15

528 64 3
                                    


"Assalamu alaikum."
Mami Asmau tayi sallama kafin ta shigo babban dakin hutawa na gidan, tare da tura kofar shiga. Katon palo ne mai dauke da kujeru kusan seti biyu kalar jinin kare da kwalliyar silba. Haka ma labulayen palon kalar silba ne. Sai kayan kallo da sauti da ke tsare a gefen kudu. A bangaren yamma sashen cin abinci ne da aka kawata da kujeru da teburin dinning kalar jinin kare, a gefensu akwai wash hand basin da fridge kalar silba.

Daga can cikin gida aka amsa sallamar Mami. Mai amsa sallamar ta karaso cikin palon tana fadin sannu da zuwa mami. "Yauwa jummai yaya gida? Ina yaran nan?" kafin jummai ta amsa aka kara yin wata sallamar. Imam ne ya shigo dauke da leda da katuwar jaka yana tambayar mami ina za'a ajiye. Ta umarceshi da ya kai mata jakar dakin baccinta. Ta amshi ledar tana fito da kayan dake ciki.

Bayan imam ya fito daga daki ta ce ya dauko mata gorar ruwa marar sanyi. Ta kasa kunne tana jira taji daga ina zata ji karadin su naana. Yana mika mata ruwan tare da kofi, a daidai lokacin aka kira shi a waya. Har mami ta sha ruwa bayan ta zauna a kan daya daga cikin kujerun falon bata ji motsin su naana ba.

Anan kausar ta shigo palon a hankali kamar mara gaskiya ko maras lafiya. Ta karasa isowa ta zauna a kasa kan dandaryar tiles kusa da mami ba tare da tayi magana ba. "Kausar yaya dai? Ina yan'uwan naki?"

Ta dukar da kanta ba tare da ta amsa tambayar mami ba, ta waiga tana kallon sashen da imam yake a tsaye yana amsa waya. Cikin mamaki Mami ta juya tana kallon jummai dake a tsaye kusa da kofa, sai jummai ta karaso tana cewa "ai nafisar ta gudu zuwa gidansu, ita kuma naana tana dakin babana."

Kan mami ya kara shiga duhu, ta ajiye katon mayafinta a gefen kujera tana kara fuskantar kausar dake zaune tace, "zaki fada min ko yaya? Nace ina yanuwanki? Me ya faru nafisar ta wuce gida ba nace ta jira ni ba zan bata sako?"

Cikin in-inaa, ta fara bayanin cewa "mami yaya Imam ya kulle naana a daki, ita kuma nafisa ta tsorata ne, sai ta hau achaba ta wuce gida.
Mami sai da nace kar ta tafi, ki tambayi inna jummai."

Mami ta waiga sashen da Imam yake a tsaye yana amsa waya, amma babu imam babu dalilinsa.

Jummai da yake ta kula da lokacin da ya fice sai tace "kila ya je ya bude naanar, mami laifi suka yi wa babana, dakinshi suka shiga."

Takaici ya kama mami sai ta mike cikin sauri ta suri mayafinta, mayafinta ma a baibai ta lulluba a kafada, ta nufi dakin Imam. Kausar har ta mike da niyyar tabi mami amma sai tsoron haduwa da yaya imam ya hana ta, don ta tabbatar mami dakin Imam zata je. Amma a kasan zuciyarta ta sani da wuya yaya imam ya dake ta, duk lokacin da suka yi kuskure to akan naana yake dora laifin.

Damuwa da tausayin nana suka kara saukar mata. Ta san da wuya idan imam bai dake ta ko ya saka ta aikin wahala ba. Ta diba wayar nafisa nokia karama dake hannunta tare da fadi a fili, yanzu fa awa uku kenan tana daki a kulle.

A dakinsa, yana bude kofar da makulli ya shiga, ga mamakinsa sai ya tarad da naanar mami a takure saman gadonsa tana sharar bacci abinta. Ta takure siririn jikinta, hular kanta baka tana gefe haka ma karamin hijabinta kalar hular, yayin da kalabar da a kullum mami ke fada akan bata da kitso sai wannan mai kama dana 'yan reggae ta watse a saman filon da yafi so.

Ya rasa abin da zai yi sai kawai ya rungume hannayensa yana kallon ta cike da tunanin abinda zai yi. Kamar an tsikare shi sai ya je saman teburinsa na computer ya dauko wayar chajin laptop ya mikar da ita, yana zuwa kusa da nana sai ya zabga mata duka da wayar a daidai kafarta. A firgice ta tashi har tana neman fadowa daga kan gado.

Tana ganin imam ta kara rikicewa bata san lokacin da ta mike tsaye a kan gadon mai dauke da farin zanin gado ta fara ja da baya tana fadi "don Allah da darajar annabi yaya kayi hakuri, wallahi bazan kara ba."

