page 18

2.4K 180 1
                                    

*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                 18

Dafe kanshi yayi bayan ya kwanta yace cikin kukan dabesan sanda ya kwace masa ba "Meya sanya arayuwa Hafsat take shan wahala har haka,ina tsananin sanki hafsat amma bazanyi ganganci nuna miki hakan ba,kamar yanda bazan tab'a bari soyayya ta tayi tasiri azuciyarki ba,gwaramun haqura dake a matsayin mata akan narasa rayuwarki har abada.." kukan yashigayi kaikace qaramun yarone,ganin wannan bazata fiddashi ba ya sanya ya shirya zuwa gun amininsa kamal khan domin sanar masa matsalarsa......

  "Kamal akwai damuwa fa babba wlhy,duk sanda na kwanta senati mugwayen mafarkai akan lallai idan har na kuskura na auri yarinyar nan se an kasheta har lahira,ni bazasu iyamun komai ba sabida riqon addini haka sukace amma wai itad'in alqawarine duk mesan tan daya aureta lallai se sun ga bayanshi babu ita ba tarawa da wani d'a namiji harta bar duniya ni sosai take ban tausayi wlhy,wama yasan ko wancan yayan nata hakance ta faru dashi,ni ina matukar san hafsat son daban taba yiwa wata 'ya mace irin saba a duniya,rashin adalci d'aya zuciyarta tamun na sanya ta qaunaceni,Bansan yanda zatayi da ciwon zuciya ba idan har naguje mata,kuma ni bazan iya cewa da ita ga abunda yake faruwa ba harga Allah" nisawa khan yayi cikin yaren india yace

" Sam karka gjjeta,karkuma ka nuna mata baka santa,wannan ba abinda zeyi illah ya wargaza mata zuciya gaba daya,sanan ni ina abu d'aya ne cikin biyu,kodai iskokaine da ita kokuma asiri aka mata,danni bantab'a jin hakan ba se'a irin harkar iskan nan,nifa a nawa tunanin kabata lokaci,ka kula da ita ka nuna mata soyayyar dakake mata inyaso a hankali kana koyar da ita girman adu'a da tsare azkhar safe rana da dare dakuma yawaita yin azumun litinin da alhamis,kana ana yawaita yin salatin annabi ba adadi,idan ma iskane zasu bayyana kansu idan kuma asirine lallai Allah ze taimaka kaga abun ya karye" murmushi yayi ya daura hannunshi akan kafadar khan

"Inajin dadin shawar warinka abokina,Allah bar zumunci hakan zamuyi ai dole ma".

    Tunda hafsat taga yananyin Uncle say se jikinta ya mata sanyi,dak'yar ta iya jan jikinta zuwa bedroom nasu,har akayi magrib da ish bata fito ba,har akazo cin dinner koda aka aika kiranta se cewa khairii tayi ta qoshi tasha fresh milk,ganin haka Uncle say ya gano damuwa tashi ga wannan yasanya ya janyo wayarsa ya rubuta mata txt kamar haka

"My love i swer idan bakizo munci abinci ba bazan ciba nima,kuma na tabbatar bazaki so Uncle say naki ya zauna da yunwa,plss kizo I LOVE YOU". Kasa dauke idanta tayi daga message din tana mamakin kalamansa har ya kuma turo wani jinta shiru

"Baby na dagaske fushi kike sabida namiki shiru dazu,tsabar jin dadin kalamanki ne yake shirin sakani kuka a dazun,kuma inajin kunyar nayi kuka a gabanki amma trust me i love you more than words can tell,plss com and hav dinner together with ur fam" Tana murmushin  jin dadi tazo dining d'in ta zauna amma me tarasa dalilin daya sanya matukar kunya ya hanata had'ata ido dashi har abincinma ta gagara ci se wasa takeyi da cokalin hannunta,wayarsa ya dauka ya rubuta mata

