14

448 67 6
                                    


SOKOTO, MARCH 2005.

“Nafisa, ina kausar da Halima?” naana ta tambaya yayin da take shigowa dakin cikin sassarfa. “Ban san ina suka shiga ba, amma nasan ba zasu wuce bayan gida ba ko wajen inna.” 

Cikin doki naana ta jawo hannun nafisa da ke kwance a kan kujera tana karatun novel na “english literature”, tace” taso muje nafisa, wani abu nake son ku gani kafin yaya Ali ya dawo.”

Tana ji an ambaci yaya ali, sai nafisa ta kwace hannunta tare da fadin “ah ah, nana don Allah kar ki jawo mana fadan yaya imam. Wai baya ce ki daina kiransa da Ali ba sai dai yaya aliyu ko imam?”

Nana tayi tsaki tace, ke kika san wannan, ni don Allah taso muje, wallahi baya nan sun fita tare da mami. Ke kin cika tsoro wallahi.”

A hanyar zuwa bayan gida suka ratsa lambu bayan sun wuce wajen da ake motsa jiki a nan suka hadu da kausar tare Halima.
Kafin wata daga cikinsu tayi Magana, sai kausar tace, “kuzo mu raka Halima tace gida zata wuce yanzu.” 

Kafin nafisa tayi Magana, sai naana ta kyafta ma ta manyan idanuwanta, sannan tace, ok, muje mu raka ta. Suna tafe a hanya suna labarin komawa makaranta, hutu ya kare.

"Ai wallahi kuna jin dadi tunda ku ba a makarantar kwana ku ke ba. Ni fa jibi kamar yanzu ina can hostel". Nafisa ta fadi taba bata fuska.

“ai  ke kika so, ni da kausar ba can aka fara kai mu ba? Amma tun ranar da mu kayi sneaking muka gudo hankalin maami ya tashi, ai ba a kara marmarin mu koma ba.” Naana ta bata amsa. Suka kwashe da dariya.

Kausar ta kai mata duka a baya tare da fadin “wato har fadi kike hankalin mami ya tashi. Amma fa kin dandana, don anty ta zane ki.” 

Naana ta gantsare baya ta harari kausar sannan ta ce, “kuma yaya ali ya kara min, ke kuma kina gida abinki, alhali tare mu ka tsero.” 

Halima da nafisa sai dariya su keyi. Can kuma Nafisa ta kara bata fuska, tace "ni babu abinda ke damuna kamar ace ni yanzu zan shiga SS1, amma dukanku SS2 zaku wuce."

"Kar ki damu nafisa, ai kamar gobe ne, kuma may be idan an yarda a gida sai ki zana waec tare damu." Kausar ta amsa ta.

Naana tace "haka ne kuma. Tunda ni da kausar sai mun je SS3 zamu rubuta waec, wai a cewar mami munyi kanana ba zamu zana waec a SS2 ba ." Ta kare zancenta tare da juya idanu. Suka koma fashewa da dariya.

"ke kuma a dole kina ganin ke big girl ce ko" halima ta fadi tana dariya.

Nana ta kama kugunta da hannuwa tace "to yaya son ranki? na kusa 15years yarinya."

A haka suka kai Halima hanyar da ta raba gidajensu, wajen da suke kira da junction.  Anan su kayi mata sallama, tare da alkawarin zasu shigo wajenta gobe kafin kausar ta wuce gida.

A gida bayan sun tambayi rabe maigadi ko mami ta dawo? ya tabbatar musu babu wanda ya shigo bayan fitarsu, sai naana tace ku zo muje. A bangaren hagu daga bayan gidan inda dakunan baki da sashen imam yake. can suka nufa.

Kausar tana tambayar wai me za muyi anan kuma? Sai suka ga naana ta zura hannu cikin aljihun jeans skirt da ke  jikinta, ta zaro makulli tare da karasawa bakin dakin Imam ta zura makullin ta bude. Sai ta kara juyawa ta tabbatar babu kowa a kusa, sannan tayi musu alama su shigo daga ciki.

A cikin dakin, kai tsaye naana ta bude drawer dake gefen gado ta shiga jawo jaridu da magazine kala kala, har ta zakulo wata magazine, mai suna Bill Fashion & style, ta zauna a kasa akan carpet dake shimfide a kasa gefen gado. Kausar da nafisa suka zauna a kusa da ita, ta bude wani shafi ta fara nuna musu hotunan da ke cikin magazine din.

Imam ne a wasu shafukan na magazine din sanye cikin shiga kala kala, dake nuna ana tallar kayan sawa da styles na dinkunan zamani, a wasu shafukan kuma wasu mutane ne mafi yawa matasa kamarsa duk dai ana tallar kayan “sham collections."

kausar ta rike baki tana fadin, "ashe yaya imam modelling ya koma kenan.  Anya ko mami ta sani?"
"Ina fa zata sani, da ni ce dai da yanzu ya fara kumfar baki yana duka na."

Suna kallon wani shafi da imam yake kusa da wata yarinya kayan jikinsu duka kalar blue da ruwan madara, sai dai na shi blue mai duhu ita kuma mai haske. Sunyi kyau har sun gaji suna kusa da juna. Nafisa tace, "ni anya wannan ba budurwarsa ce ba?"

"Ke fa kina da matsala. duk salon talla ne fa. Karanta ki ga ba mutanen ake bayani ba kaya ne da dinkuna a ke talla." Kausar ta fadi a lokacin naana mike zuwa wajen daya drawer gado ta bude ipad da ta gani ajiye,  ta zauna a bakin gado tana jira ta gama booting.

Nafisa da ke rike da magazine a yanzu tace "amma kausar kin san me, wallahi yaya imam yayi kyau, duk hotunan mazan da suke a cikin ya fi su kyau, kai har matan……..

Daidai nan aka bude kofar dakin aka shigo, da sauri suka mike tsaye! imam ne sanye da shirt mai gajeren hannu kalar sararin samaniya, sai wando da takalma duka kalar navy blue, ya harde hannu a kirji ya shigar da idanunsa ciki ya na kallonsu daya bayan daya, kamshin turarensa gaba daya ya game dakin kamar yadda tsoro da fargaba suka  mamaye zukatansu.

Daga can naana da ta mance da ipad da take rike tayi kokarin tserewa. Ai taku biyu yayi ya damko damtsen hannunta, wanda hakan ya ba kausar da nafisa damar tserewa a guje!

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now