Part 22

595 15 0
                                    

*INUWAR ZUCIYATA❤*
           _{Zarah ko Jeedah}_

*Na: Raheenat Mamoudou*

*Story by: Mamuh geee*

*ViaWattpd Raheenatmamoudou*

*Da Sunan Allah mai rahma mai jin kai*
_________________________________

*<< Page 22 >>*

Ango kam yana can Niamey, a ranar litinin aka yi ma shi birthday din she na cika shekara (30), sannan Baba Yusuf ya kira shi ya ce "Zo nan Jaheed".
     Ya zo ya durkusa a gabansa. Ya ce "Gani Baba". Yayi gyaran murya ya ce, "Me kake yi baka tafi ba?" ya ce, "Yau daman nake so zan tafi".
     Baba Yusuf wato mahaifinsa yayi murmushi ya girgiza kai, ya ce "Kayi amana ka ga amana, ka yi gaskiya Jaheed kaga gaskiya, Wallahi idan kana son Allah ya wulakantaka ka tarki rashin gaskiya, tuni Allah zai nuna maka iyakarka.
     Ka bar ganin wannan yarinyar Zarah ta kafe kai take so, ba yin kanta bane Allah ne ya nufe ta, idan ka wulakanta wallahi Allah ba zai kyale ka ba ,sai ka yi amana za ka amana, Ina gaya maka wallahi ka yi a sannu, duk inda ka ga so ya tsananta a wurin daga Allah ne, ka yi a sannu ka gama lafiya. So ba ya zuwa inda Allah bai nufe shi da zuwa ba, shima bawan Allah ne, idan har ka wulakanta Zarah wallahi Allah ba zai kyale ka ba.
     Jarabawa ta rayuwa ba irin wanda Allah baya mana, wallahi ka yi a sannu in dai kana so gamawa  lafiya da duniya, ka rike Zarah tsakaninka da Allah, idan kana son gamawa da duniya cikin musiba da bala'i ka je ka wulakanta ta ka ga yadda Allah zai yi da kai, don na ga kai shekara talatin din naka a banza za su tashi, babu hankali sai shirme iri-iri ,wannan shi ne fada na farko na karshe da zan yi maka.
      Ita kuma Zarah na yi mata nasiha ,don ba zan yi mata fada ba, son da take maka ma ya ishe ta fada, don na yi imanin yarinyar nan a yanda take sonka ko wuta ka ce ta fada za ta fada don ta kare maka so a duniyar nan, wanda ba duk namiji ne yake samun irin wannan sa'ar ba.
   Idan ka bari ka rasa irin wannan sa'ar ta kubce maka, ban yi maka baki ba, wallahi ba za ka taba samu ba. Sai kuma ka godewa Allah, tashi ka bani wuri".
     Ya mike jikinsa a sanyaye ya shiga ya ringa yi ma jama'a sallama zai tafi Don Mami har dakinta ya isketa yayi mata sallama, maimakon ta amsa sai ta ce, "Ka yi amana kayi kuma hamdala ga Allah, kayi addu'a SABANIN KAUNAR da aka samu, ya Allah yasa ya zamo alkairi a gareku Ameen, dama can Allah ya rubuta Zarah ce INUWAR ZUCIYARKA ba Jeedah ba." Jaheed ya amsa a sanyaye "Ameen".
    Ya fito dakin idonsa cike da kwalla, hankalinsa a tashe ransa baki'kki'rin ,Shi tausayin kansa yake ji, haka Allah yayi da shi, RAYUWA, kenan, auren matar da baka sonta.
  Idonsa ya cicciko da hawaye ya share tare da wata irin zaffa, ya ringa shiga dakunan gidan yana fita, Jeedah jikar Inna yake son gani ba ta nan, zuciya ta ringa ce mishi, to me za ka ce mata idan ka ganta? Meye hadinka da ita?
    Yana shirin fita yaga Abida, ya ce "Abida ina Jikar Inna?" ta dan yi dum! Cike da tausayinsa, ta ce "Wallahi ban ganta ba, nifa tunda aka fara bikin nan ta boye mini, ko yanzu Ramadan nemanta yake yi anjima za su wuce amma ba a ganta ba ".
   Yayi tsuki ya wuce ta bishi da kallo. A harabar gidan ya bai wa Malam mudi mukullin dakinsa ya ce "Malam mudi shiga dakina duk jikar da ka ganta a cikin dakin ka sanya a but ". Ya ce "To ranka shi dade".
    Ya yi zaune a cikin mota, tunani iri iri babu irin wanda baya ayayyana a ransa, zuciyarsa babu dadi, ya ringa hailala da istigifati a cikin zuciyarsa ko zai ji sanyi.
