page 4

1.9K 85 0
                                    


Satin Shamaki uku yagane emah 'dan fashine
Tundaga wannan rana yayi dana sanin bin emah

Akwai ranar da  Shamaki dasu emah suka fitoh gari
Sai shamaki yayi yunqurin gudu. Cikin rashin sa'a mota taka'de shi
Me motar kuma ya gudu
Saiga Alhaji Sa'eed yadanno kan motarsa. Aiko yaga abinda yafaru
Nan ya kinkimi Shamaki da kansa yasakashi Cikin motarsa ya kaishi asubiti
Nandanan akabashi temakwan gaggawa

Xuwa yamma Shamaki yasamu kansa aiko yatubure abashi sallama shi qauyansu xaitafi
Haka Alhaji Sa'eed Ya neman mishi sallama yabashi ku'di me yawa suka rabu Shamaki namishi kyakkyawar addu'a

Yaxo tasha xai hau mota sai kuma yaga emah
Haka Shamaki yabi emah xuciyarshi namishi suyah

Ahaka yayi wata uku gunsu emah ammafah baya binsu fashi. saidai suje suyi sudawo
dan emah yasaka masu tsaranshi

Shinefah ranar dasu emah xasu Aiki gidan Alhaji Sa'eed
Shamaki Yace xaibisu. Ashe daraban xaiga mugun tashin hankali ganin kisan rashin imanin da Alhaji Sambo yayima iyayan HAYATUDDEEN

Wannan shine Shamaki ALIYU

***                         ***

A qauyan dai Takai Anan Shamaki yayada xango agun
dan haka yana shiga gidansu saiga 'yarsa MUFULEEDA da Innah sun tareshi cikin farin ciki da murna metarin yawa

Sannan daga bisani Tace a ina kasamo yaran turawa me tsafta haka gashi kyakkyawa
Wlhi tunda nake banta6a ganin kyakkyawan 'da irin wannanba
Shamaki yagyara xama ya gayama Innah Komai bai boye mataba

Tajinjina kai Tace shiyasa akace  metemako baya ta6ewa me xuciyar imani
Gaskiya na tausaya ma yarannan
Allah yatayamu riqo
Shamaki Yace AmEEn
Tace yanxu dai dole katashi tsaye kagina yaran nan da ilimi da kuma rayuwar daya saba acikinsa
Shamaki Yace Karki damu Innah
Da ku'dine hakan xata faru kuma muna tare da kudin
Xanyi amfani dawasu takaddu daga Cikin wa'yanda  yatawo dasu dan naduba tun ahanyarmu taxuwa naga manyan kadarorine aciki Xan inganta rayuwarshi har yamallaki hankalin kansa

(Wannan kenan)

Bayan shekara goma Sha biyar

***           ***         ***
Cikin supermarket 'din jifatu dakenan garin kano NASRIN ce 'dauke da leda ahannunta. Wacce kana gani kasan tagama siyayyarta ne take qoqarin  ficcewa

Waya take batare da tana cikakken ganin gabanta bah
Aiko sukaci karo da wani saurayi yaxubar mata da kayan hannunta wanda kallo 'daya xakamai kagane shima 'dan masu dashine

NASRIN tabi kayan da kallo wanda ba komai bane illah kayan xaqi danginsu chocolate da sauransu
Cikin 6acin rai tacire hannunta taxabge saurayinnan da mari biyu xafafah

Kai wane irin dabbane shashasha wawa jahili Wanda baya kallan gabansa iye
Akan wane dalili xaka watsarmin da kayana. Shin kasankoni 'Yar gidan waye. Qaxami dakai daxaka bangajeni har qaxamin hannunka yata6a fatata

Cikin wani Yana saurayin Yace banta6a ganin jahilar mace kamarkiba

Takalleshi afurgice da waro ido
Tace Ni kake kira jahila
Yace eh nakiraki jahila Mara hankali da tarbiya

Ranfah NASRIN yakai qololowar 6aci
Dan haka tadanna wayanta
Can aka 'dauka Tace
Inasan yanxu Dad kasaka aturomin 'yan sanda sukamamin wani 'dan iska a jifatu yanxu 
Saurayin najin muryar Dad 'din nata nacewa ankagama 'Yar lele

Takalli saurayin Tace idan kacika kai tantirine a mara kunya katsaya kasha kallo dan Allah karka gudu

Saurayin yakalleta da mamaki sosai dan yasan ya girme mata nesa bai kusa ba. Amma take kallansa bashayi ba tarbiya takemai hakah
Yayi kwafah da cewa ai matsoraci shiyake guduwa
Gyara harshenki basaikin ha'dani da Allah ba inanan har uban naki yaturo 'yan sanda dubu sukamani
Ta kalleshi araine Tace baxasukai dububa Amma xasu baka mamakin da dubunnai baxasu bakaba........
Xaiyi magana aiko saiganin 'yan sanda yayi akansu
Suka tambayeta waye Wanda xa'a kamamata
Tanuna saurayin dacewa kufara dukansa tun anan dan yasan yata6a NASRIN 'Yar gidan Alhaji Sambo 'Yar lelensa

