Page 4

53 5 2
                                    

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸

*ALHAKI NEH!*

🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋🌸🦋

® *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ŧɧɛ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

By the applomb writer: *Hamagee*

Sept,2017.

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Wattpad @Hama_gee

Ina me baku hak'uri kan rashin jina da wuri,wata matsala aka d'an samu amma yanzu komai ya daidaita insha Allah.Hamagee loves u all #Team AHN👏👋

Page 04

°
Kai tsaye Mahdi ya nufa gidan Kawu Bello babu wani shayi,da isar shi kuwa ya hau doka sallama "salamu alaikum!,salamu alaikum!!,salamu alaikum!!!".Kafin a fito ya k'ara wata sallamar kafin yace "wai babu mutane ne a gidan nan?",can saiga wani yaro ya fito da gudu yana "waalaikum salam".Mahdi ya dube shi cikeda takaici yace "tun d'azu nake sallama kaman babu kowa a gidan,ina Babanka?".

Yaron ya dubeshi yace "yana ciki shine yace nazo na duba waye ma,ka shigo".Mahdi yace "duba! Ni ba shiga bace ta kawoni,yi min kiran Baban ka kawai!".Yaron yace toh sannan ya juya da gudu kamar yadda yazo.Cikin mintuna da basu wuce biyu ba da shigan shi ba saiga Kawu Mahdi ya fito sanye da babbar riga.

Ganin Mahdi a tsaye a wajen ya bashi mamaki,yace "lafiya kazo gidana ka tsaya a waje kamar wani bak'o?",Mahdi yace "lafiya lau" a tak'aice.

Kawu Bello yace "to madallah,daman ina neman ka kaga kuwa kazo a daidai".Mahdi ya dubi Kawu Bello yace "ni ba wannan bane ya kawo ni wajenka,naji abinda kaje gida kayi wa matata Zuwaira kuma ka kyauta",cikeda mamaki Kawu Bello ya saki baki yana kallon Mahdi dan be tab'a tunanin rashin mutuncin nashi ya kai haka ba,saidai wani sa'in baya ganin laifin shi dan a cewarshi Umma ceh ta b'ata shi.

"Lallai Mahdi yau ka tabbatar mun da rashin hankalinka a fili,ni kake yiwa irin way'annan kalaman?",Mahdi yace "Kawu kenan,wai a daki mutum kuma a hanashi yin kuka.Koma miye ni ba damuwata bace,damuwata d'ata kuma itace ka daina zuwa gidana kana zagin matata dan bazan lamunta ba wallahi".

Kawu Bello yace "hakane,yanzu ka tabbatar mun da cewa mace tafi iyayenka daraja a wajenka,ni dai bazan maka baki ba amma ka sani komai daren dad'ewa zaka girbi abinda ka jima kana shukawa,wannan itace maganar dan haka ka wuce ka bani waje bani ba kai kaje can ka k'arata da matar taka amma ni na cire hanuna akanka kuma insha Allahu zan d'auki Yaya daga wajenku kafin bak'in cikinka da matarka ya k'arasa ta,ja'iri kawai".

Kawu Bello na kaiwa nan ya bar Mahdi a wajen ya shige gida a fusace.Shima Mahdin barin wajen yayi,kai tsaye ya nufa gidanshi yaje ya k'are cin mutunci wa Umma kafin ya dawo wajen Zuwaira ya cigaba da bata hak'uri.

******
Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa har Allah ya kawo mun shekaru hud'u yanzu.Aminu yana tafiya kuma yayi wayo sosai,ga surutu dan har an saka shi a makarantar allo.Saidai har ila yau Umma tak'i komawa gidan Kawu Bello ita a dole tana son mutuwa a kusa da d'anta duk da cin mutuncin da yake biye matarshi sukeyi ma.

Watarana da rana,Aminu ya nufa d'akin Umma da abincin shi wai suci tare kasancewar yadda yake son zama kusada ita dukda tsangwamar da Zuwaira keyi mishi in ta ga hakan.Abunka da yaro,besan me takeyi bama.

Ya zauna kenan suna cin dambu dan yau shi akayi a gidan,Zuwaira ta k'are neman shi a cikin gidan bata ganshi ba,hakan yasa tayi tunanin ko ya shiga d'akin Umma.Kai tsaye ta nufa d'akin taci sa'ar samun shi kuwa yana zaune suna cin dambu ita kuma tana mishi hira kamar wani sa'ar shi,abinka da kaka.

Finciko shi Zuwaira tayi tana fad'in "da wannan tsohuwar k'azamar kake cin abinci Aminu?,baka san hakan zai iya cutarda kai bane,to kada na sake ji ko ganin hakan ka jini?",ta zare mishi ido,ya d'aga kai alamar yaji sannan taja shi tana masifa.

Rayuwar duniyar ta ishe Umma,babu d'a babu jika kowa yana gudunta.Dama Kawu Bello neh kuma shima ya daina taka k'afarshi gidan sakamakon rashin mutunci da cin zarafin da Mahdi yaje har gidan shi yayi mishi dama akwai shi da zuciya.

Shekaru sunata k'arewa,tsufa yana ta k'aruwa mata.Aminun ma da yake zuwa wajenta tana jin dad'i yanzu ya daina dan ya fara wayo kuma Zuwaira ta riga ta sa mishi k'inta a ranshi.Kullum ita kad'ai take zama a d'aki yanzu,ga wulak'ancin da take sha a wajen Zuwaira kuma babu yadda ta iya tunda d'an nata ma baya ganin kimarta balle matar ta gani.

5yrs ltr,
A kwana a tashi,asarar me rai inji Mallam Bahaushe,yau an wayi gari babu ran Umma.Allah yayi mata cikawa a daren yau wato Juma'a,ta idar da sallahn dare kenan kamar yadda ta saba kullum duk da kasancewar ta tsufa sosai dan da ky'ar ma take iya tashi.

Ta idar da sallahn kenan tayi addu'o'i ta shafa sa'annan ta nemi gu ta kwanta,toh tashin da bata yi ba kenan a wayewar garin yau.Masha Allah,Allah yayi ma Umma cikawa,ta huta da muzgunawa irin na Zuwaira.

Ko yaya zasu k'are? Muje zuwa dai👌😱..

     hghausanovelseries.blogspot.com

ALAHAKI NEH!!Where stories live. Discover now