FULANIN BIRNI

1.2K 53 0
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄
© ASISI B. ALEEYU
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
PAGE2⃣6⃣
Faruk yayiwa ummy bayanin yanda suka same raihan, ta kalli yusuf "ko kaine kasa mata ciyon kan" faruk ya karb'e zancen da cewa "Ahh haba ummy yayanta yafad'a mana shine ciyon ta"
"Toh ka shirya da dare su usaina suje su dubo min 'yata kagayawa fatim sannan ka sanarda uwarka in zata bisu toh inkuma bazataje ba kayi k'ok'arin had'asu a waya dan kowaccen su ta kauda wani tunanin aranta kanajina"
"Eh ummy hakan yayi yanda kikace za'ayi kigayawa 'yan biyu zan sanarda fatim"
Laila yasama tana yayyafa turare, ya gaisheta har k'asa ya duk'a ta shafa kanshi "yadai son" yayi gyaran murya yagaya mata 'yanda sukayi da ummy.
"Ta murmusa ba matsala zanje d'in ay 'yata ce kayiwa fatim waya tin da safe data fita bata dawo ba daga zuwa gidan k'awar ta"
Ya b'ata fuska "haba ammaty saunawa nake gaya miki adena barin yarinyar nan tana fita ita kad'ai ta zubarda mutuncin ta tazubar da na mu, wlh Allah zanyi mummunar sab'a mata idan bata dena yawace yawace nan ba dole se anje gidan k'awa bawani dalili"
Laila kam baki ta tab'e "k'anwar Kace zaka iya d'aukar kowanne irin mataki akanta ni kaina nagaji damata fad'a" wayar shi yaciro yakirata.
"Ke kina ina? Ta amsa da "Ina gidan k'awata"
"Toh kiyi gaggawar dawowa na baki ten minute"
"Bruh wani abun ne yataso wannan kiran gaggawar" tsawa yadaka mata seda tayi jifa da wayar ta.
K'awar ta ta kalleta "lafiya dai koh" ta b'ata fuska "inafa wannan masifaffen yayan namu ne yace nadawo acikin minti goma"
Yasira k'awar ta tace "toh wlh kiyi gaggawar tashi tinda kinsan shi ba mutunci ne da shi ba"
da sand'a ta shiga gurin amma laila sedai me, Kawai jin tayi an cakumi wuyanta "ubanwa yasaki fita da wannan matsatstsen kayan, dubeki bakida maraba da 'yar iska, ki saurareni da kyau daga yau ba inda zaki k'ara fita sekin sanar dani zansa driver yakaiki amma banyarda kifita ke d'aya ba ba kuma da wannan shigar ba"
Tunzure baki tayi "wai ni meyasa ba'amun adalci ne su 'yan biyu ai kowaccen su na fita ita d'aya sai ni" fauuu kakeji ya wanketa da mari "ubanwa ne baya miki adalci, ank'i amiki adalcin 'yan biyu basufi ki jin magana ba da sune na kafawa doka bazasu tab'a tsallakewa ba saike Mara jin magana"
Gurin laila taje tazube jikinta tana kuka, laila ta zungureta "ke kika ja saunawa ana ja miki kunne amma bakyajin magana gobe ma kya k'ara" ta d'ago rinannun idonta "anya kuwa amma ke kika haifeni dubi yanda kike fifitani akan Wanda bake kika haifeshi ba, wlh na tsanesa bana son shi ko kad'an"
Wani marin laila ta kai mata "yayan naki ne bakya so kike tsana, toh wlh nafi son shi akanki keda na aifa da cikina don yafi mun biyayya kan ki" da gudu tayi d'akin ta ta fad'a kan gado tana rusar kuka.
Tsab suka shirya har fatim d'in amma laila ce gaba se 'yan biyu backseat tareda fatim, har main parlor ummy tamusu rakiya tana k'ara jadda damusu tana gayar da ita.
A wani babban supermarket suka yada zango, daga shi sai amma laila suka fita itace ke kwasar kayan da za'a buk'ata na dubiya manyan ledoji su kayi sannan suka kama hanyar gidan su raihan, har parking space yaje ya ajiye motar shi sannan suka fito yakira Abdul yasanar dashi suna daga waje.
Tare da surayya yazo ta duk'a har k'asa ta gaida laila sannan suka gaisa da 'yan biyu da fatim taja hannun su suka shige cikin gidan, acan suka same gwaggo tana bata magani, da fara'a ta karb'e su ta musu gurin zama.
Laila ce tafara yimata sannu, duk da idonta arufe yake tsab tagano muryar ta, gyada mata kai tayi su usaina ma sunmata haka fatim.
Bingyal ce tashigo d'akin tareda sume ta rik'o ta, ta zauna gefen gwaggo tana karkarwar d'ari, jikinta ta tab'a "Aura har yanzu zazzabin kodai muje asibiti" lafewa tayi ajikinta batace komai ba, "itama ba lafiyar ne? Laila ke tambayar.
"Ehh zazzab'i ne" nan kowa yamata sannu kallonsu Kawai take bata son magana, se a lokacin Yusuf yashigo tareda Abdul, bingyal d'in yafara yiwa sannu, sannan yaje gun raihan kamar yayi kuka ganin har yanzu ciyon bai sauka ba.
ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now