Chapter 51-52

159 10 1
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad_

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

51 - 52

Washe gari Mufeedah ce ta tashi da sassafe ta shirya musu breakfast ta zauna ta ci nata saboda da wunya da ta tashi dashi. Wanka tayi ta saka lace mai kyau wacce aka yiwa aikin stone tasha kwalliyar ta tazo ta mik'e kan sofa a parlour ta shiga chatting a WhatsApp.

Jannat tagani online nan suka fara hira cikin jiran tasu Jannat take ce mata "Amarya kina cin amarcin ki har kin manta damu ko?" Tab'e baki Mufeedah tayi as if tana kallon ta ta mata reply da "banga abun amarci da zanci a gidan nan ba", Jannat tayi replying da " haba matar yaya nasan yanzu dai kin fita daga sahun mu na 'yan mata", share ta Mufeedah tayi bata mata reply ba har ta sake turo mata "mudai a k'ula mana da yayan mu mai kyau kinsan bai da lafia". Sauka ma daga online d'in tayi dan hiran Mahmoud is annoying a wajen ta.

Bayan wasu minutes kuma ta k'ara hawa dan ta tuno reply da zata mata tayi mata voice note tace "kin isheni da yayan ki kin fa san banyi aiki a asibitin mahaukata ba balle na iya curing d'insa dan haka babu wahalan da zanyi akan sa, mtsw", ta tura mata.

Mahmoud ne ya bud'e k'ofa ya fito, kallo d'aya yayi mata ya kau da kansa ita kuwa ko d'aga ido bata yi ba ballan tana ta gansa. Zuwa yayi zai wuce ta bayan ta yace wasa mata harara kaman tana ganin sa sannan ya wurga mata tambayar " ina kika kwana jiya?" Shiru tayi ta share sa bata ansa sa ba har ya k'arasa dinning table ya zauna.

Juya wa yayi ya kalle ta yaga alamar ba zata ansa shi ba ya k'yale ta ya zuba abincin sa ya fara ci. Tea yake son sha kuma baiga flask d'in ba, duba ko ina yayi a area'n amma bai gani ba hakan ya sa ya juya ya tambaye ta "ina kika kai flask na tea ne so nake nasha", da halin ina ruwa na tace " ban dafa ba", "What baki dafa ba bayan kinsan zan bukata oya tashi ki dafa mun".

Tab'e baki tayi tace "tabd'i ni bazan iya ba", da mamaki ya tsaya kallon ta yace "ke! Kina da hankali kuwa?" "Rass ma kai", ta matar masa kai tsaye, gaba d'aya sai ya rasa me zai gaya mata dan taba sa mamaki sosai, zuwa yayi ya zauna a kujeran da ke facing nata ya numfasa sannan yace " Mufeedah ", shiru bata ansa sa ba.

K'iran sunan nata ya sake yi bata k'ula sa ba, ransa ya b'aci sosai amma ya daidai ta yanayin sa yace da ita "Mufeedah ke ba mata ta nace? Ko kin manta dalilin auren ki dani, ba dan ki warkar dani ki sama mun lafia ba? Kinga kuwa dole kiyi d'awainiya ta zuwa ga ciyar dani, kula dani, girma ma ni a matsayin mijin ki da kuma gamsar dani ta bukatar aurataiya".

Sai yanzu ta d'ago da kai ta kalle sa tunda ya fito daga d'aki, kare masa kallo tayi sannan ta mik'e ta zauna tace dashi " lallai kuwa ba kayi sa'ar likitan nan da kasa aka aura maka ba, wai shin ina hankalin ka yaje ne da kaman ta akwai wacce ta d'au nauyin yi maka wannan bautar amma ka yaudare ta, toh gashi ita Allah ya so ta ta samu mijin da ya fiye mata kai amma kai fa kana nan zaka kwasa da ita dan she won't tolerate this nonsense", mik'e wa tayi tayi hanyar d'akin ta.

Tunda ta fara maganar a nuste yake kallon ta har ta gama tayi gaba, hawaye ne suka taru mar a ido aransa kuma yace _nasani, nasani Mufeedah nasan abunda nake, tunda nayi losing Siyamah ban tab'a tunanin zan samu wata macen da zuciya ta zai kwanta da ita ba sai ke, kuma ita Mahsin da kike fad'a bansan ya akayi na ce a aura min ita ba but wallahi ba wai son ta nake ba kawai ita tafi burge ni akan y'ar uwar ta Amina ne but my first sight on you nasan zaki maye min gurbin Siyamah har ma ki fita._ K'arar wayar sa da yaji ya fara ringing ne ya dawo dashi daga tunanin da yake ya d'auko wayar yayi receiving.

Mufeedah na shiga d'aki wayar ta yayi ringing Mummy ne ta k'ira ta da farin cikin ganin call d'in tayi receiving suka gaisa nan Mummy tace mata Airah zata zo mata weekend anjima, dad'i taji sosai tayi murna.

Da yamma bayan Airah ta dawo Musty yace duk su shirya zasu je yawo, hakan kuwa akayi sai kusan magariba suka dawo gida, Mahmoud na tsaye a parlour yana kallon su through window suka fito daga mota, dariya suke da shewa Musty yace "oh Mufeedah kin manta ledan shopping d'in ki a motor", ya d'auko ya mik'a mata garin hakan hannun su ya goga na juna duk a idon Mahmoud basu gan shi ba, su kuwa basu ma kula da goguwan hannun su da yayi ba.

Ganin loads da Mahsin ta rik'e sun mata yawa Musty ya k'arasa yace "oh sweety na bari na taya ki", ya karb'i sauran ledojin hannun ta suka ci gaba da tafiya Mufeedah tayi missing step kayan hannun ta ya fad'i zata zame k'asa Mahmoud dake kallon su ta window ya tsora ta har da mik'a hannu kamar zai kamo ta, Musty ne yayi saurin taro ta daga fad'uwan da za tayi, hannu yasa a kugun ta ya tare ta, Mahmoud kuwa a ransa yaji wannan kayan bakin cikin, Musty ya mik'a wa Airah ledan hannun Mufeedah suka daka su har k'ofar parlour'n ta ya kama hannun Mahsin suka wuce nasu.



Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now