Tara

4.2K 308 69
                                    

***

Sanye yake cikin Getzner mai kalar kwai, dinkin yasha aiki sosai sabida dashi yaje daurin aure dazu. Ya murza hula ɓaka na tangaran a kansa. Agogon sa na Ralph Lauren ne manne a hannunsa na hagu. Ga kuma links masu ɗankarin kyau. Takalman Balmain half cover ke ƙafansa. Yana tafe cikin nishadi zashi Rigasa inda Laila take zaune, kamshin turaren sa na OUD da Yes Saint Laurent YSL ke tashi tareda sanyin AC da aka kunna. Badman Bilal yaro da kudi abokin tafiyar manya, mai dattawa biyu iya kudinka iya shagalinka. Kura da kalabin kitse, a ganka a kyale ka. yaron maye duk garinku ana tsoron ka.

  Murna fal ransa zai gwangwaje ƙishinsa a wajen Haske. Gashi tayi gyaran gashi da dilke itama. Sannan tayi kunshi kyanta ya kara fitowa sai walkiya takeyi.

  Yana tafe yana shan cool music wakar Whitney Houston saboda yau sama sama yake jin kansa. Koda ya isa gaban gidan yayima Haske text ya isa wajen. Ankon da sukayi karamar Holland yar 5k blue ke jikin ta. Dayake batada jiki dinkin pencil gown tayi sai aka saka jela ta gefe. Blue gyale na R & S tasa mai stones saita fita waje. Yanayin tafiyan ta kalar yanga ne yasa tana tafiya zakaga tana rausaya.

  Daga cikin motarsa wanda tint ne ya hange ta. Lashe baki yayi tareda sosa gemun sa wanda yasha taza, shi kaɗai yasan me ke damunsa wani tafasa zuciyar sa ke masa. Da sallama ta shiga motar tana murmushi wanda dama yanayin ta ne. "HASKEN LANTARKI" ya faɗa chan kasan makoshin sa tareda miri miri da idanu.

  "Na'am Sweet muje ko"  wani azabtacen santa ya sake ɗawainiya dashi. Muryanta kawai ya isa ya tada mashi lissafi. Ji yake kamar ya janyota ya soma lashe ta. bai tada motar ba saida ya riƙe mata hannu ya soma murzawa. Wani yar taji kawai ta kwace da sauri.

  "Sweet muje kar dare yayi"

  Dariyar mugunta yayi sai yace, "Baby sarkin tsoro, I won't hurt you. Wallahi sanki kawai ke dawainiya dani"

  Itama murmushi tayi batace komai ba. Anan ya tada mota inda zashi gidansu dake Marafa. Tafe suke yana tuki tana kallon kwarewarsa. Ya iya murza steering mota abin gwanin ban sha'awa. Nan ta shagala ta koma duniyar tunanin sa. Tana tunanin itama wata rana za'a kaita dakinta kamar yadda aka kai Laila yau.

  Sun sha kwanar layin gidansu murna fal ransa, wai yau Haske ce zata wajen sa. Abin har mamaki yakeyi wai yana santa kuma bai taɓa kaita ɗakinsa ba. Ko first love ɗinsa Rumaisa da kanta ma take kai kanta gidansu. Mamakin Haske yake anya ita yar zamani ne kuwa? Ya za'ayi tace baza suyi wani mu'amala ba. Halan so take a kwace mata shi. Fatan sa kawai tayi daɗi kamar tantabara yar shila.

  Ya lura tanada bala'in hankali kuma zai so ace matar sa ce, amma idan yajita salap dole ya hakura da ita. Suna isa kofar gidansu sai yayi horn. Mai gadi ne yazo da gudu ta wajen mazaunin driver. A hankali ya saukar da glass sai ya Kalle shi.

  "Ya akayi ne?" ya tambaya fuska tamau babu annuri, duk cikin masu aikin gidan mai gadin ne kawai ya isa yayi mashi magana.

  "Dama Yanzu Alhaji ya shigo shine yace a kiraka idan ka dawo" ya faɗa a ladabce

  Gaban Bilal nan ya tsinke, yaga samu yaga rashi. A sittin yayi reverse saboda bai isa ya shiga da mace gidan idan Abbansa yana nan ba. Kowa kallon mutumin arziki yake masa, mai gadi ne kawai yasan sirrin sa. Duk abinda ake yi a idon Haske, bata ce uffan ba sai da taga sun soma komawa da baya.

  "Sweet wallpapers din fah?"

  "Gobe zan kawo"

  Tayi masa uzuri saboda taji ance babansa yana nan kuma bazai kyautu ace an gansu tare ba kafin ayi mata muguwar fassara. Wannan kenan!

  ***

"Hello Destiny! Dama munata jiran snacks da kajin ne tun dazu!" Laila tace ta bangare ɗaya. Shi kuma Saif shiru yayi daga farko, saida ta sake "Hello! Hello!!! Destiny kana jina kuwa?"

Hasken Lantarki (Completed) Where stories live. Discover now