Sulalewa kasa tayi ta xauna ta takure waje daya tana rufe fuskarta da dogon gashinta, dakewa yayi ya karaso cikin dakin kamar bai son taka kasa yana kallonta ya isa gabanta sae dae banda faduwa bbu abinda gabansa yake, bata dago har lkcn ta kallesa ba sae d'ada takurewa waje daya take, cire tsoro yayi ya durkusa gabanta a hankali, dago kanta tayi tana kallonsa a tsorace, murmushi yayi murya can kasa yace "Hello!" Kuri ta kura masa da ido, shi ma hakan yayi ma manyan fararen idonta, can ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "Allah ya baki lafiya don son ma'aiki S a w." A hankali ya kai hannunsa kanta ta kuma shigewa jikin bango, murmushi yayi ya matsa gabanta ya tattare mata gashinta ya mayar baya yace "Ki daina kunce gashin ki idan an daure maki Kinji" yana magana ne yana kallon fuskarta, ita kuwa wani gun daban take kallo, ji yayi ana haurowa sama, ya juya yana kallon kofa sae ga El-Ameen, dauke kai yayi El-Ameen ya shigo yana murmushi yace "Uhnn! Ka daina tsoron nata kenan yanxu?" Mikewa Junaid yayi bae ce komai ba, El-Ameen yayi dariya yace "In gaya maka meyasa kaga ta kyale ka?" Junaid ya juya yana kallonsa, sai da ya dau kusan minti daya sannan yace "akwae alluran da na mata daxu shi yasa ta nutsu, but ina me tabbatar maka da xaran ya saketa xaka gane kuran ka idan ka tsaya gabanta" yana murmushi ya kare maganar, Junaid ya tabe baki ya juya ya fice daga dakin ba tare da ya tanka sa ba, El-Ameen ya bisa da kallo yana dariya sannan ya juyo yana kallonta, karasawa gabanta yayi ya durkusa ya dago kanta, hade rai yayi yace "Sae da kika kuma cire ribbon din koh?" Kallonsa kawae take ko kiftawa bata yi, ya hade rai yace "I will knock yhu idan baki bar kallona haka ba" kamar taji me yace ta dauke idonta daga nashi, mikewa yayi ya dauko ribbon ya dawo gabanta ya durkusa ya kama gashinta waje daya ya daure da ribbon din sannan ya dagota suka mike a tare ya kama hannunta, kin binsa tayi tana tutturjewa yace "Keehh" daga haka ya ja ta suka fita daga dakin tana bin sal, Palo ya sauko da ita ya xaunar da ita kasan rug, ya dauko ledan da ya shigo da ya durkusa gabanta ya bude, fried Irish ne da kwae, sae tomatoe ketchup, ya dauki potatoe daya ya dibi kwae ya kai mata baki, dauke kai tayi da sauri tana komawa baya, ya tsaya kallonta, kai wa bakinsa yyi ya ci, Junaid dae sai kallonsu yake yana yi yana danna waya, kara daukar wani chip din El-Ameen yayi ya dangwali ketchup ya kai bakinta, tsura ma dankalin ido tayi sae kuma ta matso a hankali ta lashe ketchup din, El-Ameen ya wara ido yana kallonta, sai kuma ya saka dariya, murmushi junaid yyi yana ci gaba da danna wayarsa, sae tsotsan ketchup din take a baki, El-Ameen ya kuma dangwala ya kai bakinta ta kuma lashewa, rike kanta yayi ya tura mata dankalin a baki ta fito dashi ya fadi kasa, ya hade rai yace "I will slap yhu fah" kallonsa kawae take ko kiftawa babu, ya dauki wani dankalin ya dangwali ketchup ya kuma kai mata baki, lashewa ta kuma yi ta bar masa dankalin tana tsotsan bakinta, yayi murmushi yana kallon Junaid yace "this shows tana son ketchup lkcn da take da hankali" shi dae junaid bae ce komae ba, El-Ameen ya dinga

YOU ARE READING
Captain_Ahmad Junaid(On Hold)
RomanceCompiled by Princess Aysha Muhammad Copied by Jamiela D Ilayasu ⚓ *Captain_Ahmad Junaid* ⚓ _By Khaleesat Haiydar_ ✍? *Dedicated to......* *Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah, Ya ubangiji kamar yanda ka bani ikon fara littafin nan ka bani ikon kare shi cik...