Biyar

4.1K 289 15
                                    

***

  Wacece Haske?

   Hafsat da Hadiza tagwaye ne daga cikin yara goma na Alhaji Abideen. Komai nasu iri daya daga halitta zuwa yadda suke saka tufafi. Mahaifiyar Alhaji Abideen asalin yar garin Misra ce kuma tanada jini mai karfi wanda yasa kusan duka zuri'arta akwai bala'in hasken fata irin na larabawa.
  Dukda ana samun saɓani tsakanin harshe da hakora amma su Hafsat basu su fiye faɗa ba suyita tashin hankali kamar yadda sauran tagwaye suke, koda sunyi sai dai na ƙuruciya. Kansu a haɗe yake sai dai su taru suyi maka taron dangi suyi maka tas. Kuma basa bambanta kansu, koda Hafsat kace ko Hadiza wanda ke wajen zai amsa maka babu ƙyashi.

  Sanda Hafsat takai shekara goma sha bakwai wani Zailani yaron abokin Alhaji Abideen ya ganta kuma ya yaba da halinta. A cikin tagwayen tafi saukin kai, sai dai kuma baka gane haka saika haɗasu biyu a waje guda. Yadda zatayi faram faram dakai ya bambanta da yadda Hadiza zatayi. Sannan kuma Hadiza tafi san gayu, itace ma ta dauki ragamar zaban masu tufafi da daura masu kallabi idan ta kama.
    Lokacin Zailani na shekara 22 da haihuwa ya gama karatun sa na Chemistry kuma ya samu aiki a Abuja Water board. Su kuma su Hafsat ana FCE, soyayya ya kullu tsakanin su mai dadi da tsabta. Sai dai kuma a lokacin hankalin Hafsat ya rabu kashi biyu ne. Ga karatu ga Zailani, lokacin da zata samu suyi hira da Hadiza bai da wani yawa. Balle dama Hadiza tafi miskilanci batada saurin sabo da mutane yasa ma ko kawar kirki batada shi.

  Duk wani kawa to fah na Hafsat ne, abin yana bala'in damunta yadda Hafsat tayi watsi da ita. Kuma duk samarin dake zuwa wajenta sam basuyi mata ba. Babu wanda yakai Zailani ko rabin sa. Tun bata lura ba har ƙaramin kishi ya soma shiganta idan suna tare yazo. Ta rinka fizge fizge tana cijewa, wata sa'in tayi karyan ciwo har saiya tafi. Amma duk abinda ta keyi bai rage ko ɗigon soyayyar suba. In fact abu sai gaba yakeyi har iyaye sun saka baki gadan gadan. An saka bikin Hafsat bayan ta gama FCE.

   Anyi tunanin idan aka tsaida lokaci mai tsawo Hadiza zata samu itama wanda takeso ayi biki amma har suka gama babu wani labarin kirki. Haka akayi auren Hafsat da Angonta Zailani inda aka kaita gidanta na Garki. Sannan kuma aka samo mata koyarwa a Government College a wajen inda take koyar da Social Studies.

   Shekara ya zagayo har Hafsat ta haifa yarta mai suna Shamsiyya. Yarinya fara sol kamar HASKEN LANTARKI. gatada dan girma sai san barka. Rashin auren Hadiza ya soma daminsu cikin dangi har ta koma makaranta Direct Entry. Akai akai takanje gidansu Hafsat idan anyi hutu, wanda daga ita har Zailani basa binta da komai sai kyautatawa. Haka zata koma dasu provisions kala kala da suturu ga kuma Hafsat duk wata saita tura mata kudin kashewa.

   Kwana ya soma kaiwa shekaru, Hadiza babu wani labarin kirki wajenta. Ita ma Hafsa ta koma NTI domin ta karasa karatun ta na fannin malunta. Haka har Shamsiyya tayi girma tayi wayo sosai, ta tashi  cikin kulawa wajen iyaye da kakanni. Balle ma Dangin mahaifinta asalin yan Paki ne a Zaria. Suma suna bala'in ji da ita kamar su lashe. Duk hutu a zaria takeyi ta raba kwana gidajen yan uwa.

     Gata batada matsala sam babu kiwi ya. Akwaita da fara'a da san wasa. Ana haka ne sai Hafsat ta sake samun juna biyu. Farin cikin wajen yan uwa ba kadan ba, amma banda Hadiza. Bawai bakin ciki take mata ba. Kawai tsoro ta soma yi lokaci yanata tafiya amma ita shiru.
   Wannan Karon cikin Hafsat ya bata wuya matuka tuni an mayar da Shamsiyya Zaria da zama, sai aka ce ma Hadiza ta koma gidansu domin ta taimaka mata da wasu aiki sabida kusan kullum sai an kara mata ruwa. Ko periods dinta na makaranta sai da aka rage mata wata sa'in kuma Hadiza taje maimakon ta. Tunda bawai amfani da Hassana ko Hussaina suke ba balle a gane yan biyu ne.

***

Haka zaman su ya kasance cikin aminci baka taɓa jin kansu dama basu saba ba. Koda watan haihuwar yazo tare sukayi ta siyayya wanda dama Hadiza tafi gayu ita ta zaba komai na yan gayu. Satin haihuwa Hafsa ta ji alama amma batace komai ba. Takan tashi da ciwon baya kala kala musamman da safe koda maraice. Gashi kuma kafarta ya kumbura yayi sukutum kamar doyan Benue.

Hasken Lantarki (Completed) Where stories live. Discover now