    Shi a duniya gani yake yi babu mai matsala irinsa, zuciya ta ringa ayyana masa ka je gidan mana meye? Hakkin aure ne wallahi bana badawa sai dai ayi abin da za ayi. Ai ko yau na sake ta in dai ban daura mata idda ba dole a warware aurena a Aura mini Jeedah mai sona da gaskiya, wallahi ba za ta taba barina na shiga wani hali ba, dole ta yadda sauwake mata. Idar kuma ta ki wallahi za ta yi ta zama ne ba miji, zan ga yadda ake yi ma namiji auren dole.
   Allah a kaina zan nuna ma mata karya suke yi basu da abin da za su nuna mini na so ,abun da ba shi zuciyata take so ba, zan nuna Zarah Allah ta samu SABANIN KAUNA, ZAN NUNA MATA CEWA JEEDAH CE INUWAR ZUCIYATA ba ita ba.
    Malam mudi ya iso ya shirya akwatuna a but ya ce "Ranka shi dade angama ". Ya ce "Ka ka ajiye mukulin idan yaran gidan Sun zo ka basu ". Malam mudi ya ce "Ikon Allah, yara sun gaji babban yayansu". Sai a lokacin Jaheed yayi murmushi ya ce, "Haka ne malam mudi, muje ka kaini filin jirgi.
    Yana zuwa jirgin su ya tashi sai garin Arlit,wajen la'asar sakaliya suka isa arlit bai samu shiga cikin Ikoyi ba sai gab da magarib, don haka yana shiga gidan wanka yayi, ya kira falalu ya shigar da komai dakinsa, yayi wanka ya fito sanye da jallabiya.
    A falonsa ya iske Zarah ta sha ado cikin voil ruwan zuma, ya kalle ta yayi wani birki ya daure fuska, ta gani kamar tayi kuka don tsoron da ya ba ta. Ta ce "Sannu da zuwa ya hanya?" ko wawayowa bai yi ba balle har ya amsa, ya wuce abunsa.
     Takaici ya ishi Zarah, sai kuma ga hawaye. Wasa farin girki in ji dan koyo. Ta mike ta wuce kicin tana share hawaye, ta shirya diening table kamshi kala kala, ta sanya wata irin dinkin shadda doguwar riga da dan kwali, ta yi kyau sosai cikin shaddar, ta daura kallabinta tamkar gwaggwaro, ta sanya beat passion dan kunne da na wuya, su din ma kalar purple din ne, sai kuma ta sanya silifas, su din ma purple din ne masu laushi Yan Itali, ta fito falon cike da rausaya yana kara karfin A.C.
    Ta isa gabanshi sai kamshin turaruka kala kala take yi. Ya dago ido ya kalle ta sama da kasa ya wani yamutsa fuska. Ta ce "Ya ya ga abincinka can a diening". Ya girgiza kai a hankali ya ce "Na koshi." ta kuma kafa mashi magiya, don haka sai ya nufi dakinshi ya bar mata babban falon.
     Ta bishi har dakin yana kwance a doguwar kujera, ta durkusa a gabansa ta ce "Haba don Allah Ya Jaheed, ka zo ka ci abinci mana".
   Ya kuwa mike zaune ya ce "Kee! Zauna mu yi magana ni da ke ,idan ke ba ki da hankali ni ina da shi, idan ke dabba ce ni mutum ne. Na gane dalilin ki na aurena don ki rabani da 'Jikar Inna, kin kuma raba na gane nufin ki, don ba kaunarta kike yi ba tun farko, son ki sanya ta a matsala yasa kika rabata da abin da take so, Ina sonta.
     To kin sha karya, wallahi idan kika bari na kai hannuna jikinki sai na kusan kashe ki da duka a gidan nan. Kuma ki sani ba zan taba zaman aure da ke ba, Yadda kika rabani da Jeedah abin da na fi so a rayuwata, to wallahi dake da farinciki har abada, in dai a gidan nan kike. Kuma hakkin aure ne bana badawa, fita ki bani dakina shegiya fitinaniya yar duniya Allah zanci ubanki idan biki fita ba, duk ranar da na kuma ganin ki dakin nan wallahi Allah sai jikinki yayi tsami. Fita bani wuri shashasha kawai maras hankali!"
     Ta mike jikinta a sanyaye ta bar dakin, daga haka suka shiga rayuwa matsatsi babu kama hannun yaro. Sai ta yi kwana uku bata sa sanya Jaheed a idonta. Tana gidan yana gidan. Rayuwar so da rashin so kenan SABANI ya bayyana.

Inuwar zuciyata...(Zarah ko Jeedah) by RaheenatmamoudouWhere stories live. Discover now