Page 56

3.5K 302 53
                                    

Yau sati daya kenan da yin bikin Zeena da Khalil, soyayya sabowa suka shimfidawa rayuwar aurensu, Jamil da MK sun koma school banda Anwar da har yanzu bayajin dadin jikinshi, Khalil yazo ya dubashi ya mishi allurai da bashi magunguna, en biki duk sun watse saboda haka ya bar bq ya koma main house inda yake samun kulawa sosai daga wurin Mom harma da Dad. Binta kuwa tana nan kullum zuciyarta na azalzallarta akan ta kira Anwar amma kuma wata zuciyar na hanata wanda ga dukkan alamu tafi abin zuciyar da ke hanata kiran Anwar dukda ba karamin azabtuwa takeyi da kin kiran nashi da batayi ba. Kausar ta gane da abinda ke damun Binta ta tambayeta amma Binta tace ba komai kawai tana miss din Zeena ne dukda kowa a kullum se sunyi video call, yanzu sosai Kausar ke kokari wurin ganin tana girki wanda Miemie ta sata a grps biyu duka na girki ne kuma tana zuwa tana kowa mata wanda baza'a rasa ba sannan ita kanta Kausar din tana duba internet tayi wasu girke girken, Miemie da Ya Ahmad wan Kausar soyayya sosai suke a tsakaninsu wanda a halin yanzu ma an sa rana nan da wata biyar, Salma da saurayinta engineer Hafiz ma an sa musu rana Seema ce dai har yanzu shiru.

Anwar ne zaune kan gado yana jera kayanshi a wani karamin trolley dan komawa school saboda a halin yanzu ya tabbata Binta bazata kirashi ba, sosai ranshi ke soyuwa akan rashin kiranshi da batayi ba, yanzu ya tabbatar Binta bata taba sonshi ba kuma bazata taba sonshi ba, ta wani wurin kuma tunani yayi kodai tana blaming dinshi akan abinda Mahmoud ya mata ne danshi har gobe besan cewar Mahmoud be samu nasara a ranan ba, kawai dai karyar Mahmoud ne, sosai ya kara tsanar Mahmoud a ranshi dan gashi yanaji yana gani ze rasa masoyiyarshi saboda mugun hali irin na Mahmoud, yana gama hada kayanshi ya ajiye gefe sannan ya dau key din motarshi ya fita, be tsaya ko ina ba se a bar abinda ya dade beyi ba, yana zama ya kira waiter aka kawo mishi vodka abinda ya saba sha, be kai ga kai kwalban bakinshi ba IPhone 8 dinshi ra fara ringing, sabon number ya gani wanda wannan yasa zuciyarshi bugawa, sosai zuciyar nashi ke bugawa har ya kai hannu ya dafe wurin, yana kokarin dauka call din ya tsinke, kallon numbern kawai yakeyi yana tunani ya kira ko kar ya kira, be gama tantancewa ba wani call din ya sake shigowa wanda ya tsananta mishi bugun zuciyarshi, dauka yayi ya kara a kunne tareda cewa "hello", sallama aka mishi ta dayan side wanda be iya ya amsa sallaman ba sakamakon nishadin da ya tsinci kanshi a ciki dan ko ba'a fada mishi yasan muryar da yaji kuma ya tabbata nata ne.


Kwance take kan gado, yau ita kadai ce a gida dan Kausar da Hydar sun fita, rike take da wayanta tana tunanin ta kira ko karta kira, harga Allah tanaso ta kirashi taji muryarshi ko hankalinta ze kwanta, contacts dinta ta shiga ga MY SOULMATE 💕💘💋 nan baro baro amma ta kasa dail dinshi, "ahhhh", wani ihun takaici tayi tareda wurgi da wayar ta rufe fuskarta cikin pillow tana takaicin wannan hali data tsinci kanta a ciki, ganin idan bata kira ba kanta zata cuta se kawai ta mike zaune ta dau wayan tayi dail din number dinshi gabanta na mugun bugawa, har wayan ya karaci ringing dinshi ba'a dauka ba haushi yasa taki sake kira amma ganin bazata iya hakura ba seta sake kira wanda luckily ya dauka tareda cewa "hello", lumshe ido tayi tareda dafe kirjinta saboda bugawar da yakeyi sannan tace "Assalamu alaikum", shiru taji ba'a amsa mata sallama ba not knowing shima yana chan dafe da kirji kaman yadda ta dafe, kara sallama tayi Anwar da lumshe ido ya bude tareda gyara zaman sannan yace "amin wa alaiki salam", "Ya Anwar", ta kirashi a hankali yayi murmushi dan he was dying to hear her call his name again se gashi ta kira dat too perfectly, gabadaya se yaji ba wanda ya iya kiran sunanshi kaman ita dan kuwa sunan yafi dadi a bakinta.

