Kaduna
***
Haisam ne ke tafe bayan ya miƙa saƙon da Mummy'n sa ta aike shi dashi a tashar KSTA dake Unguwan Sarki, yana tafe cikin natsuwa wanda dama halinsa kenan. Bayada garaje ko rawar kai a cikin al'amuran sa. Komai nasa ɗas ɗas abin sha'awa. Ba abinda ke nunawa a fuskarsa banda murmushi da nuna rashin damuwa saboda shi mutum ne mai yawan fara'a da maida komai ba komai ba. Da kyar Kaga ɓacin ransa ko kaji ance yayi sa'insa da wani. Shi a nashi tunanin duniyar ƙwara nawa ne idan akayi hak'uri za'a barta, kuma abinda hakuri baiyi magani ba tashin hankali bazai gyara ba. Tafe yake yana sauraron program din 'Oga Driver' à Motar sa kirar Honda EOD. Ba kasafai zakaga yara matasa wanda suka kai a cikin wannan ba. Ko wani namiji musamman ɗan Kaduna yafisan ace yana tuƙa Benz wanda shine motar da yan matan sukayi na'am wajen sauraron mai hawanta.
Yan mata biyu ne suka shiga Napep a wajen bus stop din Unguwan shanu. "Barau Dikko" dayan tace a sanyaye. Daga nan bata sake cewa komai ba, dama haka suke abinsu. Barci tare, ci tare amma idan yan kan sun motsa sai kowa ya saka earpiece ya gimste fuska, balle kuma yau tanada dalilin shiga wannan yanayin tashin hankali.
Kafin mai napep ya burga sai wasu samari su biyu suka tsaida suka shiga, daya ya zauna a baya ɗayan a gaba. Yan matan nan suka buga tsaki suka sake kanne fuska tamau. "Ina zan kaiku?" Mai napep ya tambaya mazan. "Muje kawai karka damu"
An soma tafiya sai na bayan ya juya ya kalle yan matan yana washe hakorar sa kamar gonar auduga. dayaga bazai fisshe shi ba saiya gyara murya da kwabdeden tabaransa ya soma magana. "Afuwan na mance bamu gaisa ba, barka da asuba"
Wanda tayi magana da farko ta sakeyi yanzu, "Yauwa" saita juya. Taso fita da wayanta ta canza wakar dake yi amma ta tuna ana kwacen waya a napep. Gwara ta taimaka ma kanta ta hakura.
Sai wannan ya soma sosa keya, ya karkata ya kalle ta ɗayan gefen wanda batace komai ba. "Ke baki amsa gaisuwa ne?"
Ido rufe tace masa ana dole. Nan yayi shiru gwiwar sa yayi sanyi bai sake magana ba. Sai daga bisani ya soma waka mai ban takaici, "Doguwa fara kin baka gajera, ko baki dariya kinfi baka mummuna" muryan sa irin shaƙaƙƙe ne mara dadin sauraro musamman idan ana waƙa da ita.
Ba Yan matan ba har mai napep wakar yanata bakanta mashi rai. Amma babu yanda zaiyi yana hulda da jama'a.
Kafin a kai kwanar Barau Dikko wanda batayi magana da chan ba ta soma, "Mallam sauke mu nan kawai ya ishe mu" ba itada kawarta ba harta samarin suka sauka suma. Dari biyu zasu miƙa sai samarin suka saurin miƙa dari biyar wai a cire nasu duka."Ji mana" sarkin waka yace masu, wanda ta gwasale gaisuwar shi tace wai meye haka mallam ka wani takura mana tun dazu. Shi kuma yayi mata kallon hadarin kaji kana yace, kwantar da hankalin ki mummuna badake nake ba, da kawarki nake magana"
Kowa a wajen yayi mamakin wannan batun nasa, saboda yadda ya debo ta da zafi. "Idan ba'a kasa dake ba karki ɗiba. Kinata wani kumburi kina huci bayan ko kallo baki isheni ba. Halan bakin ciki kike ma kawarki dan ba'ayi dake""Jar uba! Karka kuskura ka zageni Mallam saboda bakayi kamada kallan samarin da zanyi tarayya dasu ba" sannan ta wuce saboda tana dabda zabga mashi mari.
Dayar itama tabi sahunta suka barshi a wajen, sai a lokacin tayi magana mai zurfi. "Yi hakuri yau banajin garin ne dasai ya yaba ma aya zaki" wanda tayi fada batace komai ba illa huci tana mayar da numfashi sama sama. Banda raini ya za'a ce tanama na gefenta bakin ciki.
"Mazaa ba haka akeyi ba!" Mai napep yace mashi. "Wannan kai ya shafa, babu ruwanka bani canji ka kara gaba" nan yayi zugum ya basu ya wuce kafin a zaga ubanshi.
Haka suka soma shafa titi babu wanda tace uffan ma yar uwarta, Haisam ne ya karyo kwana ya wuce su. Wanda tafi natsuwa tace, "Laila ga mutumin ki ɗan ra'ayi" Laila ita kuma tayi tsaki mai uban kara kana tace ɗan ra'ayi ko mara mutunci mai jiji dakai, aikin banza jibe irin motar dayake hawa kamar za'a kai dabbobi kasuwa. A tare suka tintsire da dariya sannan suka tafa hannayen su.
YOU ARE READING
Hasken Lantarki (Completed)
RomanceDan mutum yana maka wasa da dariya kuma ya nuna akwai aminci tsakanin ku ba lallai bane yana kaunar ka. Makashinka yana tare da kai, da dan gari ake cin gari... Ku biyo ni