Cikin takaicin taka masa gado da ta keyi yace "zaki sauko ko sai na karya miki kafa."
"Wayyo na shiga uku."

Ya matso kusa da ita ya mika hannu ya zabga mata wayar charger a hannu, ta dafe wajen zata fara kuka. "Kina fara kuka zan kara miki, ki sauko nace ki fice min daga daki."

"Wayyoooo ya Alee, kayi haku...." Sai kuma ta dafe baki, tana tunanin abinda ta fadi.

Yace "Ali ko? Wato ga marenin wayonki, sauko nan, yau sai na babballaki, sai na koya miki hankali"

Idan ya bita farkon gadon zai dake ta, sai ta gudu zuwa karshe tana fadin "wayyo mami, wayyo mami naa!"

Yana zabga mata bulala ta uku bata sameta sosai ba, ita kuma mami tana shigowa dakin a kufule.
Da sauri kamar zata tashi sama, haka naana ta diro daga kan gado abinka da jiki babu nauyi. Sai a lokacin ta samu fashewa da kuka ta zo ta rungume maami.

Mami ta rungumota a kafada ta dibeta da kyau, sai kuma ta mayar da kallonta ga Imam da ke tsaye yana jiran hukuncinsa daga wajen mami.

"Ka kyauta! Nace ka kyauta imam! Wato ba zaka daina dukar naana ba ko?"

Sai ta janye naana daga jikinta ta fara dukan imam da hannu. Dukawa yayi yana karewa, tare da fadin, "Pls mami tsaya kiji mana, rashin kunyar da......."

Bata saurareshi ba sai da ta kai masa duka kusan sau hudu, sai ta kula ba zafin dukan yake ji ba ita hannunta ke ciwo a wajen dukan. Sai ta katse maganar da fadin, "duk abinda tayi maka sai ka dake ta, kamar 'yar cikinka? Sannan ai an fada min ba ita kadai ta shiga dakin ba, me yasa zaka kulleta a daki ita kadai? Wai tsaya ma, tun yaushe ka kulle yarinyar nan a daki?"

Ya fara bayani "maami bayan na sauke ki wajen meeting na dawo gida zan dauki laptop da za a gyara shine na samu ita dasu kausar a daki tana min bincike."

Mami ta juyo gun naana tana tambayarta, "me yasa ku ka shigo dakin nan? An saku aiki ne?"

Maimakon naana ta amsa, sai kawai ta matso daf da mami ta rike hannunta tare da dora kai a jikin mami taci gaba da kuka.
"To ya isa haka nan, wuce muje. Kai kuma ban kare da kai ba, bari babanku ya dawo, shi zan fada wa tunda ni ka raina ni."

A zuci imam ke fadin "shikenan hukuncinta! daga ta fara kukanta na rainin wayo mami ba zata hukunta ta ba, kuma ba za ta bari a hukunta taba."

Suka hada ido da naana sai ya harareta ba tare da mami ta gani ba. Yana nan tsaye mami ta goge mata hawaye tare da jan hannunta suka fice daga dakin.

Bayan fitarsu daga dakin, ya kalli kayan naana dake watse a kan gadonsa da kuma yadda ta hargitsa ma sa gado, yayi kwafa ya zauna a kan kujerar karatu, ya fara tunani.

Toh idan mami ta fada ma daddynsa ai ya kade. Ko da yayi tafiya fushi ya ke dashi akan harkar modelling da yayi har magazine din ta kai hannun daddyn. Ya tambayi kansa anya mami zata kai kararsa akan naana gun daddy alhali ta san yadda yake fushi da shi a yanzu?

Amma yau yasan ya kulad da mami tunda har dukansa tayi da hannu, akan wannan trouble maker da ba zata daina bata ranshi ba.

Yayi murmushi a ransa ya kara fadi "Rabon mami da duka na tun muna canada, wancan lokacin ma akan naanarta ne tun tana primary school."

Ya kara fadada murmushinsa da ya tuna dukan, a fili yace "Oh God! Maami, am twenty five years, ake duka na da hannu." Amma a karkashin zuciyarshi ya damu da yadda ya ga bacin ran mami."

Ya kalli wayar chaji da ya doki naana da ita cikin fushi, sai ya ji bai kyauta ba. Amma kuma sai ya dinga lallashin kansa da cewa ai laifi tayi. Laifin da ba za ta daina yi ba, saboda ta san mami bata ganin laifinta.

Yayi ajiyar zuciya, a fili ya fadi "bazan kara dukanta ba Insha Allah!" Daga nan ya fito da wayarsa dake ta faman ringing daga aljihu, ya fara magana da Abdul Lema!

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now