zakisan koni waye 6

3K 122 0
                                    

💚💜💛♥💙
ZAKISAN KONI WAYE
💜💛♥💚💙
®zuwairat(ummu Maryam)

6⃣

Sauran kwana uku da tafiya Salem ya tafi yola ya shirgawa ummanshi gaskiya da karya amman ya gayawa abbanshi gaskiyan abinda zaiyi kuma ya bashi full support don abbanshi yafi ummanshi saukin kai.

Dukkan guards dinshi sunce zasu bishi Amman yace su zauna su jirashi har yadawo, da Abdul kawai zashi.

Ranar Thursday suka isa kano,kuma agidanshi na Kano suka sauka dukda Abdul nada babban gida a kano Salem cewa yayi I need my space.,

bayan kwana biyu Salem na zaune yana tunanin anya wannan ba stupid idea bane? Ya zaiyi kamanshi ace yayi descending so low don yana son true love.
"You can just back down" wata zuciya tace mashi
"No..not now.. I know it will be fun" ya fadawa kanshi, yana cikin tunanin ne Abdul yayi sallam yashigo tare da wani good looking guy. Ahankali ya amsa masu sallaman tare da daga kanshi yana kallonsu, cikin respect guy da suka shigo da Abdul ya gaida Salem cos yasan shi waye.

Bayan sun zauna Abdul yace
"Sir wannan guy din shine zai dan chanza maka kammanni da cosmetics" kallonsu Salem ya tsayayi for a moment sannan yace
"OK"  guy din ya dan runtsuna sannan yace
"Alh zamu fara yanzu" ya fadawa Salem
"OK" ya sake ce mashi. Wata katuwan bag gayen ya dauko ya fiddo wasu abubuwa kaman kayan kwalliya , kallon kayan Salem yayi sannan yace
"Me zaayi da wannan cosmetic din?" Ya tambayi gayen
"Dasu zan dan chanza maka kamanninka.." Ya amsa mashi
"Hope basu da side effects" ya sake tambayanshi, dan murmushi guy din yayi sannan yace
"Not at all sir"
"OK then..let's begin" Salem yace mashi.

Kayan ya kawo  gabanshi sannan ya fara dan shafa mashi kayan, Abdul kam zai kallonsu yake, da sun hada ido sai ya galla mashi harara.
Sunfi minti ashirin suna abu daya sannan guy din ya dauko gemu, mara tsawo, kallon beard din Salem yayi sannan yace
"Is this necessary?" Ya tambaya yana kallon gemun with disgust
"Yes sir...wannan zai kara badda kamanninka" Abdul ya amsa mashi, Salem baice komaiba ya mike ya dauki iPad dinshi sannan ya kunna mirror cikin, kallon kanshi yayi, sai yaga an rage mashi haske sosai, amman still duk Wanda yasanshi daya ganshi zai ganeshi, kallon guys din yayi sannan yace
"Zan koma original color dina kuwa?" Daga mashi kai yayi
"Yes sir...da akwai  wani makeup remover da zan baka Wanda zakayi amfani dasdashi kullum kafin ka kwanta"
"Are you telling me kullum zaka dinga yaba min wannan abun a fuskata?" Ya tambayeshi sounding so inquisitive,
"Yes sir..kasan in kayi amfani da makeup remover komai zai goge har sai mun sake wani" guy din yayi mashi bayani
"Ni dai babu abinda zai sami fuskata ko?" Ya kara tambayan gayen
"Sir kar ka damu" yakara jaddada mashi. Sannan Salem ya koma ya zauna aka saka mashi gemun. Daya kalli madubi yaga kamanninshi ta Dan sauya.

Bayan guy din ya tafi suka fita da Abdul cikin wata old modern Toyota corolla,  yana tuki Abdul na nuna mashi gari sannan yana gaya mashi sunayen wuraren.

