Part 1

3K 96 1
                                    

🎀🎀🎀         🎀🎀🎀
               ❤❤
                  🎀

       *MATAR UBA*

   *By Miss_ayusha*

*🌈Kainuwa writer's asso🤝*

Bismillahir rahmanir rahim da sunan Allah nake farawa.

             1⃣&2⃣

Hayaniya ne kawai ke tashi a d'akin kamar ana rigima jin hayaniyar na k'ara yawa yasani kutsa kai na ciki abinda kunnuwa suka jiyo min bai wuce banbamin da matar takeyi ba

  "Alhaji wallahi bazata sab'u ba ya za'ayi komai akayi a gidan nan sai ace Rahina ce da laifi sai kace ita bata da gata to wannan fa sam bazai yiwu ba"

  "Ke Rakiya in banda abinki Rahina da Heedaya duk ba 'ya ya na bane ko kuma bani da ikon hukun tasu kike nufi,maiyasa kwakwalwarki bata fad'a miki dai dai shin kinga Rahina kawai na hukun ta"

  "Ko ba ita kadai ka hukun ta ba amma cewa kayi laifin tane bayan kuma wanan munafuka mai b'akin aniyar ita ke haddasa komai" jin abinda Rakiya ke fad'a yasa Heedaya kallon mamin ta ganin irin kallon da mamin nata ke mata ne yasa ta yin shiru,

  "Rakiya fita ki bar d'akin nan tun kafin ranki ya baci kinaji ko"

"Ko baka fad'a ba zan fita,ke kuma mu zuba nidake shege ka fasa" nan tasa kai tayi gaba tare da 'yar ta Rahina

   "Ruwan sanyi ta debo mishi yayin da ta mika masa, Alhaji kaji kasha kodan zuciyar ka tayi sanyi"

  "Haba Murja ai ke yakamata ace na baiwa ruwan sanyi ko dan wanan masifafan matar,Murja ina mai baki hak'uri akan duk wani abu da Rakiya take miki ko ba dade ita zata kunyata"

  "Alhaji kar ka damu mahakurci mawadaci bakomai kaji ana kiran sallah ya kamata ka tafi masallaci" toh ya amsa mata yayin da yayi toilet yayo alwala sanan ya tafi masallacin, su din ma alwalar sukayi dukkan su yanda sukayi sallah bayan idar da addu'an mamin su ta zaunar dasu

"Habiba" na'am mami, "Heedaya" na'am, itama ta amsa

"Heedaya maiyasa baki jin magana maiyasa duk fad'an da nake miki bazaki ji ba,Heedaya miye ribar fad'an da kikeyi tare dasu Rakiya bayan kinsan halin su bazai taba canzawa ba"

  "Mami yanzu dan allah haka kawai muna zaune sai naji wata na fad'a miki maganar banza na kyaleta nikam wallahi sam bazan iya ba,amma kiyi hak'uri in Allah ya yarda na daina kulata"

"Ko kefa yar albarka haka nake son kin kina fad'a kinji ko"eh ta amsa mata,

  "Ai mami ni bansan halin wa ta dauka ba ace yarinya bata da hak'uri ko kadan" kan ki akeji iya abinda Heedaya ta fad'a kenan d'akin mamin su tayi yanda ta dauko mata maganin ta

  "Mami ga maganinki baki sha ba" ohh Heedaya kinga har na manta ma, nikam ina zan mata yanzu dai kisha"haka tasha maganin nan abinsu suna hira kamar ba uwa da yaran ta kai kace kawaye ne, ring ring waya ta shiga ringing ganin Habiba ne ta dauka yasa ni kasa kunne jin mai take fad'a

  "my prince ya kake?"

