Chapter 61-62

146 10 0
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
  💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of the reader's_*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad_

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
http://maryamsbello.blogspot.com

Dedicated to: *Zara Adamu*

61 - 62

        Mahmoud bai tsaya ko ina da ita ba sai k'ofar toilet inda ya Mufeedah ta bukaci towel ya d'auko mata da wardrobe. Kok'arin tashi wa take yi duk da ba mik'e war zata iya ba kawai karambani ne nan ta zame zata fad'i Mahmoud yayi saurin taro ta da damuwa a fuskar sa yace "haba Mufeedah kin fasan ba iyawa zakiyi ba kawai kibari mushiga na miki", wani d'an banzan kallo ta bisa dashi sannan tace " ai babu ruwan ka kadai karasa ni ciki amma zan iya wankan". Babu musu ya shigar da ita ya zaunar da ita kan toilet seater nan ya juya ya fita.

      Da yake komai a hankali take yi sai bayan kamar min tuna talatin ta kammala wankar ta kuma wanke bakin ta nan tashiga kwala wa Mahmoud k'ira yazo ya fitar da ita. Mahmoud ko bayan ya bar ta daga toilet d'in waje yayi ya karb'o musu abinci sannan yazo ya zauna jiran fitan ta.

     Yana jin k'iran sunan sa ya mik'e ya shiga toilet d'in tana kallon sa tace "ina wheels ina"?  Ko sauraran ta bayyi ba ya je kusa da ita ya d'aga ta cak daga ita sai towel, shure shure tashiga yi tana " ka sauke ni bana so, je ka kawo mun wheelchair na" tana kai masa duka amma yaki kula ta bai sauke ta ba sai kan gado da ya duro ta. Harara ta nisa dashi shiko ya zauna gefen ta yana mai da numfashin munafirci yace "kai duk sirantakan nan amma uban nauyi haka sai kace buhun masara gaskiya kina da nauyi", ya juya yana jiran ya ji me zata ce sai yaga shi take kallo, suna had'a ido ya fake da wani sallon yace " washh Allah na wani irin tuwo kike ci haka, hala tuwon dawa ko"?

   Tsaki ta ja masa tare da juya kan ta d'ayan gefen tace "kai kasani ai idan shi nake ci kai kuma kaine mai iya noman masaran tunda har ka iya d'aukan ta". Dariya ne ta sub'uce masa yace " amma fa gaskiya ne, lallai kinyi dace tunda mijin ki manomi ne".

      Tab'e baki tayi tace "ni tashi ka d'auko mun rigar da zan sata kuma ka d'auko mun body lotion na shafa. " Ok yes Ma" yace ya mik'e ya d'auko jakar kayan ta ya bude, d'aya bayan d'aya yake cire kayayyakin duk ya hargisa wajen sai faman surutun ya gyara mata kata take baya kula ta. Doguwar rigar barci ya ciro sai kuma ya ga wata y'ar k'arama armless daidai guiwa very light dashi murmushi yayi ya d'ago sa yace "wannan zaki saka zaki fi shan iska cikin ta", kallon banza ta wasa masa ta had'a rai tace " bana son wannan wasan ka d'auko mun wanda ka mayar yanzu".

      Murmushi yayi yace "as you wish your highness" nan ya tashi ya mik'a mata tasaka shi a kwancen. Lotion d'in ta fara shafa wa shima ya d'an lakato yace sai ya shafa mata nan ta soma yi masa fad'a, kin fasawa yayi yace "haba dai kin ma isa ke da kanki kika ce ni zan miki duk hid'imar da kike so kuma wannan ko baki fad'a ba ai nasan aiki na ne dan haka sai na shafa miki" ya matso kusa da ita ya kamo kafar ta ya soma shafa wa.

       So gently yake yi yana mata shi romantically tana kallon sa cike da haushi amma sai taji dad'in sa, tama rasa wani matakin zata d'auka ta tsaya tunani da kuma jin dad'in yadda yake matsa hannun sa a lallausar kafan ta, ji tayi ya soma kai hannun sa wajen cinyar ta yana sama dashi, atake ta tattara duk karfin ta ta fusgi kafar ta kai masa blow dashi, wani azababban k'ara ne ta sakar sakamakon jin zafi da tayi a kashin bayan nata kuka ta fashe dashi.