Ko 30 minutes basuyi da fitaba Salem ya sami parking space yayi parking sannan ya kalli Abdul yace
" alh Abdul kadawo driver seat " kallonshi Abdul yayi yana murmushi sannan yace
"Sir har ka gaji?"
"Yeah" daria Abdul yayi
"Sir a haka zamu samu biyan bukata?" Abdul ya tambayeshi, Salem yayi relaxing tare da lumshe idanuwa sannan yace
"I am excusted.. Inajin kaina yana son iyimin ciwo sannan am not use to hayaniya" ya fada yana mikewa zaune
"Sorry sir very soon zaka dan saba"  ya fada yana fita daga cikin  motan, zagayawa yayi wurin Salem sannan ya bude motan Salem yafito shikuma ya koma driver seat. Abdul yana tuki yana tambayan Salem sunan inda ya nuna mashi dazun amman yayi banza ya kyaleshi,
Suna komawa gida direct wajen first aid box ya wuce ya Balli aspirin yasha. Sannan ya wuce bedroom dinshi,

Aranan duk yanda Abdul yaso su kara fita ko kallonshi Salem baiyiba balle ya bashi amsa.

Wace garima makeup artist din ya kara zuwa ya chanza mashi fuska Amman ki fita Salem yayi wai the sun is very hot, sai bayan sallan asar suka fita, suna cikin yawo, mutane sai tsaida taxi suke amman ko kallonsu bayayi balle ya tsaya.

Around six Salem ya hangi wata babe tsaye, ta ci gayu cikin fitted gown,gata beauty, Salem kallon  Abdul yayi sannan yace
"Alh kalli wata yarinya chan..she look cute" sai lokacin Abdul ya lura da yarinyan.
"Sir ka tsaya kayi toasting dinta mana tunda tayi maka" Salem dan rage gudun motan yayi sannan yace
"Ya zanyi toasting dinta...kasan ban taba woeing yarinya ba.." Ido Abdul ya zaro
"Sir what about all the girls?.."
"Su suke nuna interest a kaina..." Bai gamaba yaga yarinyan tana tsaidasu, Dan murmushi yayi sannan yayi parking yana cewa
"Allah gani gareka" da sauri Abdul yace
"duk inda tace kanuna kasan wurin" yarinyan Dan takawa yayi saitin Salem sannan tace
"Mallam sharada zaka kaini" wani kamshin turare Salem yaji sannan ga muryan yarinyan so  melodious
"OK" ya amsa mataa shiga motan tayi suka kama hanya.

Da taimakon Abdul suka isa sharada, sai yarinyan ta cigaba da nuna mashi inda zai kaita har suka isa kofar gidansu, 1k ta fiddo ta mika mashi, kallon kudin Salem yayi sannan yace
"Bani da chanji"
"Keep the change" yarinyan ta fada mashi, Dan girgiza kai yayi sannan yace
"No...you keep the money" yarinyan hada gidan sama Dana.kasan tayi
"Malan kallanni da kyau ka kalli kanka wayafi wani bukatan kudin" ahankali Salem yace
"Nafiki bukata... Amman haka nan nakeson bar maki kudin" yarinya tsoki taja tare da wulla mashi kudin sannan tace
"Kaji matsiyaci da iya yii...dalla take your money" tana kaiwa nan ta shige gidansu. Salem kam dariya ya dingayi kaman mara hankali
"Wai kaji matsiyaci da Iya yi" yafada cikin daria. Shima Abdul daria yake, Salem kallon Abdul yayi sannan yace
"Ashe mata sun iya rashin mutunci " ya fada yana rike cikin don tsananin daria
"Sir indai wulakancin matane kadan  ka gani...don wallahi suna dashi kwando2" Salem kara tuntsurewa yayi da dariya
"Ai sai yanzu na lura da haka ...anyway nasan wannan adventure namu zai zama fun cos am feeling it already"

zakisan koni wayeWhere stories live. Discover now