Aiko suka kwakumeshi sukayi waje dashi
Ita kuma takalli kayan nata dasuka xube tata6e baki xata tajuya da nufin komawa ciki dan da'da siyayyar wasu saiko tayi ido hu'du da wani kyakkyawan saurayi Wanda tunda uwarta ta haifeta bata ta6a ganin kyakkyawa ha'dadde kamarsa bah
Farine tas Yana sanye da riga da wado English dress yakar6e sosai
Ga wani tabarau (glass) afuskarsa
Qamshinsa sai bugarta yake

Shigowa yake Cikin nutsuwa da jan aji irin na yaran masu ku'di da ilimi. Ya hucce tagabanta

Tuni tarufe bakinta data bu'desa
Taje da gudu tasha gabansa Tace jimana dan Allah
Ya'dan xare glass 'dinsa tare da nuna mamakinta Yace lafiya
Tace am sunana NASRIN Alhaji Sambo 'Yar lelensa. Nasan xakasan Dad 'dina saboda ba 6ayayye bane

Yace hmmm sannu NASRIN najiki. shikenan
Tace aa inasan kagamin sunanka dan Allah
Yace meyasa
Yafa'da da'dan xare idansa ka'dan
Hakanko yaburgeta tasaki ajiyar xuciya
Tace hakadai
Yace sunana metsadane saimunyi ciniki xangaya miki
Tayi Dariya Tace daga naira 'daya xuwa miliyoyi muyi ciniki xansiya
Yayi murmushin daya qara masa kyau Yace nalura ke'din me ku'dice
Tace sosai mah Dad 'dina yataramin

Yayi Murmushi yace bari Xan gaya miki kyauta
Tace dadai munyi cinikin Yace Karki damu sunana........
Takafeshi da ido tanasan yafa'da
Amma saiyayi kamar xaihucceta saida yaxo dai-dai setin kunnanta ya qarashe da cewa
HAYAT........

Lumshe ido NASRIN tayi danjin da'din muryarshi da kuma da'din sunansa
Tace wow beautiful fantastic wonderful name
Yace yah. Den Nagode
yayi Ciki abinsa


🕊🕊

Daskarewa NASRIN tayi atsaye agun
Yayinda HAYAT yayi siyayyarsa yadawo yaganta agun
Da nuna mamaki afuskarsa Amma ya wucceta
Ganin datayi baxai qara mata magana ba
Yasata binshi da sauri

Wow Tace ashe kaima 'dan masu dashine
Yayi kamar baijitaba
Taqara da cewa
Motarka taha'da irinta yaran hutu
Ananne yamata magana Yace
Haba dai kalleni dakyau kinga nayi kama da yaran Hutu
Tace saidai kaxagi kanka.
Amma Kasan kaxarce yaran hutun
Yayi wani shegen murmushi dacewa haka kikace
Tace eh gashi ka'iya Murmushi me tsayawa arai.
Yace ko
Tace kaima kasani
Yace gashi shima sai anbiyani nakeyinsa Amma ina mamakin yanda nake miki Komai kyauta
Tace nacancanci hakanne
Yaqura mata ido Yace toh nabarki lpy
Yashige motarsa kamar walqiya ya6acema ganinta

Yasalam NASRIN Tace
Yayinda qawarta MEENAT tadafata Tace
Niba kayan wanki bace daxaki shanyani a mota
Saboda wannan balaraban daya siye xuciyarki
Kidaiyi ahankali karya tafi da imaninki
Batare da NASRIN takalleta bah Tace yatafi dakomai nawa

Kinyi kuskurine tunda duk wannan da'dewar da kukayi baki amshe masa kunnansa bah
Tace kamar yafah
Tace baki amshi number nasa bah

Dan xaro ido tayi Tace nayi rashi

🕊🕊🕊
HAYAT ko daya shiga motarsa shima abokinsa Salix mita  yadinga mai wai ya shanyashi
Shuru HAYAT yamai

Salix yajah tsaki yace waisai adingama magana akanayin shuru
Wannan halin naka yanaban haushi
HAYAT dai baiyi magana ba

Hanyar qauyan Takai sukayi
Sai yamma lis  suka isa qauyan

Duk wata murnar Innah saida tatattaro takar6e
HAYAT yace ina Babah yakene ( Yana nufin Shamaki dake Babah yake cemai )

Innah Tace Yana bakin Kasuwa
HAYAT yata6e baki Yace aidama nasani baxaita6a xama a gidaba
Innah Tace toya xamuyi dashi yafisan xama ata hira mara amfani
Yace ina my baby toh
Innah tata6e baki Tace oho mata nidai wannan suna bana sansa wai my bebi abu ko kyan fa'da babu
Koyada yake yahudawa da nasara sunratsaku
Salix yayi dariya kamar me
Yace tunda dai yahudawan da nasaran basusa munmanta addininmu ba ai kya saurara mana
Tace kudai kuka sanih.......

HAYATUDDEN  🕊🕊 Où les histoires vivent. Découvrez maintenant