"Binta kin wahalar da zuciyata, se yau kikaga daman kira", samun kanta tayi da murguda baki kaman yana gabanta a ranta tace "ai ba kai kadai ka wahala ba malam", a fili kuwa cewa tayi"ban gane ba, me kake nufi", jingina yayi jikin kujeran da yake zaune kai yace "ki bani dama in ganki dan in fahimtar dake", shiru tayi na dan wani lokaci kafin daga baya tace "gidan da nake akwai security sosai baza'a bari ka shigo ba haka zalika nima baza'a bari na fita ba", sosai yasha mamaki wai har Binta tayi wayewar sanin security, lallai kuwa in yayi wasa yanaji yana gani zata mishi nisa, "a wani gida kike", ba tareda wani tunani ba tace "gidan Ya Hydar", "Hydar" ya maimaita a ranshi "Hydar soja?", ya tambayeta tace "eh shi", take yaji wani mugun kishi ya kamashi wanda ya rasa dalilin wannan kishin da idan Hydar da Binta sukazo wuri daya yakeji, cike da command yace "meke tsakaninku?", tasha mamaki jin yadda yayi maganan amma seta share tace "cousin brother dina ne, I was able to find my family", wani ajiyar zuciya ya sauke wanda ita da kanta tajishi sannan yace "na tayaki murnan ganin family dinki, yanzu ya zamuyi mu hadu", shiru tayi na dan wani lokaci sannan tace "bani five minutes will call u back", bata jira response dinshi ba ta kashe wayan, ta barshi da dunbin mamakinta, wai itace take turanci, dat too fluently.

Binta tana kashe wayan ta shiga duba MY SPECIAL 😘 a contact dinta ta kira, ringing biyu Kausar ta dauka tace "Hello Binta", "na'am anty", ta amsa Kausar tace "ya akayi", shiru tayi dan bata saba yiwa Kausar karya ba, amma a yau dai idan dai zataga Anwar toh a shirye take da ta shirgawa Antynta karya saboda haka se tace "Anty yanzu Afeefah (frnd dinta ta school idan baku manta ba), ta kirani wai yau birthday din brother dinta, dan Allah Anty inaso inje", shiru Kausar tayi na dan wani lokaci dan bata taba barin Binta ta fita ita kadai ba amma tinda Binta nason zuwa bazata hanata ba saboda haka tace "shirya bari na David magana ya kaiki", da murna Binta tace "nagode anty", sannan ta kashe wayan, Anwar ta sake kira wanda ke zaune yana jiran kiranta ya dauka tareda cewa "zaki samu fitowa", tace "mu hadu a asokoro nan da 30mins", da murna yace "toh", sannan ya tashi ya fita dan yaje ya canza kaya saboda kar yaje mata bayan kayanshi ya kwashi warin bar din. Itama tana kashe wayan ta fada bathroom da murna ta fara wanka, wanke jikinta takeyi kaman zata canza fatar jikinta, tana fitowa ta shafa mai tasa wani gown peach color, batayi wani kwaliya ba banda powder da lipstick se brushing din gashinta da tayi tasa white veil da white heel dan yanzu ta kware a tafiya da heels, wanka tayi da perfs ta dau purse dinta white ta fito, koda ya fito David na jiranta da wani mota fara kirar 4matic, saboda kar a samu matsala ta kalleshi tace "oga david", yace "yes madam", tace "to tell u the truth I'm not attending any birthday party but I'm going out to meet a friend", da mamaki yake kallon ta tace "yes, my aunt won't allow me if I told her I'm to meet a frnd dats y I lied, I hope you will not reveal dis little secret of mine", da sauri ya kad'a mata kai tareda bude mata mota ta shige baya ya shiga gaba yaja yana tsoron kar maigidanshi Hydar ya gano wannan lamarin da Binta ta janyoshi ciki karfi da yaji.


Pls u guys should manage this, nasan na muku alkawarin kara tsayin page din amma gashi ban iya nayi ba.

Finally Binta ta kira Anwar and they are to meet up a next page. A next page Anwar da Binta zasu hadu, fans ku hararowa kanku haduwar Anwar da Binta.

Don't forget to vote, comment & share.

Mzzdaddy💋

'YAR HUTU (LABARIN KAUSAR DA BINTA) EditingWhere stories live. Discover now