Babi na biyu

1.4K 74 0
                                    

Ko da Anas ya kammala cin abincin bai nufi ko ina ba sai wajen mahaifiyarshi. Banka kofar yayi ba tare da sallama ba. Ya dubeta yace hajiya wallahi yarinysn nan tana shige min hanci Al-Qur'an zan fyato ta, kema kin fini sanin rashin mutunci na fa. Yasin ba mutunci ne da ni ba fa.

Nan da nan hankalin hajiya ya dagule tana rawar murya tace mishi wai meke faruwa ne? Wa ya tabo min kai ne haka? Ya kalleta yace wannan yarinyar, ya hado wasu ashar masu kauri ya watsa mata, yasin fita daga idona. In ba haka ba zan sassamata. Dan kawai taci sa'a ina eh yane dinta ne. Wllh da ta gane kurenta tuntuni.
Hajiya ta soma bashi hakuri tana lallaba shi  ba tare da taji ainihin abinda ya hada su ba. Tana nunawa yaranta ao da kauna na fiye da kima, shi yasa daga mazan har matan sun gagareta basu ganin kimarta ko yaya. Amma hakan bai sa ta fasa basu gurbataccen so ba.

Yaranta uku a duniya, Anas shi ne babba, sai saratu sannan sai murjanatu. Dukkansu ba wanda zaka dauka a ciki da zaka ce yana da tarbiyya ta gari. Haka nan suke watsewarsu ba abinda yai musu zafi. Tun sunayi a boye har mutanen unguwa suka fahimta aka fara gaya mata. Sai ta shafawa idonta toka ta dinga zazzaga rashin mutunci tana cewa anayi wa 'ya'yanta bakin ciki saboda auna cigaba. Da aka ga haka sai kowa ya fota hanyarsu.aka hana sauran yaran unguwa hulda da su.

Amma ba wanda hajiya(ainihin sunanta talatu) ta raina take wa kallon 'yar bariki kamar 'yar tahalika intisar da 'yar uwarta rayhaan.
Bin malamai da bokaye kamar shan ruwa ne a wajen hajiya talatu,a haka ta shanye mijinta marigayi ya zama mijin-hajiya. Ba shi da katabus a gidan shi, ta hana shi zumunci da yan uwa.
Mutum daya take gani da mutunci, ba dan komai ba kuwa sai dan suna da arziki. Hajja fatima tana zaune da ita tsakani da Allah. Amma ita a wajenta ba haka bane har ra kai ga mummunar kaddara ta fada musu rikon su rayhaan ya dawo hannunta.

Wannan shi ne silar shigar su rayhaan mugun yanayi.

******
Fitar anas daga wajen haj.talatu ke da wuya ya iske ta a tsakar gida tana wanke wajen da tai wanki, bata ankara ba kawai sai ji tayi anyi tapping mazaunanta..juyowa tayi a fusace tare da cewa wannan wane irin iskanci ne? Ni wallahi ba 'yar iska bace..aikin banza kawai, ta murguda baki hade da juya idanunta..galala anas ya tsaya kallonta kamar yau ya taba ganinta. A zuciyar shi kiwa cewa yakeyi da sannu zan koya wa yarinyar nan hankali, naga ta fara iya rashin kunya. A zahiri kuwa cewa yayi, kin ga kuwa ni dan iska ne kuma ina son iskancin. Dan haka ki shirya, yanxu kika fara ganin iskancin..ba karamin tsorata tayi da kalaman sgi ba, domin ta san sarai waye anas, ta san shi kamar yunwar cikinta.. Allah gani gareka ni 'ya su. Allah ka fidda ni, ta fada a zuciyarta tana share guntuwar kwalla a idanunta.

DUNIYA MAKARANTAWhere stories live. Discover now