"Meye hakan kunyan wa kike kuma? Yauba shagwab'a kenan" karayin k'asa tayi da kanta bayan ta karanta message d'in amma batayi replyin nashi ba,murmushi yankumayi yace cikin message

"u go and get set,we r going for a date" murmushin dake qarawa fuskarta kyau ta d'ago tana masa cikeda qauna sannan a hankali bayan sun had'a ido ta sadda nata idon k'asa lokaci daya taji tana masifar jin nauyinsa kuma ya mata kwarjini,miqewa yayi kakarsa ta kallesa tace

"Bakaci komaiba?" murmushi ya sakar mata

"Nida hafsat zamuje yawo ne,bamasan mu qoshi danyawa a gida,murmushin tayi itama bata tankaba,tun dazu ta kula da yananyinsu ai yau taga sauyi sosai awurin dukkansu musamman Sayyeed dabaya iya d'auke idanshi akanta duk wani zumud'i yake ji......

    A hanya yau hafsat gaba d'aya ta kasa sakin jikinta dashi,hannunta ya janyo yace "'Yan matan uncle say yadai niyau tsiwar nakesanji sa shagwab'ar" batayi magana kurun dai ta juyar da kanta d'ayan gefen tana murmushi,hannunta dake had'e da nasa ya matse sosai da sauri tashiga janye hannun ta saka wata qaramar qara,tace cikin shagwab'a "Nashiga uku Uncle say dazafi wlhy" sake hannun yayi yace yana dariya

"gobe ma kya kuma mun banza idan ina miki magana" batace komai ba,shima shirun ya d'anyi,se can taje bayan ya wuce wani samosa joint

"Uncle say onions samosa zanci" kallonta yayi yace "sekin cemun baby tukunna" zaro ido tayi tace "Haba mana Uncle sayyeed" murmushi ya sakar mata yace yana kallon dayan gefen alokacin dayake shan kwanar barin layin "Kinwa kanki sekince Baby say zan siya miki komai ma" Turo baki sannan ta sadda kanta kasa a hankali tace "Baby" dariyar mugunta ya saki sannan yakuma cewa "Cewa zakiyi,Baby say zanci onions samosa" Kara turo baki tayi batai magana na yace "Bazaki fada ba na qara gudu kinwa kanki kenan??" cikin muryan kuka tace

"Baby say zanci onion samosa"  parking yayi ya mayarda hankalinshi akanta,sannan yace "kinsan Allah hafsat ba wasa a zancena akan wannan yawan koke koken wlhy semunyi fad'a ke ko wasa aka miki se kinyi kuka,bazan ma qara miki wasa ba" D'agowa tayi tace tana share kwallan

" Im so sorry Uncle say,bazan kara ba" cikin kuka tayi maganan ko yanzu,shi wlhy dariya ma ta basa,itafa komai qarantar abu kukane,kannewa yayi yace "Oya call me Baby say again" tana kukan tace "Baby say" yace "Noo cewa zakiyi I love u baby say" kallonshi takumayi sannan tace

"I love you Baby say" ta fashe da kuka" jiyayy kamar ya rungumota amma ba hali,ya tabbatar cewar lallai jitai kamar yace ta maresa dayace setace masa baby,yasani tanajin nauyinsa amma wannan ita kadaice damar dazeyi amfani da ita ta saki jikinta dashi mastayin saurayi seya ganar da ita amfanin suturta jiki dakuma yawaita ibadar mahaliccii.... Da wannan yace "kiyi hakuri dear,bazan kuma sakaki kuka ba kinji?" daga masa kai tayi tace "Tokimun matashin murmushi mana,dariya tayi gaba daya hawaye shabe shabe a fuskarta tace " Uncle say a murmushin ma akwai matashine?" dariya ya saki shima "Ea mana bagashi kinyi ba?" suka saka dukkansu......

Mom Nu'aiym

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneWhere stories live. Discover now