LAILAH-DIZHWAR

1.8K 78 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
            🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
            🌷🌷🌷🌷🌷🌷
   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*
    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*
         *_ZAINAB NASEER SARKI_*
             *_ (ZEENASEER😘)_*
          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*

*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*

*(34)*

__________

Tunda Lailah ta dawo gida hankalinta ya kasa kwanciya sabo da halin da Rauda take ciki Mamaki da kuma tunani sun hanata sukuni, Rashin Sanin abunda ya saka Rauda cikin wannan yanayi shine yafi damunta, amma haka zata daure ta yakice abun daga cikin zuciyarta dan tabbas in Mama ta ganta cikin damuwa itama zata iya shiga damuwar.

Tashi tayi ta nufi kitchen dan dauko abincin ta taci, A kofar kitchen din ta tarda Mama tsaye da alama tunanin wani abun take.

Tabata tayi tana kiran sunan ta duk da ba ji take bah.

Da sauri ta kalli Lailah tare da juyawa zata koma ciki, hannunta tayi saurin rukowa tare da shiga gabanta tana kallan fuskarta.

_"Menene? "_
Ta mata tambaya da hannu.

Girgiza kai tayi tare da saurin dauko mata abincin ta, ta miko mata tana murmushin yake.

Amsar abincin tayi ta ajje a gefe tare da rungumetah, tasan babu abunda Mamar take yima sai tunanin rabuwa da zasuyi.

Ta jima a jikinta yayin da itama Kuka Mamar take, da sauri ta share kwallar ta jin Lailah na kokarin barin jikinta.

Kallan ta tayi tana mata nuni da koda ta tafi har abada bazata taba mantawa tana da iyaye bah, zata dinga zuwa wajan su duk bayan kwanaki, zata kuma ci gaba da kula dasu kamar yanda ta saba zataci gaba da yi musu biyaye har karshan rayuwarta, ta nuna mata duk duniya bata da wanda suka fisu a wajan ta, haka kuma babu inda yafi mata dadi duk da kuwa dadin da zata ji,sama da wajan su, in tana tare dasu tafi samun farinciki da kuma nutsuwa, haka tayi ta kwantar mata da hankali dan itama bata san rabuwa dasu dan tasan baza suji dadi ba amma babu yanda zatayi tasan koba aure akwai mutuwa shiyasa bata nuna damuwarta sosai akan hakan, duk da sabo babban abune, balle kuma da iyaye.

Sun jima anan tana nuna mata abubuwa da kuma irin kauna da kewarsu da zatayi, Mama taji dadi dan tana kaunar Lailah sama da duk wani abu dake cikin duniyar nan, haka zalika tana tausaya mata hakanan.

Sallama tayi mata ta koma dakinta dan itama Mamar tana bata tausayi.

Koda ta tafi daki da abincin nata kasa ko loma daya tayi, zama tayi ta saka shi a gaba tana kallo ta rasa abunda yake mata dadi.

Wayarta da take silent ita ta hango tana haske.

Da sauri ta janyota, ganin Jafar ke kira tayi saurin dagawa.

Bayan ta amsa Sallamar  yace da ita,
_"Ya gidan yasu Abba, ya kuma karin saukin jikin naki"_

_"Alhamdulillah na warware sosai, ya gida da matan gidan"_
Itama ta bashi amsa.

_"Duk suna lafiya, Da fatan babu wata damuwa ko? "_

_"eh"_ ta bashi amsa harda daga kai sama kamar yana kallan tah.

_"Toh ga Asiya Matata, ku gaisa ta damu da kuyi magana da ita  "_

_"Toh"_
Lailah ta fada tana murmushi.

Amsa Asiyar tayi tare da sallama.

Amsawa Lailah tayi cikin fara'a tare da fadin,
_"Ina yini?"_

LAILAH-DIZHWAR Where stories live. Discover now