Chapter 19-20

181 11 0
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
  💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of reader's._*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad._

19 - 20

     Da daddare Daddy ne ya k'ira Mahmoud ya zo ya zauna kusa dashi tare da cewa "gani Daddy", sai da yagama chewing abincin da ke bakin sa sannan ya juyar da fuskar sa side dinsa yafara magana.

   "ina fatan dai kunyi magana da manager'n company'n naku yace next week saka shiga Office koh?" "Eh Daddy mun gama komai".

   "yauwa naji dad'in hakan kuma Mahmoud idan kaje ka can kaga babu idon Uwa babu na Uba sannan babu wanda kasani a can dan haka ka maida hankalin ka kayi abun da ya kai ka kar kayi shegen takar da kasa ba dan babu mai taimakon ka dan Lagos zaka kowa takai yake, sannan banda abokan banza da girman ka yanzu ka kai shekara 28 amma sai an maka magana akan wannan kaga bai da amfani dan haka ka kula da kanka, kaji?"

   "Eh Daddy", "kuma ina so ka tattara tunanin aure yanzu ka ajiye agefe dan shi aure lokaci ne Allah dai yayi wancan ba rabon ka bace amma duk sanda kasamu wata kamun magana". Yana wani kumbure kumbure yace " toh Daddy ". Sannan Daddy yace "shikenan zaka iya tafiya" nan ya mike ya bar parlour'n.

    Bayan kwana biyu da yamma Airah na wasa akan keke'n ta a harabar gidan Engr. Ahmad ya shigo. Sauka tayi ta nufi wajen sa da gudu tana "Daddy 2 Oyoyo".

     Murmishi yake mata ya d'an doka ya rungume ta yace " Oyoyo 'yata, wasa kike ne?" "Eh" ta basa ansa ataikaice. Ya kama hannun ta suna tafiya cikin gidan ya tambaye ta "Daddy'n ki na nan kuwa?" "A'a baya nan sai Mummy".

   Suka karasa cikin parlour'n da sallaman sa amma shiru babu kowa Mummy na kitchen. Airah tace "bari na k'ira maka Mummy" ta wuce shi kuma ya zauna kan sofa.

    Airah na fad'a wa Mummy ta wanke hannun ta a sink ta fito da murmishi d'auke a fuskar ta. "Sannu da zuwa Engr. Ina wunin mu?" "A'a Hajiya Asma'u lafia ya gida?" "Alhamdulillah, ya Mufeedah da Hajiya Kaltum duk da dai mun gaisa kwana ki". " lafian su kalau ita Mufeedah'r ma zata zo next week ", da murna tace " haba naji dad'i amma Allah ya kawo ta lafia iyee bari Jannat ta dawo taji wannan labarin dan tabi ta ishe ni da yaushe Mufeedah zata dawo", "Ayya toh sai ki sanar da ita kam inaga ma suna waya ai ko chatting ne ma dan ita Mufeedah'r tana fada mun", "eh haka ne kam".

    Engr. Ya mike zai tafi Mummy tace " a'a tafiya da wuri haka?" "Eh wlhy kinga mutumin nawa ma baya nan sai kigaishe sa", " Toh insha Allah zaiji, Allah ya kiyaye hanya".

     Al amarin Salma kuwa kullum sai ta k'ira Mahmoud awaya tun yana rejecting har yasaka ta a black list. Ko da Mummy ta sake mar magana akai cewa yayi shi kar a damesa dan baya santa. Saida yayi wa Mummy'n nasa fushi sannan ta daina mar maganar Salma.

     Akwana a tashi har gobe ne d'aurin auren Siyamah. Ita da kawayen ta sai shirye shiryen dinner da zasu yi da daddare suke. Salma ta saki ranta dan ta fahimci zab'in da mahaifin ta ya mata shine mafi alkhairi dan Allah ba zai zab'a mata wanda bai dace da ita ba shiya sa ta hak'ura dan babu yadda zatayi da soyayyar Mahmoud.

    Washe gari aka d'aura auren ta da Saleh. Tana zaune kan carpet tana breakfast wata k'awar ta tashigo da gud'a tace "Siyamah Amarya a yanzu fa kin kasance matar Saleh". Murmishi Siyamah tayi ta d'aga kanta tana kallon hoton Mamar ta dake jikin bango aran ta tace _Allah ya ji kanki Mama da kina nan nasan Abba bazai raba ni da Mahmoud ba_ ta goge hawayen da suka sauko mata a lokacin ta ci gaba da cin abincin ta.

    Tunda Mahmoud yaga time d'in d'aurin auren ya wuce hankalin sa ya tashi dan yasan daga yanzu Siyamah matar wani ce. kulle kansa yayi a d'aki ya kwanta a kan gado sai zubar da hawaye ya ke yana tuna moment inda suka yi sharing tare.

    Zazzab'i ne yaji ya fara kamashi yaja blanket ya rufu dan wani sanyi yake ji ga tunanin Salma ya mamaye shi kuma bacci yake son yi amma bazai iya ba.

    Badan yaji bayi da karfin jiki ba da ya tashi ya je Bar ya sama wa kansa sauki amma bazai iya ba. Tuno wasu drugs da Nasir ya basa kwana ki yayi ya lallab'a ya je wajen drawer'n da ya ajiye ya d'auko ya wasa gaba d'aya abakinsa ya tura da ruwa sannan ya kwanta. Ahaka baccin ya sace sa babu b'ata lokaci.

    Around azahar ya farka ya tashi yashige bayi yayi wanka ya fito yayi shirin sa cikin Kaftan fari tas. Ya masa kyau sosai ya amshi jikin sa yaje gabar mirror ya taje sumar kansa ya gyara side box d'in sa mai kyau dashi.

    Mahmoud kyakkyawa ne duk mace da tagan sa sai ta kwad'ai tu da sonsa kuma abunda yafi tafiya da imani wajen mata idan suka gansa shine yadda side box inda suka amshi fuskar sa kawai dai wannan shan giyar tasa ne ya b'ata sa.

   Murmishi yayi ganin kyau da yayi ta mirror yace "kamata yayi yau nine mijin ki Salma". Hawaye suka taru mishi a ido. Zuwa yayi ya bud'e wata drawer ya fitar da wata farar envelop na hoto.
 
    Zama yayi kan gado ya ciro su, hotunan shi da Salma ne wanda sukayi kafin yaje US. Wrapping yayi ya saka a aljihun sa ya fita zuwa d'akin su Jannat ya tarar da ita tana kwalliya a gaban mirror.

    Cewa yayi kiyi sauri ki same ni a motar zamu fita. Da mamaki ta juya tace "Yaya ina zamu?" "Rakani zakiyi wani waje ina jiran ki kuma bana son wani tambayar", ya juya ya fita.
   
     Tab'e baki tayi a hankali tace " ni fa ina da wajen zuwa in ba son b'ata wa mutun rai ba", ta ja gyelen ta akan gado ta d'au ka jakar ta ta fita.



Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now