page 16

2.8K 190 8
                                    

*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

* A shafin daya gabata,munyi kuskuren number,amaimakon 14 se muka saka 15,idan muka ce zamu dawo baya da matsala wasu zasu rikice sabida haka zamu ci gaba da 16 inshaa Allah,nagode.*

16
A asibiti kuwa uncle say gaba daya hankalinsa ya tashi jin za'a shiga da suhail cs sabida ta kasa haihuwa,sosai hankalinsa yaqi kwanciya,yakasa zaune ya kasa tsaye shi kuma ba b'angarnsa bane gefen haihuwa,Ganin Dr. Hafiz ya fito daga thereter room ranshi a b'ace ya sanya qirjin say ya doka da k'arfin gaske,yana fatar ba abunda ya faru kenan ba, Gwiwa a sace Dr. Hafiz yazo kusa dashi kallanshi yayi sannan ya d'ora hannunshi a kafad'arshi ya kura masa ido,hannun nashi Dr. Say yabi da kallo sannan a hankali ya mayarda dubansa zuwaga Dr. Hafiz amma beyi magana,cikin dakiya hafiZ yace dashi

"Im so sorry to say we lost both the mother and the child,tunka mufara thereter d'in Allah yayi ikonsa akansu kayi hakuri abokinaHaka Allah ya tsara"Kasa koda motsi yayi idonshi sun qeqeshe sunyi jajir amma ba alamun ruwa acikinsu,ihun da hafsat ta kwallah ne ya dawo dashi duniyar tunanin dayaje,da sauri sukayi kanta se gunjin kuka take wayyo ita Allah Aunty suhaila, bata taba ganinta ba se a hoto kasancewar wancen lokacin dasukayi shiri sosai ita bata gani kuma tunda ta warke bata zoba amma sunyi wata irin shaquwa mara misaltuwa kullum se sunyi waya yafi a irga,ko jiya sanda sukayi waya,yauma da safe haka, sosai hafsat ta gigice dajin zancen Dr.Hafi,say shi yama rasa me zeyi Dr.bafiz ne ya lallashinta azatansa qanwar marigayiyar ce, A haka ya lallaba yayiwa mahaifinshi waya da kuma nata mahaifin kasancewar dama basusan ankawota asibiti ba,mutuwar suhaila ta rikitar da Dr. Say sabida yana matukar qaunar matar tasa,sannan be tab'a kawo mata mutuwa ba ko kan yafita da safe lapiya lau ya barta kuka yake tayi tamkar wani qaramun yaro har akayi sadakar uku,hafsat ma gaba d'aya ji take duniyar ta mata duhu,batajin dad'in komai,haka dai dole kowa ya haqura wanda ya fisu san baiwarsa ya dauke abarsa gaba daya.......

*Bayan sati uku*

Yaa shaam zaune a parlor din gidansa kusa dashi haleema ce take ta faman taunar cingam sekace abun dole, shi kuwa gaba daki daya hankalinsa baya kan kallon dasukeyi yana gun wannan hafsat da gaba d'aya tun zuwanta ta sauya masa tunani,be tab'a zata akwai ranar da tunanin hafsat ze hanashi sakat ba,anya kuwa bazece da abba yayi nadama ze maida itaba,kai idan yaje gun abba baze saurareshiba wataqil gwara ma yaje gun daddy,da wannan tunanin yaje ya kwanta....
Niko nace hmm ubanka zakaci d'anye wlhy..

"Mero ni kuwa wai in tambayeki?" kallon hafsat meron tayi "Ina jinki mana Allah yasa na sani" gyaran zamanta tayi ta tattare nutsuwarta gun mero tace

"meyake damun yaa shaam? Naga duk yabi yayi baqi ya rame,kuma ya rage kiza kiza" kura mata ido mero tayi na yan dak'k'u kan daga nisani bayan ta gama nazarinta ta nisa tace

" kaidin mace ke d'awainiya da shaam hafsat,wlhy haleema tagama da yaa shaam ta shanyeshi tas,danma su momy sun tashi tsaye da adu'a,danma bazaki fahimta bane amma da kunnena naji tana magana da qanwarta harira akan naqasashin dasukayi,ko kad'an fa baya sha'awar mace wai sabida karya tuna abunda suka aikata,in taqaice miki dai kud'ad'e take karba a hannunshi da kadarorinsa baji ba gani nan da kika ganshi yanzu bashi da komai se asibitinsa shi d'inma sabida daddy yana tsaye ne akan asibitinsa da takardun wurin gaba d'aya,sedai tayita yawon banza nabin maza,ni a ranar danaji suna zancen aunmai asiri a ranar na sanarwa momy nanne fa aka d'an samu sauqi domin adu'o i da magungunan tsari sukayita nemar masa,gashi baya kula da ibadunsa da addininsa seda daddy ya tashi tsaye yanzu dai yaji sauqin rashin jin sha'awa duk nice yar rahoto akwai lokuta da dama da idan naje gidan nikan tadfasu suna wasaninsu wasu time ma har kwanciyar aure nake fahimtar sunayi dukda ni ban yarda da matar ba,yanzu abu daya ya gagaremu shine rabashi da matar sabida tsananin santa yakeyi fa,gashi ita kuwa komai ya samo seta qwace shi tatas ni na rasa wane irin kaine sa yaa shaam,gashi kumansu daddy sun saka yana adu'o i kema dai ki tayashi gaskia,yana cikin wahalar mace" nisawa tayi sannan tace "Allah ya kyauta musu,Allah ya shiga tsakaninsa da ita" kallon tausayi mero ta mata ganin tana kwallah tace

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneWhere stories live. Discover now