowa daga wanka ya raahe a gado, ita kuma ta rakube a gefe. Jin fitowarshi ya sa ta mikewa ta zauna don tana son yi mishi magana. Malam! Ya juyo a gadarance yace mata meye ne, nan ta daburce ta rasa ta cewa ta fara in ina. Dama dam..dama cewa zanyi ko zaka dan taimaka mana da wani abu, wallahi kayan abincinmu yayi kasa. Kallonta yayi a wulakance yace bani da shi.. idanunta sukayi rau rau kamar zatai kuka tace haba malan, ka san bana tambayarka abu in dai ba ta kure mana ba, ka dubi Allah ka taimaka man... malama ji nan, ya katse ta, kin taba gani ina cin jagwalgwalonku? Ni ba ruwana wannan ke ta shafa. Ran ta ya baci saboda ta gaji da abinda alhaji buba ke mata. Mutum bai san darajar ta ba a matsayinta na matar shi, bya sauke mata hakkokinta, zaluncin yau daban na gobe daban.. wannan wace irin rayuwa ce?
  A take taji zuciyarta ta dake, ta dube shi tace mishi, alhaji buba! In baka yi min ba ni ba matsala bace, amma ka tuna kana 'ya'ya, suma suna da hakki a wajenka. Mamaki ne ya lullube shi, wai shi yau hajo ke mayarwa da magana, kafin yace uffan ta nemi inda dare yai mata sboda bacin rai.

         *******
Da asubar fari hajiya almasifatu aka fito tashin baiwar Allah intee. Da kyar ta iya tashi saboda tsamin da jikinta yayi. Ta samu tayi alwala tayi sallah, tana cikin addu'ointa ne bacci ya kwasheta. Intee akwai hankali, duk da karancin shekarunta, duka duka bata fi sha hudu zuwa biyar ba, amma tasan addininta daidai gwargwado. Su murja kiwa ko oho, sai ta hantse a gado sannan take tashi in ta ga dama tayi sallah, in kuma bata ga dama ba, toh ta sha ruwa kenan.
    Gari ya waye shiru intisar bata fito ba. Hajiya na fitowa dama da ragowar ruwa a hannunta wanda ta sha. Shibta watsa mata tana dura mata uwar ashariya. Ni baiwarki ce da zan miki aiki? Cikin murya cike da rauni tace hajiya ban da lafiya. To ubanki zan miki, kalleta kamar ragowar yunwa. Kar ki fito ki ga yanda zanyi dake. Haka ta kuma zubewa a kasa tana kuka kasa kasa. Kamar an ce ta waigo taga aysha ta shigo dakinta da sanda, abu ta miko mun a leda ta juya da sauri ta fita, ina dubawa naga chips plantain da kuma peppered chicken. Bata yi wata wata ba ta fara bawa ciki hakkinsa. Tana ci tana tuna rayuwarsu da iyayenta da yan uwanta. Oh mamana kin mutu kun barni a wahala, babana da 'yar uwata ina kuke a fadin duniyar nan? Oh ni intisar! Allah ka zame mini gata. Tana tunani tana hawaye. Ji tayi kamar motsi akan ta, da sauri zata boye abinda ta ke ci amma ina! Ta makaro. Murja ta riga ta ganta. Wani murmushin mugunta kawai tayi tace hajiya! Da sauri ta karaso, tace mata zo ki ga munafukar nan. Intisar kirjinta kidan kalangu kawai ake yi, ta tsananin tsorata. Yanzu kuma me zai biyo baya?

*** assalamu alaikum my people.ya kuke? Hope kunyi sallah lfy.. Allah ya maimaita mana, ameen. Pls keep on voting and commenting.i love you so much😍😚😙

DUNIYA MAKARANTAWhere stories live. Discover now