FULANIN BIRNI

1.1K 60 0
                                    

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 3⃣4⃣

"Wow you look stunning you're very  beautiful very pretty you look as pretty as always I so much love you thank god for giving me a good wife a beautiful wife in the world.
   Murmushi kawai takeyi ta zuba mishi ido se wani kod'ata yake ita kuma aganinta yafi yin kyau acin shigar shi ta wani yard yellow.
   Hannunta yarik'e yana matsawa, "Raihan i gave you my house, you made it a home, I gave you my heart you made it your abode I gave you my soul you made it your own Thanks for everything.
I cannot rank you as a wife because no rate card in this world has numbers going up to infinity Thanks for being the best for me I love you beyond your imaging"
   Ta rik'e haba "tin yanzu ai ka tsaya tukun kagan yanda na rik'eka kan kace haka."
    Danna bell d'in k'ofar ya dakatar dasu, koda ya bud'e ganbun fatim yagani da usaina, atake ya b'ata fuska "lafiya da sanyin safiya haka? Fatim dake jin haushin sa tace " lafiyar kenan amma tace akawo muku breakfast" jin ta ambaci sunan amma yasaka ya manta da bak'ar maganar data sakar mishi.
    Yana karb'a yace dasu "to se anjima ko" raihan tayi saurin cewa "bazaka bari mugaisa ba har wani korar su kake kamar ba gidan yayan su ba".
     Fatim kam harta juya se usaina ce ta tsaya suka gaisa sama_sama saboda kallon dayake mata sukayi sai anjima ta wuce "kice mungode kinji" Uhm kawai tace tasa kai tawuce.
    Haushin abunda aka musu yasa fatim bata wani tsayawa gayawa laila meta aiketa ba se d'akin ta tawuce cikeda haushin yayan nasu wanda take mugun jin haushi aranta.
     Amarci sosai sukeci kamar ba gobe. raihan tana taka tsan_tsan da b'acin ran mijinta shikan shi yana kauda kai ga wani abun kunsan mu mata dole se ansaka hak'uri zama damu yake armashi.
   Wata al'ada ce Yusuf ya d'aukarwa raihan dik jumu'a bayan anyi sallah yake d'aukar ta suje gidan su itakuma bazata iya zuwa hannu rabbana ba.
    Had'ad'd'en delicious take had'awa takai gidan sirakan nata.
    Kunsan  nothing  is better than going home to family with gitf of food.
   Yauma kamar kullum tayi sakwara miyar egusi da kunun gyada wanda yaji madara.
    Yusuf ne agaba yana rik'eda babbar kula se raihan abayan shi tana d'auke da babban jug.
    "Ke" ya kira fatim yana mai d'aure fuska. "Karb'i key d'in nan ki ciro sauran kuloli a mota" tunzure da baki taje tabud'e motar k'amshin abuncin kawai yadaki hancinta duk ta k'agu bataci ba.
  A dining suka jera sannan suka shiga d'akin laila.
Gyaran k'afa suka taradda anamata ta hannu.
   Yusuf yayi murmushin nan nasa mai tsada yace "ammaty ke Kullum gyara kike gaki always fresh amma kiyita kankare fatarki" da murmushi ta maida masa amsa "son kenan mata ai seda gyara bara ayiwa surukar tawa tukun, nan gaba dakanka zaka rik'a kawo min ita.
  Raihan kuwa sadda kanta k'asa tayi se a lokacin tasamu damar gayar da ita.
Sun jima ad'akin kana sukayi sama gurin ummy. Tin kafun suzo tasan da Zuwan su saboda haka har ta saka 'yan biyu sun shirya musu drinks a table.
Har k'asa ta duk'a ta gaida ummy irin gaisuwar uwa da d'anta, Yusuf yabita da ido ganin irin ladabi da nutsuwar da take bai gun ummy ko rabinsa bata yi atareda da laila ba.
    "Fira suka sha sosai tareda ummy tana bata tarihin k'uruciyar Yusuf wani gurin tayi dariya wani gurin ta jin_jina kai jin irin zuciya da halayyar mijinta tana k'ara samun satar ansar mallake mijinta ta hanyar gano wasu dab'u nashi da bata sani ba.
     K'asa suka sauko gabad'ayan su Raihan da kanta tayi saving d'in su har Yusuf d'in se albarka take sha gun Dady yana yaba girkin nata sosai.
  Lokacin da zasu wuce gida yakawo kud'i yabata amma tak'i karb'a seda Yusuf yasaka baki sannan ta duk'a har k'asa ta karba tana godiya. Dady yak'ara yabawa da hankalinta sosai aranshi yakejin yasamu surukar kirki zata gyara mishi Yusuf akan wasu d'abi'un nasa.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

FULANIN BIRNIWhere stories live. Discover now