page 35

2.4K 177 6
                                    

*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

35
Gaba d'aya muhammad hankalinshi ya gama tashi, da gudunshi kuwa yayi hanyar waje,buzun megadinsu yace wa

"Bani gawayi da sauri bani gawayi" cikin rashin fahimta me gadin yace "Ranka shi dad'e Me wuta kho mara hi?" cikin takaici yace mara dan Allah yi maza ka daka mun me yawa yanzunnan sauri nake,dashi aka daka gawayin yaje ya jute a cup ya zuba ruwan dimi, da sauri ya dawo ya goge mata baki ya ringa sanya cokali yana mata d'urensa a baki gashi bata cikin hayyacin ta, haka harya samu ta hafiye fiye da rabin shi,aikam segashi tafara amai me baqi da kore sosai sosai, tun tana iya yunkurawa harta soma yinsa daga kwance ganin wannan jiran baze haifar masa da komai ba ya sanya ya kwashe ta xuwa asibiti ya gano poison taci,duk ya gama diriri cewa kuma tunaninsa ya tsaya cak, karb'ar gaggawa aka mata a asibiti,kuma atake suka gano poison ne taci a abunci kuma me yawan gaske,muhammad na tsaye yana jiran fitowar doctor's d'in,waya aka masa akan ga Ammy tanata fitar da kumfa a baki,she's unconcious ma self,kukan gaske ya saka ya sanya aka kawo masa ita a wannan asibitin,poison iri daya suka sha,kuma irin wanda yake dadewa yana zagayar jikine kafin yafara aiki, Ita dai kam Ammy an samo matsala sabida yashiga jikinta sosai amma ita dai da sauqi,dama yana kashe wa slowly within 24 hours Allah yasa anyi saurin ganewa aka kawosu asibiti before d time,hafsat ce da sauqi sedai zasuyi inducing nata ta haihu sabida babyn ya mutu already,muhammad yasha kuka inda atake ya soma tunanin inda sukaci abinci jiya atare,sabida police report da ake buqata, se kaiwa da kawo wa yakeyi a parlor yabaro asibitin, yasan sunsha lemo gidansu hafsat amma banda hafsat shida Ammy ne kawai, in hakane shida ita ya dace su kamu banda hafsat,yama rasa tunanin dazeyi gaba d'aya,zama yayi ya dafe kanshi,can kuma se gabanshi ya fad'i tunawan da yayi an kawo musu yoghurt anan b'ngaren na hafsat dasuka dawo jiya kuma shi be shaba,sabida baya shan abu me sugar se sugar free,ko lemon na gidansu hafsat sparkling soda ne kawai yasha, zabura yayi yaje ya samu hasano,wacce itace ta kawo drink d'in,kallonta sosai yayi ya murtuqe fuska yace

"Wannan milk da kika kawowa Ammy na dakuma hafsat jiya damuka dawo,daga ina ya fito?" Cikin rashin damuwa tace

"Da safe ne jiya Karime tazo dasu guda biyu,tace wai kaine kace ta kawo nan kuma kar wanda yasha se hajiya natane,shine jiya naga Ammy babban baquwane kuma nasan batashan cock shika dai ne kuma a gidan se wannan shine na kawo musu daya daga cikin madarar" kallon sosai ya mata jeki ki kiramun karimen, miqewa tayi suka dawo tare da karimen

"Waye ya baki madarar dakika kawo kika ce nine na baki kawo? Kuma yaushe mukayi dake cewar kar wanda yasha na hafsa ne?" ita dinma dai cikin rashin damuwa tace

"yallab'ai ai haj zainab ce tace kaine kace abani in kawo,har cewa nayi da itan ai haj hafsat bata nan tace dani zata dawo ne a ranar wai shiyasa na isar da saqon naka" nisawa yayi ya soma gano da babbar matsala sabida wlhy ko zainab seta fuskanci hukunci

"Ke hasano sanar dani ina dayar madarar da sauran wacce suka sha jiya?" gyaran zama tayi.

"Suna nan acikin fridge har sauran rabin ma" "Jeki kawon su yanzu,ke kuma karime karbo kizo muje wurin zeezee din" Da sauri sukayj yanda yace....

A tsaye suke ya miqa mata madarar yace k'arbi kisha wannan,saqon dana baki ki kaiwa hafsat ne,tasha kuma ya mata aiki sosai,inda kika taimaka ma har Ammy tasha kuma duk sun kamu da sharrin ki,se kema kisha yanzu in ga ko zeyi aiki a naki jikin" zaro danta tayi waje,cikin tsiwa tace

"Wlhy bazan shaba,kuma Allah ya sanya cikin ya zube gaba daya" be fahimci kalamanta ba ya sanya hannu ya kwasheta da kyakyawan mari yace cikin qaraji

"Shine zaki zomun da hauka,shine zakiyi poisoning matana? Meta miki zaki kashe tq? Yanzu gashi sabida wani gruges na banza zaki mun hauka ki hada har uwata,rashin hankakin naki har ya kaiki ga tunanin yin kisan kai?" zare idanta tayi jin ya ambaci kisa tace

"Nashiga ukuna ni zainab wlhy ni ban saka maganin kisa anan ba,na zubewar ciki ne kawai na saka mata" wanketa yayi da wani marin

"shine zasuna riqan fitar da kumfa a baki,shine likitoci zasu tabbatar cewar deadly poison ne? Kuma inna zubar da cikine ya akayi yayi affecting har Ammy? Idan na zubar da cikine kema karbi kisha muga yanda ze miki" kin sha tayi se kuka da take tana rantse rantse akan na zubar da cikine, a fusace yace

"Zanje da madarar nan aduba wlhy sena hallaka ki idan hakanne" yana barin dakin ta janyo wayarta ta kira qawarta data kawo mata maganin datake iqirarin na zubar da cikine wato *HALEMAH SHAMMAZ*.

Mom Nu'aiym

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneDonde viven las historias. Descúbrelo ahora