     Mahmoud da yayi dodging dukan a rikice yayi ta kanta ya riko hannun ta yana "sannu me yasa mukayi hakan?" Warce hannun ta tayi taci gaba da kukan, Mahmoud ya dad'a matso wa ya kamota ta yace "calm down Mufeedah its the matter of your health no any intimacy in it" nan ya d'ago kanta ya jinginar da ita a jikin sa yana shafa gadon bayan ta a hankali har ta samu nutsuwa nan ta zame jikin ta a nasa ta koma ta kwanta.

      Mahmoud ya tashi ya d'au ko abincin ta ya a ajiye a kan side drawer yace "abinci zaki ci bari na jinginar dake jikin gadon bata musa ba nan ya shiga d'aga ta daga kwanciyar da take ya jinginar da ita. Plate din ya d'auko ya sa cokali ya d'ebo fried rice zai kai bakin ta ta sa hannu ta karb'i spoon d'in tace " zan iya cin abuna", murmushi yayi yace "OK kici ga ruwa sai ki had'a da maganin ki kisha sai ki kwanta kinsan gobe da safe zamu tafi asibitin", Mufeedah ta nisa bayan had'iyan abincin da ke bakin ta tace " kaman ta banyi sallah ba ko" nan yace "oh sorry wallahi na manta but kin yi alwala ai ko" gyad'a masa kai tayi takai wani loma bakin ta. Yace "toh ki gama kiyi sallan sai ki kwanta".

     Tashi yayi ya shiga toilet shima yayi wankar ya d'auro alwala ya fito kafin nan har ta gama cin abincin ta sha magungunan ta.

   Jallabiya ya d'auko cikin kayan sa ya saka ya saukar da ita kan sallaya ya d'auko mata hijabin ta tasaka ya wuce gaba ya tada sallah ita ko a zaune take dan tana d'an iya zama na wasu lokuta sai kuma ta gaji ta kwanta ahakan take sallar.

  Bayan sun idar tagama adduo'in ta ya kaita kan gado ya kwantar da ita.

   Wajen k'aramin table da abincin sa ke kai yaje ya zauna ya ci ya gama ya sha ruwa ya wanke bakin sa ya kashe wutar d'akin ya kwanta kan gadon.

   Mufeedah ce ta fara musu musu Mahmoud yace " me ya faru kuma"? Cikin zazzakar muryan ta na cike da shagob'a tace "ni ka tashi kabar mun gadon in yaso ka kwanta a kan couch", "what's your problem there in na kwana anan d'in", kuka ta ajiye masa yace " hey its not a big deal zan tashi kar ki cika mun kunne amma kinsan its your own benefit in na kwanta kusa dake idan kina bukatar abu I might be a help but idan na tashi kar ki kuskura kice kina nema na".

    Ahankali tace "eh naji nidai ka tashi kuma in na neme ka kar kazo d'in za mu gani ai", dariya yayi ya sauk'o tare da cewa "mutum sai shegen gadara gani mara zuciya ko", "eh mana sosai ma kuwa" tace ta kuma karawa da "oho ka dai tashi ai".

    Kunna wutar d'akin yayi ya kalle ta, ihu ta sakar masa tace "ni ka kashe please barci zanyi fa", ko kula ta baiyi ba yana kallon yadda take masifar sai burge ta yake hawa kan gadon ya kuma yi ya matso dab da ita " wai meye haka ne" cewar Mufeedah tana kok'arin ja da baya shi kuma yana matso wa bakin sa yakai kan goshin ta zaiyi pecking d'in ta wayar sa dake kan drawer ya shiga ringing "oh this lovely moment was to be distracted" yayi stating nan ya mik'e ita kuma tace "mayen mutum kawai ai na gode wa mai k'iran nan kuwa".

   Mahmoud na d'aga wayar yaga Daddy ne nan yayi receiving da wuri suka gaisa Mahmoud ke fad'a masa yayi magana da likitan akan yace suje gobe, ya bawa Mufeedah ma suka gaisa Mummy ma ta karb'i wayar suka gaisa gaba d'aya sannan sukayi sallama. Mahmoud na dropping wayar ya sauka daga gadon ya kashe wutar d'akin yaje kan kujerar yayi kwanciyar sa bai bi ta kan Mufeedah ba.




Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now