Page 2

68 4 0
                                    

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸

*ALHAKI NEH!*

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋

® *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

By the applomb writer: *Hamagee*

Wattpad @Hama_gee

10th Sept,2017

Page 02

°
"Ina fa lafiya,wai ni don Allah Umma yaushe zaki daina takura ma Zuwaira neh? Me tayi miki haka neh?",Umma ta dubi Mahdi tace

"Me nayi mata?ita tace maka nayi wani abun ko kuwa?",Mahdi bbu koh kunya ya dubeta yace

"Ba kiyi mata komai d'in bane?,nifa gaskiya bana son irin abunda kike mata",Umma dai bata ce komai ba dan ganin yanayinshi,tasan tabbas inta matsa zai zageta shiyasa ta jaa bakinta tayi shiru.

Ganin hakan yasa Mahdi barin d'akin yana banbami.

Zuwaira kuwa ji takeyi kaman an tsundumata a aljanna tsananin murna,fitowar Mahdi yasa ta daina rawa da tsallen da takeyi.Ta wani marairaice kafin tace

"Yi hak'uri megida,karka sa damuwa a ranka da Allah".Ta ja shi suka shiga d'aki tana kanainaye shi da zantuka masu sanyaya zuciya.

****
Umma kuwa kwanciyarta tayi dan ta rigada ta saba da irin wannan yanzu,gashi k'aninta yayi yayi da ita ta koma gidanshi da zama amma firr ta k'i,k'aninta me suna Kawu Bello.

Shi kad'ai ya rage mata a rayuwannan,babu iyaye babu yayye kuma babu wasu k'annen,sai d'a d'aya tilo.Hakan yasa bata k'aunar rabuwa dashi koh kad'an dukda irin wulak'anci da tsangwamar da take fuskanta a gidanshi.

Babban abun takaicin ma wai harda shi d'annata ake ci mata mutunci,da iya matarshi ceh me yi mata hakan da da sauk'i amma dukansu.Ita kam taga rayuwa,kuma da ba haka yake ba.

Kuma babu alamun asiri a tattare dashi,kawai irin sonda yake ma Zuwaira neh yasa shi yake yin komai.Amma koma miye ita dai tana mishi addu'ar shiryuwa tareda matarshi.

Sallamar Kawu Bello ta jiyo dan hakan ta tsaya tsak da tunaninda takeyi tareda k'ak'alo fara'a a fuskarta.Yana shigowa kai tsaye d'akinta ya nufa dan daman wajenta yake zuwa tunda su Mahdi kam saidai suje gaidashi.

"Assalamu alaikum",ya fad'a a daff k'ofar shiga d'akinta.Ta amsa mishi da "wa'alaikum salam,Bello neh yau a gidannan,shigo mana".

"Nine yaya",ya fad'a tareda shiga d'akin.Neman guri yayi ya zauna,itama ta tashi ta zauna kafinnan suka shiga gaisawa.

Sun gama gaisawa kenan saiga Mahdi da Zuwaira sunzo gaidashi suma,har k'asa Zuwaira ta tsuguna tana gaidashi baki a yashe kamar da gaske,Umma dai girgiza kai kawai tayi ganin irin tadda Zuwaira ta k'ware a munafurci.

Bayan sun gaidashi sai Zuwaira ta tashi ta tafi d'akinta,Mahdi kuma zama yayi suka d'anyi wasu maganganu kafin ya tashi shima ya bita,bayan fitarsu neh yake tambayar Umma koda wata matsala,tace mishi babu.Daga bisani yayi mata sallama ya tashi ya tafi.

Bayan ya fito neh ya had'u dasu a waje sukayi sallama kafin ya wuce.

****
Bayan sati uku,
Kamar wasa Kawu Bello yake cewa bari yaje ya dubo yayarshi danya jima baije gunta ba,kamar zaije kamar kuma ya bari sai gobe dan akawai wajenda yake son zuwa yau d'in.

Kamar wasa dai saiya kama hanyar shi ta zuwa gidan,abunda ya tarar a gidan ba k'aramin b'ata mishi rai yayi ba.Wai Aminu ne yaje d'akin Umman yana wasa,itama wasan take mishi dan a rayuwarta inda abunda tafi k'aunarsu sune Mahdi da kuma Aminu jikanta.Sonda take ma Mahdi shiya shafi d'anshi amma duk baya gani idonshi ya rufe da son zuciya da biyewa mace.

Har yayi sallama ya shiga Zuwaira ba taji ba tsaban masifa da tijarar data tsaya yiwa Umma.Ranshi a bace ya k'arasa shigowa ya nufa inda suke,har yanzu Zuwaira bata san ya shigo dan sai masifa take tayi

"kurwan d'ana kurr in gaya miki,kin lallab'a kinga idona baya gurin shine kika je kika d'aukoshi samun kiyi mishi wani abun,to nafi k'arfinki in gaya miki.Kuma duk wani makirci da rashin mutunci irinnaku na sirakai na sanshi dan haka bazan tab'a yadda dashi a gidannan ba ehee,sannan......"

Bata k'arasa ba Kawu Bello yayi caraf yace "ya isheki haka keh,marar mutunci wanda bata san darajar na gaba da ita ba,kedai wallahi Mahdi beyi saan mata ba,tir da keh da masu irin halinki,inba rashin mutunci ba Yaya batayi sa'a da uwarki bane? Ko baki darajata dan uwar mijinki ba ai kya bata darajar ta haifeki.Dama tunda nazo ranan nasan baki dena mata tijara ba kawai dai tace mun babu komai nayi shirune amma ba wai na yarda ba".

Kamar mutuniyar arzik'i tayi shiru,kai kace ba ita ke zazzage masifa yanzu ba.Bayan ya gama da ita yayi tsaki ko amsa gaisywarta ma beyi ba ya shige d'akin Umma dake ta faman share k'walla tana fad'in yayi hak'uri ya k'yale Zuwaira.

      hghausanovelseries.blogspot.com

ALAHAKI NEH!!Where stories live. Discover now