  "Lafiya lau, ya gidan dasu mami?" Ita din ma lafiyan ta amsa mishi,

"Princess kinsan meye" a'a sai ka fad'a ki shirya yanzu ina zuwa"

"My prince ka dawo ne?" Tun yaushe princess " shine kuma baka fad'a min ba "am swry baby na yanzu baga shi na fad'a miki ba sai ki shirya ina nan zuwa kafin sukayi sallama,

  "Mami wai fa kinsan Ahmad ya dawo shine koya fad'amin sai yanzu wai na shirya yana zuwa"

"Toh habiba tunda ya fad'a miki yanzu ai sai ki shirya ko" toh ta amsa mata

  "Iyye masoya wato ya Ahmad niko ya fad'amin ya dawo ko zai zo ya sameni ai"Kunfi kusa cewar Habiba,

  "Yar kanwata zo kiji dan Allah ki taimaka ki hada mishi orange juice kafin na fito wanka sai ki dan dafa mishi abinda bazai yi wahala ba kinji" toh ta amsa mata itadai mamin su na jinsu ko tak bata ce  musu ba,toilet Habiba ta shiga domin yin wanka yanda Heedaya ta shiga kitchen rasa mai abinda zatayi daya dan tasan kafin tace zatayi abinda take so zai iso kawai ta yanke shawaran dafa mishi jellof na taliya wanda taji uban ganye da hanta a ciki ga kuma juice din da take had'awa tuni wurin ya kaure da kamshi b'angaran Habiba tayi wankan ta tsaf nan ta zauna gaban mirror mai nata da shafa kafin ta danyi makeup wanda bai ma fuskan ta yawa ba wani blue less nata ta saka mai ratsin pink a jiki dinkin riga da skirt sosai kayan ya zauna a jikin ta yanda taci daurin ta sanan ta feshe jikin ta da turare masu sanyin kamshi d'akin ta zata sauke shi ta shiga shidin ma abin kamshi ta fesa yanda duk wurin ya kaure da kamshi kafin ta koma wurin Heedaya, "wow yar uwa kinga yadda kika fito kuwa" da gaske Habiba ta tambaya sosai ma shine amsar da Heedaya ta mayar mata

  "To yanzu dai kin gama girkin ne?" Eh gashi nan komai na jera mishi yanzu fruits kawai zan yanka sai a had'a ko" kiss kawai Habiba ta manna mata a goshi kafin tayi wurin mamin su

  "Mami kiga nayi kyau" sosai ma yar mami kin fito abinki tsaf ina fatan dai Heedaya ta gama shirya komai" eh ta bata amsa "toh ai itama tazo tayi wanka tunda ta gama"to mami bari na kirata" haka ko tayi kitchen dan kiran ta amma me batanan lekawan da zatayi tajiyo hayaniyan ta a waje da hanzari ta karasa wurin

  "Heedaya lafiyan ki daya kuwa mai kuma ya hadak'u"

  "Adda Habi wai fa kawai nafito zan zubar da shara shine wanan banzar yarinyar ta watsa min ruwa ashe uwarta na ganin mu dan na mata magana shine suka hayayako min dukkan su"

  "Ke dan ubanki har zaki yi wani magana to bari nai maganin ki inyaso uwarki ta fito sai ta shigar miki nan fa sukayi kanta ga Habiba sai faman kiran mami take jin kiran yasata fitowa,

  "Inalillahi ke Heedaya mai kike shirin aikatawa haka iyye " me zakiyi da kujeran"

  "Haba mami ya d'aga fitowana kawai Rahina ta zuba min ruwa d'aga magana kuma suka fara balbaleni da bala'i harda wai uwata tayi miye dinta oho"

  "To kiyi hakuri kinji kinga lokaci yana wucewa maza wuce ki shirya Habiba ku wuce mu tafi"

"Shegu dangin munafukai a haka zaku kare matsiyata wanda basu gada arziki ba woo uwa da yarta suka shiga ihu"

  "Mami kinji abinda suke fad'a ko" Heedaya kiyi hak'uri mu tafi" dakin suka koma yanda ta saki kuka da kyar suka lallabata tayi shiru sanan tayi wanka itama, misalin karfe 8 baban su ya dawo a sallah Habiba ke fad'a mishi yau Ahmad zai zo fatan alkhairi yay musu sanan ta tafi kaya iri saya suka saka abinsu kamar yan biyu idan ka gansu dole su baka sha'awa karfe 8:15 Ahmad ya iso gidan.







Miss_ayusha💋

MATAR UBAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt