Part 8

1.5K 39 0
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

       *MATAR UBA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*By Miss_ayusha*




*🌈Kainuwa writer's asso🤝*


         1⃣5⃣&1⃣6⃣

Kuyi hak'uri jina shiru da kukayi wallahi school ta sani gaba ga abubuwa sunyi yawa amma da komai yayi dai dai zaku riga jina.




  Gid'an amarya yayi kyau 'yan kai amarya sai san barka sukeyi itako banda kuka babu abinda takeyi yau ga ranar da Mamin su taci buri ta gani amma babu ita a wannan lokaci nan fa rasuwar mahaifiyar tata ta dawo mata sabuwa itama Heedaya ba'a barta a baya ba ganin zata rabu da yayarta gashi Matar Ubansu ba kaunar su take ba wannan abu idan ta tuna yana d'aga mata hankali.

Misalin karfe 8 na dare Ahmad da abokan shi suka iso gidan sosai sukai musu nasiha kafin abokan su tafi da sauran kawayen amarya an bar d'aga amarya sai angonta.

Kulle dukka kofofin gidan yayi kafin nan ya dawo yanda ya barta a haka ya sameta umartan ta yayi akan taje tayo alwala suyi sallah tashi tayi kirjinta na bugun uku uku sai da tafara wanka kafin tayo alwala turarukan da Antyn ta ta bata kuwa ta feshi dukka jikin ta dasu kafin kace me har ya dawo cikin d'akin abin sallah ya shimfida musu nan kuwa ya jasu sallah ya dade yana musu addu'a sannan ya matso da abinda ya shigo dashi.

  A cup ya tsiyaya mata sannan ya zuba nashi.

  "Gimbiya sarautar mata bismillah ko" nok'e kafada tayi alamun a'a murmushi kawai yayi da kanshi ya shiga bata tana ci sai da ta koshi sannan yaci nashi shidin ma sai da ya koshi ya tattara su a gefe tana gado can karshe haka ya hau shima tuni ya kashe musu wuta tattara kafana nayi nay waje na basu wuri.

Su Heedaya an koma gida duk kewar 'yar uwarta ya isheta Allah Allah take gari ya waye taje ta ganta.

Washe gari misalin karfe 10 taci ado atampan ta mai purple color ta saka bata yi wani havy makeup ba amma tayi bal'in kyau.

  "Babynah Allah miki albarka" jawota jikin shi yayi yayin da ta amsa mishi da amin maganganun jiya kawai yake tunanowa.

  "Wayyo ya Ahmad zan mutu kay hak'uri bazan iya ba" bugun wasa tai mishi tare da rufe fuskarta.

  "Kaga wallahi kadaina bana so"

  "To zo kiji wani magana"

  Kusan shi ta zauna batayi auni ba ya cafke bakin ta yana kissing dinta ganin abin nashi zae yi yawa yasata fara kuka a hankali da kyar ya raba bakunan su ya saki.

  "Baby yi shiru nine ko" kai ta d'aga mishi "yi hakuri princess kedin ce kinfi zuma dadi" dariya kawai tayi yanda ta daura kanta a cinyar shi suna a haka sai ga sallamar su Heedaya da sauri ta tashi d'aga cinyar shi.

 
Da gudu Heedaya ta rungume Habiba tana hawaye

"Addana nayi missing dinki wallahi" shii kanwata kiyi shiru haka kinji ba zan dinga zuwa miki gida ba kuma kema zaki dinga zuwa min" kai ta d'aga mata "yawwa ko kefa" sai sannan tayi dariya.

  "Ya Ahmad ina kwana" lafiya lau ya amsa musu

  "Ya gidan da kowa ya tambaya yanda suka amsa lafiya lau d'aki ya shiga domin fita dan yasan dole b'ak'i zasu yi ta zuwa mata.

  "Princess zan fita"Tasowa tayi tayo wurin shi kiss ya manna mata kafin tay mishi adawo lafiya ya tafi d'akin ta dawo yanda suka zauna sai hira ga uban mutane da suke zuwa ganin d'akin amarya.

MATAR UBAWhere stories live. Discover now