LAILAH-DIZHWAR

1.8K 92 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com




*73*

Cikin gari ya shiga sai bayan La'asr ya nufi Sokoto.

Koda ya koma anyi magariba dan haka bayan ya dawo daga masallaci ya shiga cikin gida.

beyi mamakin ganin Fareeda cikin falonsa bah, shiga yayi tare da zama gefanta yana cire hular kansa.

Bata mai magana ba shima haka.

Bayan ya cire agogonsa ya dauki hularsa ya nufi bedroom dinsa.

_"Faisal"_
ta kira sunansa.

Batare daya amsa bah ya juyo ya zauna kusa da ita.

_"Inasan magana dakai"_
ta kuma fada tana kallansa ranta a bace.

Kara matsawa jikinta yayi tare da fadin,
_"Ina jinki"_

Sai lokacin ta juyo ta fuskanceshi,
_" kana sona ko kuma baka sona, kana san muci gaba da rayuwa tare ko kuma bakaso? "_

Gira ya daga tare da kallantah, ba karamar dariya taso bashi ba yanda ta hade ranta.

_"Babyna me kuma ya kawo duk wannan tambayar haka kuma? "_
  Ya fada yana janyota jikinsa.

Da sauri ta matsa baya tana turesa
_"ba haka nace ka tambayeni bah, malam ka bani amsa mana"_

_"Baby in bana sanki kuma bana san in rayu dake, ai bazan taba auranki ki ba, sannan dukkan abunda kike mun ban taba jin zan iya rabuwa dake bah, har gobe har abada ina sanki kuma bazan dena sanki bah, illah wasu halayenkine da bana san su"_

Jin haka yasa ta kuma fadin,
_"Amma meyasa baka kin abunda nake so? "_

Ajjiyar zuciya yayi tare da fadin,
_"Mena miki, dan banje Zamfara dake bah, kema zaki iya zuwa ko dole sai tare zamu, nagaya miki inda zani amma kinki yarda, Baby aure nake san karawa insha Allah, bana tunanin zai dauki wani lokaci me tsaho, nagaya miki dan kar kice na munafunceki,kisan ina da damar karo mata uku, amma bani da ra'ayin hakan Ku biyu kun isa, sabo da haka bana san ki daga hankalinki dan bazan taba rabuwa dake ba kuma san da nake miki shima bazai taba Raguwa ba, in...... "_

_"Dakata dakata"_
Ta mike tsaye tana daga masa hannu.

_"Lallai Mommy tayi Gaskiya datace namiji ba dan goyo bane tun huri tace nayi sake kuma na gama da kaina, sabi dakai na guji komai nawa dan na faranta maka rai amma da abunda zaka saka min kenan.Faisal mun tabayi dakai zaka min kishiya"?_

Yana daga kan kujerar ya furta, _"Kuma ai ban taba gaya miki bazan miki kishiya bah"_

Kukan ma kasawa tayi cike da mamaki take kalkansa.

Tasowa yayi tare da rungumeta.

tureshi tayi tana kallansa cike da mamaki.

_"Tunda har abun yazo da haka, ni bazan taba iya zama da kishiya ba wallahi, ka sakeni"_

LAILAH-DIZHWAR Where stories live. Discover now