Page 24

3.8K 299 16
                                    

A rikice Kausar ta fito daga motan ta karasa wurin yarinyar da ta bige, dago yarinyar tayi tana jijjigata amma shiru sema jini daya biyo hannunta, kuka tasa tana gani kaman ta kashe rai gashi area din shiru babu mutane balle ta nema taimako, komawa mota tayi ta dauko wayan jikinta na rawa ta dannawa Hydar kira toh in ya dauka me zaki ce mishi?   Wani zuciyar ya tambayeta, katse kiran tayi kafin ya fara ringing  ta dannawa Khalil kira wanda shima shiganshi gida kenan daga masallaci yanaso yaje ya duba Anwar dan tunda su Mom suka  dawo bata ce mishi komai ba. Wayanshi dake cikin jallabiyanshi ne ya fara ringing, cirowa yayi ya duba yaga Kausar ce ke kira, cike da mamakin kiran me take mishi ya daga wayan tareda sallama, Kausar ganin ya daga wayan tasa mishi kuka sosai hankalinshi ya tashi yace "Kausar lfy kike kuka, meya faru? " cikin shesheka tace "Khalil I need ur help, nazo shiga unguwa na samu accident, na bige yarinyar mutane gashi kaman ma bata numfashi" salati yayi yace "calm down I'm on my way, gani nan zuwa" be jira amsarta ba ya kashe wayan yayi cikin gida da gudu ya dauko key din motarshi ya fito.



Kausar kuwa zama tayi a kasa kusa da yarinyar babu tabbacin da rai a jikinta ta hada kai da gwiwa tasa kuka, batasan adadin lokacin da ta dauka ba se ganin hasken headlight  din mota tayi ana mata horn, sosai gabanta ya fadi dan a tunaninta wani ne kuma gashi ta bar motanta akan hanya saboda haka ta taso dan ta gyara parking  kafin Khalil yazo amma se ganin shi tayi ya fito daga motan ya karaso wurinta amma idonshi nakan baiwar Allahn dake kwance kasa cikin jini, juyowa yayi yace "gyara parking  dinki kin tare hanya bari na dubata" kada kai kawai ta iya mishi sannan ta shige  motanta shikuma ya karasa kusa da yarinyar, hannunta ya kama yaji pulse dinta na aiki saboda haka ya kinkime ta yakai ta mota Kausar tabi bayanshi suka kama hanyar hospital Kausar se kuka takeyi shikuma ya kira hospital  ya shaida musu gashi nan zuwa da patient kuma emergency ne.





Shiru sukayi a mota se sheshekan kukan Kausar har suka karasa hospital  din, koda sukaje nurses na jiransu da gadon daukan marasa lfy, da taimakon Khalil suka shiga da ita ciki Kausar na biye dasu a baya emergency room  suka shiga da ita Kausar ta zauna a bakin kofa tana duk adduar da ya fito daga bakinta dan a tsorace take sosai. Sai da suka kwashe 3hours a ER kafin su samu numfashinta ya dawo sannan suka danyi gwaje gwaje akayi treating ciwukanta, fitowa Khalil yayi yaga Kausar zaune ta hada kai da gwiwa sai ta bashi tausayi, kiran sunanta yayi a hankali ta dago ganin shine yasa tayi saurin goge hawayenta da mayafinta tace "Khalil ya take, ta farfado" kada mata kai yayi yace "bata farfado ba amma numfashinta ya dawo,  muje office muyi magana kafin ki fito an gyarata seki shiga ki ganta" kada mai kai tayi sannan tabi bayanshi zuwa office din.



Zama tayi shikuma ya dauko mata ruwa a fridge ya bata, kadan tasha sannan tabishi da kallo tana jira yayi magana ya zauna yace "fadamun ya akayi kika bugeta" goge hawayenta tayi tace "wlh yarinyar ta shigo gaban ne out of no where, nikuma koda na ganta it was already  late" girgiza kai yayi yace "yarinyar is trying to run from someone, dan naga alaman fingers da cizo da sauransu a jikinta, she was molested to the core, amma Allah ya taimake ta tayi escape, yanzu jira zamuyi ta farfado kafin musan abinyi dan seta farfado zamu samu mu gane ko tanada internal injuries" kada kai Kausar tayi tana goge hawayenta, tare suka fito zuwa dakin da aka kwantar da baiwar Allah inda Khalil ya shiga yaga komai daidai sannan yace "Kausar shigo, bari naje na dawo se in kaiki gida" kai ta kada  mishi sannan  ya fita ta jawo kujera ta zauna kusa da gadon tana kallon yarinyar dake kwance numfashinta na fita a hankali, kallo daya gabadaya setaji yarinyar ta shiga ranta, hannunta ta kai ta riko na yarinyar tana murzawa a hankali hawaye na ciko mata a ido, murya kasa kasa tace "I'm sorry" goge hawayen da suka zubo mata tayi sannan ta gyara zamanta tana addu'an Allah yaba baiwar Allahn nan lfy.



'YAR HUTU (LABARIN KAUSAR DA BINTA) EditingWhere stories live. Discover now